Skip to content
Part 7 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Habeeb na kwance a kan doguwar kujera ya ji an murɗa handle ɗin ɗakinshi tare da turo ƙofar a hankali.

A hankali ya buɗe idanunsa da suka yi nauyi sakamakon ciwon kan da yake fama da shi.

“Fateemah” ya faɗa a ransa, lokacin da ya kai duba ga Jummai da ke tsaye a bakin ƙofa tana kallon shi.

Jiki a mace ya tashi zaune, lokaci ɗaya kuma yana tunanin me ya kawo ta ɗakinshi, wanda shine karo na farko a wurinta.

Yana cikin wannan tunani ne ya ga ta kunno kai cikin, ƙamshin turarenta mai kashe jiki ne ya riga ta ƙarasowa tsakiyar ɗakin.

Jajayen idanunsa ya kafe ta da su, cikin ransa kuma yana jin tunda yake bai taɓa ganin ta da kyau irin na yanzu ba.

Sai da ta zo tsakiyar ɗakin sannan ta tsaya suna kallon juna, kallon da za’a iya kiranshi da munyi kewar juna, sakamakon kwana biyu da suka yi ba tare Habeeb ya bari sun haɗu ba, saboda gudun faruwar abin da zuciyarsa ke ingiza shi.

“Fateemah, me ya faru?”, ya tambaye ta cikin sanyin murya.

Kamar zata yi kuka ta ce “Ina ka je ban gan ka ba, ko na yi maka laifi ne?”

Ido ya lumshe tare da sauke ajiyar zuciya “Ba ki yi mani komai ba fateemah.”

“Kuma shi ne ka ke boye mani, bayan ka san ba zan iya juran rashin ganin ka ba, me ya sa ka za6i cutar mun da zuciya ne?”. Tana faɗin haka hawayen da ke maƙale a Idonta suka zubo.

“Kuka kuma Fateemah, Habeeb ya faɗa lokacin da ya tashi tsaye, don ba zai iya jurar ganin fitar hawaye a idon ta ba.

“Toh ya ba zan yi kuka ba, bacin kai ne..” sai kuma ta yi shiru saboda kukan da ya ci ƙarfinta.

Cike da rashin sani Habeeb ya jawo ta tare da kwantar mata da kai a ƙirjinshi ya ce “sorry Teemana, ban ɓoye maki ba sai don ina tsoron na cutar da ke”, idonsa lumshe ya ƙarasa maganar lokacin da ya kewayo da dukkan hannayensa biyu a gadon bayanta.

Tana jin haka ta ɗago idanunta cike da ƙwalla ta dube shi,

“Har akwai wata cutarwa da zaka yi mani, bayan wadda ka yi ta nisanta kanka dani?”

Ko kusa Habeeb bai jin me take cewa, saboda fita hayyacinsa da ya fara yi sakamakon jikinsu da ke haɗe, ɗan ƙaramin bakinta ya shiga kallo, take zuciya ta fara ruwaita mashi da ya saka nasa a ciki.

Bata ankare ba sai jin saukaukar numfashinsa ta yi a fuskarta lokacin da yake ƙoƙarin saka bakinsa cikin nata.

Aikuwa ta ɗauke kanta tare da ƙoƙarin ƙwace jikinta daga ruƙon da ya yi mata, “Miye haka ya Habeeb” ta faɗa tana ja da baya, don gaba ɗaya yanayinsa ya fara bata tsoro.

Cikin shaƙaƙƙiyar murya ya ce “Please Teemah” tare da sake riƙo ta ya maida ta a jikinshi.

“Don Allah ka sake ni in fita” Jummai ta faɗa cikin murya mai cike da tsoro, lokaci ɗaya kuma ta tattaro dukkan ƙarfinta ta Ingiza shi baya,  ta nufi ƙofa da sauri.

Bayanta ya bi da saurin shima, aikuwa ya samu sa’ar cafko ta, kan gado ya wurga ta, tare da faɗin “Ki saurare ni Fateemah Don Allah.”

Cikin tsiwa ta ce “A hakan zan saurare ka?”

