Skip to content
Part 11 of 16 in the Series Ko Wace Kwarya by Sadik Abubakar

A fusace Hajiya Sabuwa ta ce, “Lallai yarinyar nan ba ki da mutumci, tunda haka kika ce, za ki ga makircinmu. Sai kin yi nadamar faɗa mini wannan maganganun.”

“Ki gafarce baiwar Allah! Ni fa ban faɗa miki wani abu na zafi ba, abubuwan da ya kamata ki sani ne, domin tafiya ba tare da ka san halin abokin tafiyar ba da wahala. Sai a yi ta samun cikas da saɓani, amma yanzu aƙalla kin fara sanin ko ni wace ce? Don haka nan gaba idan kin ji na faɗi wata magana ko na yi wani abin ba za ki yi mamaki ba. Amma idan kalamaina sun yi miki ciwo to ina neman yafiyarki, ban yi don haka ba akasi aka samu.”

Rasa abin cewa ta yi, ta juya laƙwas gwiwa a saluɓe. Wajen Hajiya Lami ta nufa tana hucin harbin iska, “Kin ga garin kwashe-kwashen Alhaji ya je ya kwaso mana ‘yar jaraba, kin ji yadda ta zage ni tas da baƙaƙen maganganu? Gaskiya sai mun tashi tsaye akan wannan yarinyar, sai mun yi kamar muna yi kafin ma ta samu gindin zama. Idan ba haka ba kuwa za mu yi ƙarkon kifi.”

Dariya Hajiya Lami ta yi sannan ta ce, “Ke do Allah ba na son wannan barkwancin naki, yarinyar da wataƙila tun zuwanta gidan nan take faman kuka, shi ne za ki ce ta zage ki. Ko iya haɗa ido da mutane ba ta yi.”

“Cabɗijan! Lallai kam, amma dai kin san idan wasa nake za ki ga alamar dariya a tare da ni, idan ba ki yarda ba zo mu je ki ji da kunnenki.”

Miƙewa ta yi suka sake komawa, daidai lokacin Zaliha ta fito da Ƙur’aninta za ta ɗan taɓa tilawa. “Lafiya dai? Ko akwai abin da kuka manta ba ku faɗa ba ne?” Ta tambaye su bayan ta ɗaga kai ta dube su.

Hajiya Sabuwa ta dubi Hajiya Lami ta ce, “Kin ji abin da na faɗa miki ko?”
Kafin ta yi magana Zaliha ta kalle ta sosai, zuciyarta a dake babu jin fargaba ta ce, “Ba ki yarda da abin da ta faɗa miki ba ne? Saƙona ne zuwa gare ku gabadaya. Kamar yadda kuka amayar mini da abin da yake ranku wanda kuke so na sani, shi ne ni ma na furzar muku da nawa saƙon, kun ga an yi canjaras ke nan (Watau Balancing) a harshen ‘Yan Jarida. Saboda haka idan babu damuwa ku ɗan fita zan yi karatu ne.”

Wani irin mamaki ne ya ɗaure musu kai har suka rasa abin da za su ce, sai kallon juna suke, zuwa can Hajiya Lami ta nisa tare da cewa, “Ke ‘yar nan ki yi ƙasa-ƙasa da muryarki, iyayenki ne a gabanki. Ki bi mu ki zauna lafiya a gidan nan, idan kin ƙi kuma kwaɓarki ta yi ruwa. Yanzu za mu yi sanadiyar yanka miki biza zuwa inda kika fito, kin ga kin ci ribar auren Alhaji, kin zama ƙaramar bazawara.”

Wata ‘yar gajerar dariya mai cusa takaici Zaliha ta yi sannan ta ce, “Iyayena fa kika ce? Anya kuwa kin san ma’anar wannan kalmar ta ‘iyaye’? Da dai kishiyoyina kika ce da na fi yarda da ke, domin a zahiri ma matsayinku ke nan. Amma na yi alƙawarin ba zan taɓa yin kishi da ku ba kasancewar kun ajiye kama ta da wanda suka fi ni, kuma shekarunku kusan na mahaifiyata ne. Abu ɗaya nake son ku yi mini, ku yi sanadin fita ta daga gidan nan!”

