Skip to content
Part 9 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Mamaki tare da tsanar Habeeb ne suka sa Jummai dena kukan da take.

“Lallai Habeeb ka amsa sunanka Namiji, mai hali irin na Ɗan kunama.”

Abin da ta faɗa kenan a ranta, lokaci ɗaya kuma ta raka bayan motarshi da idanunta da take jin kamar zasu faɗo saboda raɗaɗi, har sai da ya ɓace ma ganinta sannan ta ƙyafta idanun.

Wani irin ruɗani ne ta samu kanta a ciki, duk tabbacin tana da ciki da ta samu a sibitocin da suka je bai sa ta gazgata hakan ba, har sai da ta je wata asibitin.

Abin da sauran suka faɗa mata, nan ma shine. Tamkar zautacciya ta fito daga asibitin,”Yanzu ya zanyi da wannan bala’i, da wace irin fuska zan kalli iyayena?”

Kai ta girgirza sannan ta cigaba da magana a fili.

“Kai ya zama dole ma Habeeb ya karɓi wannan cikin, sannan dole mu san abin yi tun kafin asirinmu ya tonu”.

Tana cikin wannan magana ne wani Mai Napep ya tsaya a gabanta “Hajiya tafiya ne?” ya faɗa tare da ɗan leqo da kanshi waje.

Kai ta ɗaga mashi alamar “Eh”, sannan ta shiga, faɗa mashi inda zai kaita ta yi, sannan ta maida kanta cikin Hijabi ta cigaba da fitar da hawayen takaici.

Har aka zon wurin da za ta sauka bata sani ba, sai da mai napep ɗin ya ce “Hajiya mun zo wurin”.

Goge fuskarta da hijabi ta yi, sannan ta fito ta bashi kuɗin ya tafi.

Yar tafiya kaɗan ta ƙara, sannan ta zo ƙofar gidan, Kafin ta shiga sai da ta goge duk wani hawaye dake idonta duk don kada a gane ta yi kuka.

Sai dai kuma kumburin da idanunta suka yi ya sa Uwani faɗin “Kukan shagwaɓar ne kika yi musu a can ko?”

Cikin muryar kuka ta ce “Toh ban da lafiya fa”,tana gama faɗin haka ta shige ciki, ba tare da faɗa mata ba’asin asibiti ba.

Baki Uwani ra taɓe don gani take duk ragwancinta ne.

Kan gado ta faɗa tare da fashewa da kukan baƙinciki da nadamar ba Habeeb kanta, gashi tun ba’a je ko ina ba ya ɓata mata rayuwa kuma ya guje ta.

“Allah ya isa ce tsakanina da Habeeb, kuma wallahi sai ka karɓi wannan cikin tunda ba wanda na taɓa ba kaina sai kai.”

Haka ta riƙa kuka tana maganganu tare da neman sakayyar zaluncin da Habeeb ya yi mata a wurin Allah.

Tana cikin kukan wani irin amai ya taso mata, ba arzki ta tashi da gudu ta nufi banɗaki.

Uwani na falo ta riƙa jiyo kakarin amanta, da hanzari ta shigo ɗakin ta ce “Wai abin har ya kai haka.”

Ruwa ta zuba mata ta wanke jikinta, bayan ta fito Uwani ta wanke banɗakin.

Kwance Uwani ta same ta tana ta maida numfashi, “Sannu” ta ce mata, sannan ta nemi ta bata takardar maganin da ta dawo da ita daga asibiti.

Miƙa mata ta yi, Uwanin na karɓa ta ce “Bari in ba Habeeb ya karɓo maki maganin.”

Kamar Jummai ta ce kada a bashi, sai kuma ta yi shiru, Uwani na fita ta fashe da matsanancin kuka.

Habeeb na zaune ɗakinshi yana ta fargabar kada Jummai ta fasa wannan magana ya shiga Uku, duk da ya na ji a jikinshi ba shi ya yi mata ciki ba, amma ba zai fita ba tunda ya taɓa kusantarta.