Wata irin faɗuwa gabanta ya yi lokacin da ta ga ya hawo kan gadon, bakinta na kyarma ta ce, “Don Allah ka sauka ya Habeeb, kada ka matso inda nake don Allah”.

Shi kuwa kamar bai san me take cewa ba, rarrafawa ya yi a hankali ya nufi inda take.

Yana zuwa dab da ita yasa hannu ya fizge gyalen da ke jikinta, take cikakkiyar surarta dake cikin riga da skirt na atamfa ta bayyana.

Tana ganin haka ta fashe da wani irin kuka tare da ƙara shigewa jikin bango. 

“Nashiga uku, kada ka cutar mani da rayuwa.”

Cike da buƙatuwarta Habeeb ya ce, “Ki taimaka mun Fateemah, don Allah kada ki hana zuciyata samun abin da ta ke buƙata a yanzu”, yana gama faɗin haka ya fizgo ta tare da matse ta tsam a jikinshi.

Ita kuwa ba abin da take sai kuka da fizge-fizge, burinta kawai ta raba jikinta da nashi.

“Ki natsu mana Fateemah, ko so kike wani ya ji mu.”

Ta ce “Toh ka rabu da ni.”

Kai ya ɗaga “Toh zan rabu da ke, amma sai kin natsu tukunna.”

Natsuwar ta yi tare da jifarshi wani mugun kallo.

Bai damu ba, sai ma idanu ya kafeta da su.

Jin karkarwar da jikinta ke yi ya sa shi yin magana da wata irin murya “Yanzu Habeeb ɗin naki kike tsoro haka?”

Shiru ta yi, idanunta na fitar da ƙwallan baƙinciki da takaici, yau ita ce riƙe a hannun namjin da ba muharraminta ba. 

Halshe ta ga ya sa lashe hawayen da suka gangaro ta gefen idonta.

Wani irin abu ta ji ya tsarga ta, bata san lokacin da saki ajiyar zuciya tare da lumshe ido ba.

“Ba zan iya asarar hawayenki ba Fateemah,” ya faɗa yana cigaba da lashe duk wani hawaye da ya fito a idonta.

Daga ido kuwa ta ji ya gangaro wuyanta, har yana shirin zarce inda bai kamata ba.

Aikuwa ta ƙwalla wata irin ƙara, wadda ta sa Abbanshi da ke shirin tafiya Masallaci dakatawa.

Kasa kunne ya yi daidai window ɗin ɗakin Habeeb, yana son tantace daga inda wannan ƙara ke fitowa.

Muryar Jummai ya tsinkaya tana Faɗin “Na shiga Uku, don Allah Habeeb ka rabu da ni”.

Gabanshi na wata irin faɗuwa ya zagaya ɗakin Habeen, tare da banka ƙofar ɗakin da ƙarfi ya shiga.

Mutuwar tsaye ya yi lokacin da idanunsa suka dira a kan Habeeb da ke  riƙe da Jummai a hannu.

Cikin ƙaraji ya ce “Habeeeeeb.”

A gigice Habeeb ya saki Jummai tare da waigowa suka yi ido huɗu da Abbanshi..

Kunya da tashin hankalin da Habeeb ya samu kansa a ciki basu misaltuwa, hannayensa na kyarma ya ɗauki gyalen Jummai tare da rufe mata jiki dashi.

Ita kuwa idan ba kuka ba abin da bakinta ke yi.

Jikinshi na ɓari ya sauko daga kan gadon, wurin Abbanshi dake tsaye tamkar soja ya nufo.

Aikuwa tsayawarshi ta yi daidai da sadda Abbanshi ya sauke mashi lafiyayyen mari a kumatu, wanda sai da komai nashi ya tsaya sakamakon wannan mari.

Firgigita Habeeb ya tashi daga baccin da yake, hannunsa da fe da kumci, lokaci ɗaya kuma bakinshi na furta “Inna li Llahi wa inna ilaihi raji’un.”

“Me ya ke faruwa da ni ne?” Ya tambayi kansa.

Idanu ya shiga rabawa cikin ɗakin yana son gane gaskiyar abin da yani yanzu.

Ganin ba Abbanshi a tsaye, sannan kuma ba Jummai a kan gado ya tabbatar mashi da mafarki ne ya yi.