“Kin yi da ‘yan halak yariya, indai mu ne za ki ga tsiya tsirararta kuwa.”

Suna faɗa suka juya suka fice, ita kuma ta mayar da ƙofar ta rufe ta zauna ta fara karatunta. Karatu ta yi sosai wanda hakan ya sa ta ji kaso mafi yawa daga cikin damuwarta ya ragu. Ta samu nutsuwa a zuciyarta sosai, abu ɗaya ne dai ya tsaye mata a rai shi ne yaya Abdul, amma duk wani baƙin ciki da ɓacin rai yanzu ba ta jin sa.

Hajiya Lami da Hajiya Sabuwa suka yi turus babu nauyi, ɗan lokaci mai tsayi suka ɗauka ba wacce ta yi magana, zuwa can Hajiya Sabuwa ta ce, “To kin gani dai kuma kin ji da kunnenki. Yanzu mene ne abin yi? Ya kamata mu san matakin da za mu ɗauka tun kafin ya ɗauke ta su tafi Umara. Ba don ayyuka da suka yi masa yawa ba da yanzu ya fara shirin tafiyar.”

Murmushin ƙeta Hajiya Lami ta yi sannan ta ce, “Don Allah ki kwantar da hankalinki, akan wannan ‘yar ƙaramar yarinya duk kin bi kin tashi hankalinki. Wace ce ita? Wace uwarta a garin nan? Me suke da shi? Ina ta sani? Wa ta sani? Kada ki manta fa, boka na kan tsauni yana raye, kuma ya yi mana alƙawarin matuƙar yana numfashi babu wata buƙata da za mu kai masa kokenmu face ya samar mana mafita. Ki bar ni da ita kawai.”

“To ai ni lamarin yarinyar ne har tsoro yake ba ni, zance a cikinta kamar an koya mata. Kuma da alama wannan ko wajen bokan aka je da wahala a yi nasara a kanta, domin na ga alamar mai riƙo da addini ce. Kin ga kuwa irin waɗannan ana shan wahala kafin magani ya huda su, wasu ma sai dai a yi ƙaiƙai koma kan masheƙiya.”

“Ke kam kina da matsala wallahi, ana ba ki kina roƙo. Ita ɗin banza! Wai kin manta wace ce ni? Na buga da ‘yar malamai ma na kai ta ƙasa bare ita, ko kin manta karanbattanmu da Madina ‘yar Maiduguri? Yasin ta riƙa jefo mini, amma dayake bokan kan tsauni ya tsuma ni sai da na ga buzunta. Don haka yadda ta ce tana son barin gidan, to sai ta bar shi koda kuwa da izglanci ta faɗa.”

Ita kuwa Suwaiba ba ta san wainar da ake toyawa ba, da yake sun haɗe mata kai su biyu suke sha’aninsu. Sannan kuma ita ɗin ba mai son hayaniya ba ce, tana can sashenta tana sabgar gabanta.

A ɓangaren yaya Abdul kawo yanzu a iya cewa ya ɗan samu kansa, ya miƙe. Sai dai har yanzu zuciyarsa fal take da ƙaunar Zaliha, yawan tunanin ta ne maƙare a ciki. Abin da ya sa Inna ta ci gaba da ƙoƙarin kauda masa da tunanin ta hanyar dawo masa da batun Aisha, har ta riƙa kiran yarinyar tana zuwa tana yi tare da Jamila, ko a haka Allah zai karkato da hankalinsa kanta. Domin abin da zai rage masa tunanin ko ma ya cire shi daga ransa shi shi ne ya samu wacce zuciyarsa za ta riƙa bege.