Yana cikin wannan tunani ne ya jiyo muryar Uwani na kiranshi a bayan window.

Ras! gabanshi ya faɗi, cike da tsoro ya amsa tare da yaye labulen ya ce “Aunty”

“Don Allah Jummai zaka karɓo ma magani, bata jin daɗi.”

Karɓar tarkardar haɗe da kuɗin da ta ziro mashi ya yi “Ok”, tana juyawa ya zauna turus! a kan kujera.

“Lallai Zaman wannan yarinyar barazana ne a gidannan, domin zata cigaba da rashin lafiya, ƙarshe a gano tana da ciki, kuma idan aka tambaye ta zata ce ni ne.”

Zumbur ya miƙe tsaye “Wallahi ba zan bari ta sa ni a uku ba, ya zama dole ma ta bar gidannan.”

Tashi ya yi ya fita, cikin ranshi yana saƙa irin matakin da zai ɗauka akan Jummai, don muddin ta cigaba da sanya shi acikin maganar cikinta, toh ya shiga uku a wurin mahaifansa.

Kai tsaye chemist ya nufa ya siyo maganin, yana dawowa ya nufi ɗakin Uwani.

Shigarsa kuwa ta yi daidai da lokacin da Uwani ke ma Jummai faɗan lambo tana faɗin “Sai wata muɗuɗɗuka kike kamar mai ciki.”

Kusan a tare Habeeb da Jummai suka kalli juna, a tunainsu Uwani ta gane Jummai na da ciki.

Take tsanar da suke wa juna ta ƙaru, a hankali suka ɗauke kawunansu,  kowa na saƙa irin matakin da zai ɗauka.

Miƙa ma Uwani maganin ya yi, ba tare da ya yi magana ba ya fice daga ɗakin.

Faɗin fargar da suka samu kansu a cikinta ɓata lokaci ne. Da ƙyal Jummai ta iya haɗiye maganin da Uwani ta ɓallo mata. 

Wasu mata ne dangin Alhaji Mai Nasara suka zo yi ma Uwani barka, tashi Uwani ta yi suka koma bedroom, don ƙawayenta ne sosai. 

Hakan ya ba Jummai damar fita ta nufi ɗakin Habeeb.

Samun shi ta yi yana ta kai da kawowa a tsakiyar ɗakin, yana ganinta ya tsaya chak tare da ƙara murtuke fuska “Me kuma ki ka shigo yi mani a ɗaki.”

Ido ta lumshe tare da matse wasu zafafan hawaye ta ce “Yanzu ni ce kake juya ma baya, bayan duk halinda na shiga kai ne sanadi.”

Tana gama faɗin haka ta ƙaraso tsakiyar ɗakin.

Cikin fushi ya ce “Kada ki sake cewa ni na saka ki a wannan halin,” ta ce “Toh waye idan ba kai ba, wallahi dole ka karɓi wannan cikin tun kafin asirinmu ya tonu, idan ba haka ba wallahi zan ce kai ne.”

Ai yana jin ta ce haka ya fizgo ta tare da wanka mata mari, don tun a mota yake ƙule da ita, “Dan Ubanki kice ni ne ki ga yadda zan maki, kin je can wurin karnukan ƙauyenku sun ɓata ki, shine zaki liƙa mani, toh ƙaryarki ta sha ƙarya yarinya.”

Hannunta dafe da kumci ta ce “Wallahi Allah ya isa ban yafe ba, kuma wallahi muddin aka gane, kuma aka tambaye ni, kai zan ce”

Shaƙaro ta ya yi, tare da ɗaukar wuƙar da ke kan table ya sa mata a wuya “Wallahi kika ce ni ne sai na kashe ki, don haka ki iya bakinki.”

Wani irin tsoro ne ya kama Jummai, take ta shiga karkarwa, don a yadda ya yi mata, ta tabbata zai iya kashe ta.