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke tare da dafe kansa da ke ta sarawa sakamakon firgicin da falka da shi.

Ƙunci cike da ziciyarshi ya ce “Me hakan ke nufi?”

Wani sashe na zuciyarshi ya ce, “Abin da kake ƙudurtawa a zuciyarka ne ka fara gani a cikin mafarki”.

“Tir!” Ya furta a fili, tare da jin tsanar kansa.

Hannayensa ya ɗaga sama ya fara addu’a kamar haka, “Allah ka tsare ni daga sharrin wannan mafarki, sannan ka kiyaye ni daga aikata abin kunya.”

Yana gama addu’ar ya shafa tare da miƙewa ya nufi banɗaki.

Wanka da alwalla ya yi don ko kusa bai gamsu da tsaftar jikinshi ba, yana gamawa ya fito tare da chanja kaya ya nufi Masallaci, don gabatar da sallar Magrib.

Bai dawo ba har sai da aka yi isha’i. Wayarsa da ke maƙale a chaji ya duba, kiran Ummanshi ya ne ya shigo a wayar.

Tamkar wanda bai da lafiya ya ɗaga wayar, tana jin muryarshi ta ce, “Ya na ji muryarka a haka, ko baka da lafiya ne?” 

Ya ce “Wallahi kaina ke ciwo Umma.”

Sannu ta yi mashi, haɗi da umurtar shi da ya sha magani kafin ya kwanta.

“Toh” ya ce, tare da tambayar ta yaushe zata dawo daga Saudiyyar?” 

Amsa ta bashi da”Nan da sati ɗaya, saboda ban gama ganin likita ba,” Fatan dawowa lafiya ya yi mata, sannan suka yi bankwana ya aje wayar.

Turus ya zauna a gefen gado, don har yanzu mafarkin ci mashi rai yake.

“Oh, da ace da gaske ne ya zan yi da Abbana?”, tambayar da shiga yi ma kansa kenan.

kai ya girgiza don ya san sakamakon amsar ba zai yi kyau ba.

Faɗa sosai ya yi ma kansa akan watsi da duk wani ruɗi na shaiɗan da ke taso mashi a zuciya, sannan ya ƙudiri yin nesa da Jummai don hakan ne kaɗai mafita.

Yana gama yi ma kansa faɗa ya ɗauki makullin mashin ya nufi gidansu Nasir domin karatun Exam ɗin da ke tunkaro su.

Bai dawo gida ba sai shaɗaya saura. bai wani nemi abinci ba don ya cika cikinsa a gidansu Nasir.

Key ya sa ma ƙofar tare da kashe fitilar ɗakin, kai tsaye gadonsa ya haye ya kwanta, cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya tafi da shi.

Tun daga wannan rana Habeeb ya fara wasan ɓuya da Jummai, idan ya fita tun safe, bai dawowa gidan sai an yi isha’i.

Aikuwa Jummai ta rasa inda zata sa kanta saboda kewar shi, bini-bini tana waje don ganin ko zata ganshi.

Uwani kuwa dashi da babu duk ɗaya suke a wurinta, don haka bata damu da ɗauke ƙafar da ya yi musu ba.

Tamkar marar lafiya Jummai ta koma, har Uwani ta fara tunanin ko gida ta ke so.

Shima juriya kawai yake, amma ba don ransa ya so yake nisa da sahibarsa ba.

Da safe yana cikin kulle ɗakinshi ya ji takun mutum a bayansa, yana waigawa ya ga Jummai.

Rasss!  Gabanshi ya faɗi, take mafarkin da ya yi rannan ya faɗo masa a rai.

Itama faɗuwa gabanta ya yi lokacin da taga ya haɗe fuska, tunani ta shiga yi ko ya dena son ta ne, don bai taɓa yi mata irin haka ba.

Jiki a sanyaye ta juya zata koma inda ta fito.

“Fateemah” ya kira sunanta, don ya fahimci kamar ranta ya ɓaci.

Ƙin tsayawa ta yi ta cigaba da tafiya, bayanta ya bi tare da cigaba da kiran ta, amma taƙi sauraronshi.