Aisha dai kyakkyawar yarinya ce mai nutsuwa ga kunya, fara ce sosai ba ta da jiki, Zaliha ta fita jiki da tsayi. A ɗaya ɓangaren layin su yaya Abdul ɗin take. Duk da wannan kyawawan siffofi nata, sam yaya Abdul ya ƙi sauraren ta, haka takan zo su yini da Jamila. Wani lokacin yakan yi mata magana amma ba ta soyayya ba. Soyayya gamon jini, wannan batu haka yake.
*****

Ranar da Zaliha ta cika kwana goma cif a gidan Alhaji Saminu, suka gana da Suwaiba. Har ɓangaren Zalihar ta tako da sallama, ta amsa masa da sakin fuska. “Amare manya, ko leƙowa ba a yi a ɗan gaisa.” Cikin sanyin murya ta yi maganar.

Murmushi Zaliha ta yi ta sunkuyar da kai ba ta ce komai ba, Suwaiba ta ci gaba da cewa, “Tun washegarin tarewa ba a sake ganin ki ba, ba kya fitowa. Kodayake gidan haka yake bahagon gida ne, gara ma mutum ya yi zamansa shi kaɗai ya fi masa alkairi. Idan ya fito sai a nemi ɓata masa rai da gangan.”

“Ai kam dai haka abin yake, rayuwa sai haƙuri.” Zaliha ta faɗa cikin murmushi a takaice.

Suwaiba ta yi shiru tana ƙare wa Zaliha kallo sannan ta ce, “Ƙanwata zan ɗan ba ki shawarwari duk da cewa na san abin da aka faɗa miki a gida ya wadatar yadda za ki zauna lafiya maigidanki da kuma abokan zamanki. Amma duk da haka game da wannan gidan sai kin kiyaye wasu abubuwa.”

Ta ɗan tsagaita, Zaliha ta baza kunnuwa tana jiran ta ji da me ita kuma ta zo?

Ta nisa ta ce, “Ni ce matar Alhaji ta uku, yaranmu biyu da shi, duk tsawon lokacin da na shafe da shi bai fi sati ɗaya ba ne na yi zaman farinciki ni da shi. Tun daga nan kuwa komai na yi ba birge shi nake ba, ba ya taɓa yaba mini. Kuma duk lokacin da wani abu ya faru ya je kunnuensa to ni ce laifi, koda kuwa ina da gaskiya. Na yi kuka har na gaji na saba. Waɗancan guzumayen matan su ne matsalar gidan nan, sun riga sun ɗaure shi tamajau. Bai isa ya zartar da wani abin ba sai da saninsu, su suke tafiyar da ragamar gidan nan. Yarana ba su da sukuni kamar agololi haka suke a gidan nan. Saboda haka ina son kada ki tanka musu, ki roƙi Allah Ya yi miki tsari daga makircinsu.”

Zaliha ta tattara dukkan yanayin tausayi a fuskarta ta ce, “Allah Sarki! Sannu da zaman Ibada. Gaskiya na tausaya miki sosai, wannan zaman akwai zalinci, amma Ubangiji zai yi sakayya babu shakka! Su ɗin da suke ganin kamar sun gagara, ƙarya suke, su ƙananan alhaki ne su guji ƙarshensu ba zai yi kyau ba. Ni ƙaddara ce da biyayyar mahaifiyata ta kawo ni hannun Alhaji, amma ko kaɗan shi ko dukiyarsa ba sa gabana. Kuma har yau ban ji alamar zaman gidan nan ya kama ni ba. Ina sa ran zan fita ba da jimawa ba. Na yi wa uwata biyayya ne a matsayina na budurwa ta aurar da ni ga zaɓinta, amma idan na fita daga nan zaɓin kaina ne zan bi.”

“SubhanAllah! Ban gane kin kusa fita ba? Saki kike nufi?”

Cikin murmushin takaici ta ce, “Labarina dogo ne, a dunƙule dai mahaifiyata ce ta ruɗu da dukiyar Alhaji har ta raba ni da wanda ya fi kowa sanin darajata. To amma fa a zahiri ne ta raba ni da shi, kullum neman wayarsa nake, shi ne namijin da zan iya rayuwa da shi a duk faɗin duniyar nan.”