So take ta ƙwaci kanta, amma tsoron kada ya yanke ta da wuƙa ya sa ta tsayawa cak.

Kashedi ya cigaba da yi mata akan ta yi gaugawar bar musu gida, kuma idan ta sake ya ƙara ganin ta zo gidan, kai ko birni ya ji labarin ta zo sai yasa an yi kidnapping ɗinta.

Da yake matsoraciya ce, sai ta yadda da duk abin da ya ce zai mata, take bakinta ya mutu, ba abin da idanunta ke yi sai fitar da hawaye. Yana sakin ta ta yi waje da gudu tana kuka.

Tun daga wannan rana Jummai bata sake bari suka haɗu da Habeeb ba, ana yin sunan Uwani kuma ta bi Asabe suka koma gida, duk da Uwanin ta so ta tsaya, amma ta ce Islamiyya an fara dukan masu ƙalula.

Rashin lafiyar da take ta samu sauƙi, sai dai fargabar kada a gane tana da ciki ce duk ta figar da ita, gaba ɗaya ta rage cin abinci, don bai ma birge ta.

Yardar da ta yi ma Halima ce ta sa ta samun ta har gida ta faɗa mata tana da ciki, aikuwa hankalin Halima ya tashi, ta ce “Me ya ja maki wannan bala’i Jummai?”.

Cike da baƙinci Jummai ta ce “Ƙaddara Halima, ni baƙincikina abin da Habeeb ya yi mani, cewa ya yi sai ya kashe ni idan na ce shine, kuma wallahi cikinshi ne Halima,” tana gama faɗin haka ta rushe da kuka.

“Ya Salam” Halima ta faɗa tare da dafe kai, gaba ɗaya kanta ya kulle, gani take kamar almara.

“Toh wai Jummai me ya kai ki ba namiji kanki, shi fa duk abin da ya yi ado ne, ke kuma tabo ne a wurinki ke da iyayenki da ƴaƴanki.”

Cikin kukan Jummai ta ce “Halima ni ina kallon wannan a matsayin ƙaddara kawai, amma ba zan iya ce maki ga yadda aka yi har na amince ba.”

Maganganu suka cigaba da yi, har dai Jummai ta bayyana mata buƙatarta, a kan zata zubar da cikin kafin a gane, don idan aka gane, toh ta shiga uku a wurin mahaifanta da kuma mutanen gari.

Cike da damuwa Halima ta ce “Mutuwa fa ake Jummai.”

“Toh Halima ai gwara in mutu da inga ranar tonuwar asirina.”

Dafa kafaɗarta Halima ta yi, “Ki dena faɗin haka, Insha Allah zan taimaka maki a zubar dashi, kuma ba za’a samu matsala ba da iznin Allah.”

Jummai ta ɗan ji daɗin maganarta. Birni suka tsara zasu je a cire cikin, idan sun tashi a gida zasu ce suna cikin ɗaliban da aka zaɓa debate a makarantarsu, idan ranar da za’a tafi ta yi, sai su yi tafiyarsu Asibiti.

Yadda suka tsara haka suka yi, sai dai da baƙinciki suka dawo, domin ba asibitin da aka yadda za’a zubar ma Jummai da ciki sai guda ɗaya, ita kuma wanda zai zubar ɗin sai da ya buƙaci kuɗi, waɗanda basu dasu, kuma basu da dalilinsu.

Kuka sosai Jummai ta riƙa yi, tare da nadamar ba Namiji kanta, yanzu shi yana can hankalinshi kwance, ita kuma ya bar ta cikin tashin hankali.

Haƙuri da magana Halima ta riƙa bata, akan ta ɗauki wannan a matsayin ƙaddararta, sannan kuma ta yi mata alƙawalin ba zata bari wani ya san da wannan magana ba.