Bai ji daɗin haka ba. Ciki ya shiga shima, ya same ta kwance falo tana sharɓar kuka.

Daidai saitin kanta ya tsaya “Ki gafarce ni Teemah, yanzu school zan je, idan na dawo zamu yi magana”.

Yana faɗin haka ya juya ya fita.

Kuka ta cigaba da yi, Uwani na fitowa ta shiga zazzaga mata masifa, wai ta gaji da wannan sakarcin da ta tsiro mata, idan gida take so, toh ta tattara kayanta ta koma.

Shiru Jummai ta yi tana ta sauke ajiyar zuciya.

Da Yamma Habeeb na dawo wa daga school ya shiga ɗakin Uwani.

Zaune ya same su a falo, Jummai na mata tsifar kai.

Gaisawa suka yi da Uwani, ta tambaye shi ina ya shige kwana biyu?

Idonsa na kan Jummai da ke ta haɗe rai ya ce “Exam mu ke, shiyasa bana zama.”

Allah yayi jagoranci Uwani ta yi masa, ya ce “Amiin ya Allah.”

Fuskarsa da ƴar dariya ya dubi Jummai ya ce, “Jumale yau ba magana.”

Baki Uwani ta ta ɓe ta ce “Tana jin wulaƙanci fa ya za’a yi ta yi magana.”

Dariya ce ta kusa suɓuce ma Habeeb, “Toh ko gida take so?”

Uwani ta ce “Ai jibi dai zata tafi kowa ma ya huta, ni ba zan juri baƙin ranta da ta tsira ba kwananan ba.”

Baki buɗe ya kalli Jummai da ke shirin fashewa da kuka.

Fakar idon Uwani yayi ya ɗaga mata hannu alamar “Sorry”

Haɗe kukan ta yi, ta cigaba da tsefe ma Uwani kai.

Hira suka riƙa yi da Uwani, amma idonsa na kan english wears ɗin da ke jikin Jummai, wadda rigar ta fiddo da duk wani shape na jikinta.

Take lakkar jikinsa da saki, sha’awar da kullum yake yakicewa a zuciyarshi ce ta taso mashi.

Duk yadda ya so hana kansa satar kallon Jummai amma ya kasa.

Ita kuwa tunda ta lura da haka ta sadda kanta ƙasa.

Yana nan zaune har ta gama tsifar, Uwani na tashi ta ce ma Jummai

“Ki nemo Hijabinki, yanzu zanje kitson,” tana gama faɗin haka ta nufi bedroom.

Habeeb ya ji daɗin shigewarta don magana yake son yi da Jummai.

Idonsa a kanta ya ce “Ina ne gidan kitson?”

Taƙaitacciyar amsa ta bashi da “Nan baya ne.”

“Toh Mu haɗu a can,” ya faɗa, don ya gane gidan kitson.

Tashi ya yi ya koma ɗakinshi.

Itama Hijabinta ta ɗauko ta sa, Uwani na fitowa suka nufi gidan kitso.

Saida aka fara ma Uwani kitson sannan ta tashi zata  fito,

Uwani ta ce “Sai ina?” Ta ce “Gida zan je.” Tana gama faɗin haka ta zura takalma ta yo waje.

Tsaye ta same shi jikin wata bishiya dake kusa da gidan. Yadda take ta haɗe fuska ne ya kusa sashi dariya, “Mu je can Ranki ya daɗe” ya faɗa lokaci ɗaya kuma yana nuna wani dakali dake nesa da gidan.

Ba tare da tayi magana ba ta juya suka nufi dakalin suka zauna.

Shiru ce ta ratsa, daga bisani Habeeb ya dube ta “Wai wannan fushi duk na miye Teemah?”

Sake haɗe rai ta yi tana jin wani ƙululu a zuciyarta, wato bai ma san dalilin fushinta ba, a tsiwace ta dube shi “Tambayata ma kake ko, bacin kuma kai ne sanadi”.

Murmushi ya yi tare da faɗin “Toh Allah ya baki haƙuri, na san dai kwana biyu bamu haɗu ba, kuma Exam ce ta sa haka…”

Katse shi ta yi da “Toh ɗazu kuma haɗe ran me kake don na je ɗakinka, na fara zargin ka gaji da ni.”