Haka Jummai ta kasance cikin baƙinciki da nadama, tunda ta lura da cikinta ya fara girma ta cigaba da sanya hijabi, burinta idan Allah ya bata sa’ar haihuwa ba tare da sanin wani ba, sai ta kai yaron bayan gari ta a je.

Tafiya na ta tafiya har cikinta ya cika wata bakwai ba tare da wani ya sani ba, duk da damuwar da take ciki,  bai hana ta yin ƴar ƙiba ba, Asabe na lura ta ce “Yarinya kin samu lafiya”

Rana mafi tashin hankali a wurinta itace ranar da Asabe ta gane tana da ciki, shima bata yi zaton Asabe na tsakar gida ba.

Hannunta riƙe da Hijabi ta fito.

Aikuwa idon Asabe ba inda ya dira sai kan cikinta, a kiɗime ta taso daga inda take ta yo kanta, sallallamin da Asaben ke yi ne yasa ta ruɗewa. 

Take ta riƙa fatan ta farka daga mafarkin da ta ke yi tun kafin Asabe ta ƙaraso inda take, sai dai fizgar da Asaben ta yi mata ce ta sa ta dena wannan fata, domin a zahiri ne hakan ke faruwa ba mafarki ba.

***** *****

Nisawa Asabe ta yi sannan ta ce “Malam ko dai Uwar yaro nan ce ta sa shi ya ɓata mana ƴa, duk don ta rama abin da muka yi mata.”

Kai Malam Amadu ya girgirza tare da faɗin “Haba Asabe, wace irin uwa ce zata sa ɗanta ya aikata irin wannan ɓarnar.”

“Da alamu dai Malam ka manta wace ce Mairo.”

Ya ce “Ni kam ya za’a yi in manta Mairo, ni da ta kusa ja ma sharri a gari, amma kuma duk mugun halinta ba zata sa ɗanta ya aikata alfasha ba.”

Shiru Asabe ta yi, bangare ɗaya kuma tana ta kaɗa ƙafafu, don abin na matuƙar cizon ta a cikin rai.

Aje magana suka yi cewar gobe zasu yi sammako zuwa gidansu Habeeb, don a sanar da mahaifansa irin aika-aikar ya yi ma ƴarsu.

Duk da Malam Amadu bai so hakan ba, shi abin da ya so shine su rungumi ƙaddara, domin abu ne mai wahala Hajiya Mairo ta yadda da laifin tilon ɗanta.

Tun a daren Asabe ta kira Uwani, tare da shaida mata gobe zasu zo.

Murna Uwanin ta fara yi, sai da ta ji Asabe ta ce “Idan Alhaji Mai Nasara na gari, ki ce don Allah kada ya fita, don wurinsa zamu zo?”

“Lafiya dai ko Yaya Asabe?”, Uwani ta tambaya don basu taɓa cewa zasu zo wurinshi ba.

Kamar Asabe zata yi kuka ta ce “Ina fa lafiya Uwani, Shegen ɗanshi Habeeb ya kai mu ya baro”.

“Kamarya haka?” Uwani ta sake tambayar Asabe.

“Ciki ya yi ma Jummai.”

Sallallami Uwani ta shiga yi tare da zama jagwab akan kujera, lokaci ɗaya kuma ta tsinke kiran don bakinta ya mutu.

Hannu ta ɗora akai ta yi ta rizgar kuka, don tabbas sun gama wulaƙanta a idon duniya.

A wannan dare Uwani bata rumtsa ba saboda tashin hankali.

Da safe Alhaji Mai Nasara na shigowa ya ga idanunta duk sun kumbura alamar ta kwana tana kuka.

Cike da damuwa ya tambaye ta abinda ya sa ta kuka.

Kasa bashi amsa ta yi, saima wasu hawayen da ta cigaba da fitarwa.  Lallashinta ya shiga yi,

Ba don ranta ya so ba tayi shiru, faɗa mashi ta yi akan kada ya fita, su Asabe zasu zo.

Ya ce “Ko wani abu ya faru ne?” shiru ta yi, ya ce “Toh Allah ya kawo su lafiya, daman yau ba zan fita ba ai”.

Cike da tunanika ya baro ɗakin Uwani, tabbas akwai abin da ya faru marar daɗi, sai dai yana fatan Allah ya sa wanda zasu iya ɗauka ne.

Wurin ƙarfe goma su Asabe suka iso unguwarsu Uwani. ƙofar gida Malam Amadu ya tsaya, Asabe da Jummai kuma suka shiga ciki.

Uwani na ganinsu ta tashi tare da rungume Asabe suka dasa sabon kuka.

Jummai kuwa kasa ƙarasowa ta yi cikin falon, kunyar Uwani da baƙinci ne suka hana ta shigowa.

Wani mugun kallo Uwani ta yi mata, wanda dole ta sadda kanta ƙasa,

“Yanzu Masifar da kika jawo mana kenan Jummai, duk faɗan da na yi maki akan ki rabu da Habeeb baki ji ba ko.”

Asabe ta ce “Au dama kin san suna tare?”

“Alama na gani yana sonta, kuma tun kafin a je ko ina na yi mata faɗa, ashe bata ji ba har sai da haka ta faru.”

Suna cikin wannan magana ne sai ga Alhaji Mai Nasara, ciki Jummai ta ƙaraso don ya samu hanyar wucewa.

Zama ya yi suka gaisa dasu Asabe, daga bisani ya ce “Uwani ta ce zaku zo, Allah dai ya sa lafiya.”

Shiru Asabe ta yi, don ba zata iya faɗa mashi abin da ke tafe dasu ba, saboda kunyar shi da take ji.

“Malam na waje, kwa iya ganawa Alhaji” Asabe ta faɗa kanta na ƙasa. 

“Toh ba damuwa” ya faɗa tare da miƙewa ya nufi waje wurin Malam Amadu.

Da fara’a suka gaisa, sannan ya yi mashi iso har rumfar da yake ganawa da mutane idan sun zo.

Wata gaisuwar suka ƙara yi, daga bisani Malam Amadu ya zayyana mashi abin da ke tafe da su, cewar ɗansa Habeeb ya yi ma Jummai ciki.

Tamkar almara Alhaji Mai Nasara ya ji wannan magana, “Malam ka kuwa san me kake faɗi”, don a tarbiyyar da ya ba Habeeb bai tunanin zai aikata haka.

Murmushi Malam Amadu ya yi “Kwarai kuwa Alhaji, yarinya ta faɗa da bakinta shine wanda ya yi mata ciki, har ma yana iƙrararin kashe ta idan ta faɗa.”

Tashin hankali ba’a sa maka rana, lallai yaran yanzu sanin gaskiyar halinsu sai Allah.

A kiɗime ya tashi ya koma ɗakin Uwani, cikin tashin hankali ya ce “Jummai mi ye gaskiyar magana.”

Kukan da take saboda faɗan da su Uwani ke yi mata ya hana ta magana.

Kamar zai yi kuka ya duƙa gabanta, “Kada ki ji komai, Habeeb ne? Jummai ta ɗaga kai alamar “Eh”

Wata irin juwa ce ta kwashe shi, zama ya yi kan kujera tare da dafe kai, wane irin bala’i ne wannan, ashe ɓarnar da Habeeb ke yi kenan, duk Nasihar da yake yi mashi akan ya kiyayi mata, ashe bata shiga a kunnensa ba.

Shiru ɗakin ya yi, kowa da irin zafin da yake ji a ranshi.

“Ashe ba banza ba Habeeb ya matsa mani akan zai bar ƙasar, ya san ɓarnar da ya aikata, Maganar da Alhaji Mai Nasara ke ta maimaitawa a ransa.

Zumbur ya miƙe ya nufi ɗakin Hajiya Mairo.