Kai ya girgiza yana dariya “Toh ya bazan haɗe rai ba, kina budurwa ki je ɗakin saurayi?”

Ta ce “Toh laifi ne don na je?”, ya ce “Laifi babba ma wallahi, zaki ja ma kanki ne, ko so kike in murƙushe ki cikin ɗaki?”

Ido ta zaro “Murƙushewa?” ya ɗaga mata kai, “Murƙushewa kuwa, kuma ba mai ƙwatarki.”

“Wallahi da sai na tara maka mutane.”

Ya ce “Daga baya kenan”, Nuna mata illar haka ya yi, duk budurwa mai kamun kai ba zata je neman saurayi a ɗakinsa ba, idan har hakan ta kama, toh tana iya aikawa a kirawo mata shi, amma ba ta je da kanta ba.

Sosai ta gamsu da bayanan shi, ɗaukar ma ranta ta yi akan ba zata sake ba.

Haƙuri shi kuma ya bata da kalmomi masu tausasa zuciya, tare da nuna mata har abada ba zai guje ta ba.

Basu gushe ba sai da fushin da Jummai ke yi ya tafi.

Batun komawar ta gida ya tambaye ta, shin da gaske ne jibi zata tafi?

Tabbatar mashi ta yi da haka, take ya shiga damuwa, don bai san irin yanayin da zai shiga ba idan ta tafi.

“Wallahi Fateema bana so ki tafi” ya faɗa fuskarsa ɗauke da damuwa.

Murmushi ta yi “Toh ya za’a yi, sati na uku fa, kuma an koma school.”

Kai ya gyaɗa “Hakane, yanzu a jinki nawa a school?”

Tace “Ss two”

Ya ce “Ashe da sauran lokaci kafin mu yi aure.”

Ta ce”Da saura kam, tunda har Jami’a sai na je.”

Ido ya zaro “Ke Fateemah?” Ta ce “Wallahi”

Dariya ya yi “Taɓ, toh me kike son ki zama idan kin yi karatu?”

Ta ce “Likita”

“Babbar magana, ai Wallahi ba zan iya jiranki har ki zama likita ba.”

Ta ce “Toh wata zaka samu kenan?”, ya ce “A’a, ke ɗin dai ce, idan kin je gidana kya ƙarasa karatun a can”.

Dariya Jummai ta yi, don duk da gaske take ɗaukar zancenshi, shima gskiya ce tsantsa a cikin magarshi ba ƙarya.

Haka suka yi ta hira, yana ta yi mata daɗin baki irin na maza, basu tashi ba sai da Jummai ta sallama mashi dukkan yaddarta a kanshi.

Gidan kitson ta koma, shi kuma ya koma gida.

Ana gobe Jummai zata koma ta fara haɗa kayanta.

Alhaji Mainasara ya bata kuɗi haɗi da yadi goma na shadda mai kyau ta kai ma babanta.

Uwani kuma ta yi mata ɗinkuna haɗi da bata yar qaramar waya.

Habeeb ma ya siwo mata kayan maƙulashe, wanda sai da uwani ta yi mamakinsu.

Bayan ya fita Uwani ta dubi Jummai “Waɗannan kaya da Habeeb ya siyo maki, anya kuwa ba wani abu a tsakaninku?”.

“Wani abu kamar me Aunty” Jummai ta tambaya.

Uwani ta ce “Ban sani ba, ki faɗa mani gaskiya, me ye tsakaninku ki da shi.”

Shiru Jummai ta yi, daga bisani ta ce “Wai so na ya ke Aunty.” 

“Ke kuma kika ce mashi me? “, Uwani ta sake tambayarta.

Shirun da Jummai ta yi ya tabbatar mata da itama tana son shi.

“Toh ki yi a hankali Jummai, kada ki koya ma kanki son abin da, da wahala ki same shi, kin ga dai irin zaman doya da manjarn da ke tsakaninmu da su, abu ne kuwa mai wahala a yadda ku yi aure, don haka ki bi a hankali”.