Samun ta ya yi tana shirin fita, cikin ɓacin rai ya ce “Sai ki aje gyalen, ga ɗanki nan ya jawo mana bala’i har gida”.

Sanin Habeeb bai ƙasar ta ce “Daga Wajen ya aiko mana da bala’in ko yaya?”

“Ko daga ina ne ma zaki gani” yana gama faɗin haka ya fito.

Kiran su Asabe ya yi su duka hada Malam Amadu suka shigo ɗakinta, tana ganinsu ta yamutse fuska “Waɗannan masu kama da shanun fa?”

Wani mugun kallo Asabe ta jefe ta da shi.

“Toh ko har a ɗakina ma tsiyar za’a yi mani” Hajiya Mairo ta faɗa tana kallon Asabe.

Asabe bata ce komai ba, don kunyar da take ma Alhaji Mai Nasara.

Zama su duka suka yi, Alhaji Mai Nasara ya nuna Jummai “Ga ta nan haihuwa ko yau ko gobe, kuma ɗanki Habeeb shi ne Uban ɗan, don haka sai ki shirya tarbar jaririn da jarabar ɗanki ta siyo maki.”

Wani mutum kallo Hajiya Mairo ta wurga ma Alhaji Mai Nasara “Duk da ban cika gane azancin maganarka ba, amma na fahimci wannan, kana nufin Asabe ta turo ɗiyarta birni yawon karuwanci ta yi ciki, duk don su ja mana sharri.”

Aikuwa wannan magana ta hasala Asabe, kamar wadda aka tsikara ta miƙe tare da nuna ta da yatsa “Ke matsiyaciya, ko kuma kin sa ɗanki ya ɓata mani ƴa duk don ki huce takaici ba.”

Murumushin mugunta Hajiya Mairo ta yi, “Maida wuƙar Asabe, ki ji da abin kunyar da ke gaban ƴarki ba rigima ba, ni nan da kike ganina na sha gabanki wallahi, ɗana Habeeb ko yana zina bana tunanin zai yi da banzar ɗiyarki ƴar ƙauye, bare kuma tarbiyyar da muka bashi ba zai ja mana abin kunya ba.”

Tsawa Alhaji Mai Nasara ya daka ma Hajiya Mairo, ta ce “Ka dena yi mani tsawa Alhaji, har ɗakina aka shigo, don haka ba zan lamunci iskanci ba.”

Tsaye ta miƙe tare da cigaba da magana “Kai wallahi ni ba zan lamunci wannan ba, a can baya ƙarfina ne ke raba ni da waɗannan sheggun, a wannan karon kuwa sai na haɗa da shari’a wallahi, don haka ma ki lallaɓi ƴarki ta faɗa maki karen da yayi mata ciki tun kafin mu je ga hukuma.”

Abu kamar wasa sai Uwani da Asabe suka miƙe tare da cigaba da zaginta, Uwani ta ce “Kare ya wuce ɗanki Habeeb, kuma ai ku ne sheggu masu baƙin halin gado, shari’a kuma ki je duk inda zaki, ko kin ƙi ko kin so ɗanki ne ya yi ciki”.

Alhaji Mai Nasar da Malam Amadu duk kansu ya kulle, hana su suke amma kamar ba su jin me suke cewa.

Zagi ta uwa ta uba suka riƙa yi ma Juna, Hajiya Mairo ta ce “Kai ba zan sake cewa ba Habeeb bane, ciki ko? to ya je ya yi, kuyi abin da zaku yi.”

Asabe ta ce “Ahaf ai dama na ce ke kika sa shi, amma kin ji kunya wallahi.”

Jummai kuwa na ganin haka ta fashe da kuka, don duk itace silar wannan riki.

Ƙarshe Alhaji Mai Nasar ya jawo Uwani, shi kuma Malam Amadu ya jawo Asabe suka fiddo su waje.

Hajiya Mairo ta dubi Jummai “Tashi ki ɓace mani a gani, shegiya karuwar banza.”

Wannan magana ta daki zuciyar Jummai, tsaida kukan da take ta yi “Kwarai kuwa karuwa ce ni, amma tare da ɗanki muke kawalcin, tunda har ga rabo mun samu,”  tana gama faɗin haka ta yo waje.

Eho Hajiya Mairo ta leƙo tana yi musu, don yau burinta ya gama cika.

Haƙuri Alhaji Mai Nasara ya yi ta basu, tare da tabbatar musu da zai zo har gida akan maganar.

Shirin tafiya suka yi, Alhaji Mai Nasara ya fiddo kuɗi ya basu, suka ƙi karɓa, tilasta musu ya yi, dole suka karɓa tare da godiya.

Zukatansu a dagule suka bi hanyar da zata sada su da tashar mota.

Sun ɗan yi nisa da tafiya kenan suka ji ihun yara a bayansu suna faɗin “Eho wata ta yi cikin shege! Eho wata ta yi abin kunya!”

Ashe Hajiya Mairo ta kira ƙawarta ta faɗa mata, ita kuma ƙawar ta yo zugar yara ta basu kuɗi akan su tozarta su Asabe a idon mutane.

Tamkar Su nitse ƙasa don kunya da takaici, Asabe da ta koma kamar zautacciya ta bi yaran da gudu, aikuwa ta yi sa’ar cafke ɗaya daga cikinsu. Wani irin mari ta yi ta falla mashi, daƙyal Malam Amadu ya ƙwace shi.

“Wai ke me ya sa baki da haƙuri ne,” Malam Amadu ta faɗa cikin ɓacin rai.

Asabe ta ce “Baka ji me suke cewa ba ne.” 

Ya ce “Ai Ɗan kuka ne ke ja ma uwarsa jifa. Duk abin da suka ce ‘yarmu ce ta ja mana, don haka ya zama dole mu toshe kunnuwanmu, don bamu ji komai ba”

Shiru Asabe ta yi, tana jin kamar ta yi ta kurma ihu, hannunta Malam Amadu ya ja “Mu je” Haka suka yi ta tafiya yaran na binsu, Jummai kuwa sai kuka ta ke.

Har sai da suka isa inda mutane suke, sannan wani matsahi ya kora yaran, tare da basu Haƙuri.

Ana azuhur suka isa gida, tun da suka shige gida Malam Amadu bai sake fitowa ba sai Asuba, don haka bai san wainar da ake toyawa a gari ba.

Sai da Asuba ya fito Masallaci da zummar limanci, har ya shiga gaba Maigari ya dakatar da shi, “Yau ba kai zaka yi mana limanci ba.”

Jiki a mace ya dawo baya, wani kuma ya shiga gaba ya ja su sallah. 

Bin sallar kawai yake, amma ko kusa bai iya tantace ruku’u aka yi ko sujuda saboda tashin hankali, abin da kawai yake tambayar kansa shi ne, “Waye ya tona mana asirin da muka daɗe muna rufewa?”

Ana sallame sallah Maigari ya tashi, “Daga yau an tsige Malam Amadu a matsayin limamin gari, an ɗora Na’ibinsa.”

Duka mutanen dake masallacin suka maido hankulansu a kan Malam Amadu dake ta raba idanu kamar bai san me ake cewa ba.

Wasu sun san me ya faru, da yake Hajiya Mairo ta bugo waya ta faɗa ma danginta maganar, su kuma suka fiddo maganar har a wurin Maigari.

Tashi Malam Amadu ya yi ya fito daga Masallacin, waɗanda suke abokan gabarshi suka biyo shi baya suna yada mashi Habaici, “Yau dai ƙaryar Liman ta ƙare, ƴarsa ta ɗebo abin kunya.”