Har Uwani ta gama magana Jummai bata ce komai ba, sai da Uwanin ta ce “Kin ji dai me na gaya maki ko?”, sannan ta ce “Eh Aunty”

Washe gari Uwani na ta shiri don ita zata raka Jummai gida, sai ga wayar Alhaji Mai Nasara, cewar ta dakata da tafiyar saboda yau Hajiya Mairo zata dawo.

Uwani bata so haka ba, amma saboda biyayyar da ta ke ma mijinta sai ta haƙura.

Haƙuri ta ba Jummai akan ta bari sai Hajiya Mairo ta dawo, Jumman ta ce C.A Test zasu fara a school.

Ƙarshe dai aka yanke shawarar ita kaɗai zata koma.

Habeeb kuwa yana can yana yaƙi da zuciyarshi dake son fin ƙarfinshi, sakamakon  mafarkin da Jummai da ya sake yi a daren jiya.

Wurin ƙarfe goma Jummai ta caɓa ado, ta fito falo.

Habeeb da ta gani zaune yana ta raba ido.

Da murmushi suka tari Juna.

Ya ce “Tafiyar ta tashi kenan,” ta ce “Yanzu ma kuwa”, kai ya langaɓe alamar zai yi kewarta. 

Dariya kawai ta yi, ta koma ɗaki ta fiddo kayanta.

Uwani na fitowa ta ganshi “Yauwa Habeeb, don Allah ka miƙa Jummai a tashar mota.”

Ya ji daɗin haka, cikin zumuɗi ya tashi ya fita, kan kace me ya fiddo mota, da shi da ita suka sanya kayan a motar.

Uwani na lura da yadda yake ta zumuɗi tace a ranta “Ƙwalelenka wallahi, irin marassa mutunci.”

Ciki Jummai ta dawo suka yi bankwana da Uwani, Uwanin ta tabbatar mata da suna nan tafe suma.

Kamar su duka zasu yi kuka, musamman Uwani da Jummai ke ɗebe mata kewa.

Mota Jummai ta shiga, Habeeb ya ɗauke ta suka fita.

Hancin shi buɗe yana shaƙar ƙamshin turarenta da ya game cikin motar ya juyo, “Fateema, kamar murna kike ko?”

Ta ce “Toh zan ga mahaifana ba dole in yi murna ba.”

Murmushi ya yi ya ce “Hakane”, yana faɗin haka ya tsaida motar.

“Lafiya ka tsaya? ” ta tambaye shi.

“Pics nake son mu yi, kin san na rasa duka pics ɗinki da ke wayata.”

Yana gama faɗin haka ya buɗe motar ya fito, itama fitowa ta yi tare da zagayowa ɓangaren da yake.

Wani irin kallo ta ga yana yi mata, ta ce “Lafiya”

Sai da ya lumshe ido sannan ya ce “Ba komai”

Fiddo wayarshi ya yi daga aljihu, tare da fara ɗaukarta pics, yadda take ta styles kala-kala ne ya burge shi, “Wallahi kina da kyau” ya faɗa yana dariya.

Bayan ya gama yi mata ya ce “Toh mu yi Selfie”,  ba tare da tunanin komai ba ta matso, suka fara ɗauka.

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke lokacin da jikinsa ya haɗu da nashi, ƙara shige mata ya yi suka cigaba da ɗaukar pics ɗin, suna gamawa ya ce “Mu je ko?”.

“Toh” ta ce, ta koma ciki.

Jiki a sanyeyae shima ya koma, don ta sosa mashi inda yake yi mashi ƙaiƙayi.

Shiru ya yi yana ta saƙa da kwancewa a zuciyarshi, Jummai kuwa bata lura ba don idonta na kan waya tana kallon pics ɗin.

Tsaida motar da ya yi ne yasa ta juyowa ta kalle shi, sai ta ga ya ɗan jingina da bayan kujera ya lumshe idanu.

Kiran sunanshi ta yi “Ya Habeeb.”

Shiru yayi kamar bai ji me ta ce ba.

Aikuwa sai jin hannunta ya yi a kan cinyarshi “Yaya Habeeb.”

Wani irin tsau ya ji, zata janye hannun kenan, ya yi maza ya riƙe.

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 6Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.