Wani kuma ya ce “Ni fa a kan idona ta shigo gari tana ɗingishi, na san a ranar ne aka ɓare ƙwan” waɗanda ke tare dashi suka bushe da dariya.

Tamkar mashi haka wannan magana ta soki zuciyar Malam Amadu, amma sai ya danne ya cigaba da tafiya, yana shiga gida juwa ta kwashe shi ya zube.

Da gudu Asabe ta fito don a ƙofar ɗakinta ya faɗi, ganin idanunsa a kafe yasa ta kurma ihu tana faɗin “Mun shiga uku, Malam don Allah ka tashi.”

Da hanzari Jummai ta sallame Sallah ta fito itama tana kuka, Ruwa Jumman ta ɗebo Asabe ta yayyafa mashi, aikuwa yana farfaɗowa ya ce “Asabe zuciyata ta gaza da ɗaukar wannan baƙinciki, ina ji a jikina mutuwa zan yi.”

Asabe na wani irin kuka ta ce “Don Allah Malam ka dena faɗin haka.”

Kamashi ta yi da zummar ta tashi, aikuwa ya kasa, saima sake sumar da ya yi.

Aminishi Malam Sambo da tuni ya biyo bayanshi daga Masallaci ya iske wannan Al-amari, cikin hanzari ya samo mota aka nufi Asibitin birni da shi. 

Cikin sa’a kuwa Dr. Ameer Sarkee da wasu likitoci suka karɓe shi, ba ƙaramar kulawa ya samu daga wurin likitocin ba.

Da yamma yana falkawa daga dogon baccin da ya yi, ya tambayi Asabe ina Jummai.

Ta ce “Tana gida” ya ce “Toh a kirata mu gana,” Cike da faɗuwar gaba Asabe ta ce “Toh kai da za’a sallama, don Allah ka dena maganarta ma.”

Matsawa ya yi akan shi dai a kira ta, waya Asabe ta buga ma Jummai cewar gobe su taho ita da su Basheer.

Washe gari wurin ƙarfe shabiyun rana sai gasu, Kuka sosai su Jummai suka yi da suka ga yanayin jikin Mahaifinsu.

Sun daɗe a tare da shi, da zasu tafi ya kira Jummai ita kaɗai, sauran kuma ya ce su jira ta waje.

Nasiha sosai ya riƙa yi mata akan ta yi haƙuri da rayuwa, Sannan ya tabbatar mata da bai riƙe da ita, ya ɗauki wannan a matsayin ƙaddara, fatan da yake mata wannan ya zama kuskure na ƙarshe da ta aikata a rayiwarta.

Da kuka ta fito daga ɗakin, sauran yaran ta tattara suka tafi, kafin su kai gate ɗin Asibitin wata mota ta tsaya gabansu.

Dr. Ameer ne ya fito, wanda Jummai ta daɗe da saninshi tun lokacin da suka zo a fidda mata ciki.

Gaishe shi suka yi, ya amsa tare da tambayarta jikin Babansu, ta ce “Da sauƙi.”

Sake tambayar su inda zasu ya yi, tace “Gida zamu koma,” ya ce “Toh mu je in kaiku tasha.”

Kai Jummai ta girgirza “A’a ka barshi,” murmushi ya yi, ƙasan ranshi yana jin wani irin tausayinta, don ya ga alamar har yanzu tana cikin damuwa, kuma ga tsohon ciki.

Bai matsa musu akan sai sun shiga ba, sai dai ya zaro kuɗi ya ba Basheer “Toh ku sha ruwa a hanya.”

Yana faɗin haka ya juya, kasa magana Jummai ta yi, sai dai Basheer ya ce “Mun gode.”

Murmushi ya yi, idanunsa na kan Jummai da ke ta kallonshi, buɗe motar ya yi ya shiga. Saida ya tafi sannan suma suka tafi.

Isarsu gida ta yi daidai da saukar baƙin labari a garin cewar an bugo waya Malam Amadu ya rasu.

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 8Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×