“To Allah Ya rufa asiri, gaskiya ke ma na tausaya miki. Wani lokacin iyaye mata suna yin ba daidai ba, ba su cika duba abin da kan je ya dawo ba. Sai kuma abin ya rikice su fi kowa shiga matsala.” Sun jima sosai suna tattaunawa.

To kamar yadda Hajiya Lami da Hajiya Sabuwa suka nuna dogaronsu ga boka, kici-kicin yadda za su bullo wa Zalihar suka shiga. Abin ma har mamaki ya riƙa ba su, yadda ta riƙa zaƙalkala tana nuna ita barin gidan take da muradi. Kodayake Hajiya Sabuwa ce take mamakin hakan, amma ita Hajiya Lami gani take kamar galatsi ne da iyashege, don haka ta sha alwashin za ta bi duk hanyar da za ta bi don ganin ta tsige ta daga gidan.

Bayan kwanaki uku da yin musayar yawun nan ne suka shirya su biyun suka tafi wajen ubangidan nasu, suka kwashe zance suka faɗa masa. ‘Ya yi ‘yan tsibbace-tsibbacensa sannan ya tambaye su, “Me kuke so a yi mata?”
Hajiya Lami ta ce, “Boka da bakinta ta ce tana son barin gidan, ba son sa take ba, shi ne yake son ta. Don haka a saka masa ƙin ta sosai, ya ji ba ya son ganin ta bare ya yi tunanin akwai aure a tsakaninsu.”

Boka ya jinjina kai sannan ya kawo wani garin magani baƙiƙƙirin ya ce, “Wannan a zuba a hanyar da aka san za ta bi ta ƙetara, idan an yi haka zance ya ƙare, a ranar idan ya dawo ba za ta sake kwana a gidan ba.”

Cike da murna suka karɓa, suka ba da ladan bokanci tare da yin godiya suka miƙe. A hanya suke tattauna yadda za su barbaɗa maganin. Shin a ina za su barbaɗa mata?

Hajiya Lami ta dubi Hajiya Sabuwa ta ce, “Ke za ki yi wannan aikin, ni na gama nawa. Sai ki kula sosai kin ji dai abin ya ce, idan aka samu matsala to abin kanki zai juyo, saboda haka ki lura sosai idan za ki zuba kada ki ƙetara.”

Wani nishi mai nauyi ta saki sannan ta ce, “Wallahi har gabana ya faɗi, anya kuwa zan iya?”

“Ban gane za ki iya ba? Wace irin magana ce wannan? Kin ga ni fa duk wannan abin da kika ga ina yi taimaka miki nake, ke sanin kanki ne Alhaji ko babu boka zan sa shi ya yi ko kuma ya bari. Na ga tamu ta zo ɗaya ke ne shi ya sa ma har nake sauraren ki, idan kuma kina son na bar ki da waɗannan yaran to shike nan, kin ga dai wannan ‘yar bana-bakwai ɗin da ya kwaso muku.”

A sanyaye ta ce, “To shike nan babu komai.”

“Yawwa ko ke fa, ai ba a bori da sanyin jiki. Kin ga yau ba a wajenta yake ba, da Magariba za ki lallaɓa ki shiga sashen nata ki barbaɗa mata shi sosai yadda dole sai ta ƙetara muddin za ta fito.”

Haka suka ajiye magana, har suka iso gida hankalin Hajiya Sabuwa bai kwanta da wannan aikin kasassaɓar da za ta yi ba, alatilas ta amsa wa Hajiya Lami don ba ta son yin jayayya da ita.

Bayan Magariba kaɗan Zaliha ta gama ɗan girkinta iya cikinta ta ci, tana zaune tana jiran lokacin sallar Isha ya yi ta sauke farali sannan ta kwanta, sai ta tuna ba ta kulle ƙofar shigowa ɓangaren nata ba. Miƙewa ta yi ta nufo wajen da nufin ta rufe ƙofar, me idanunta za su yi tozali da shi in ba Hajiya Sabuwa ba, tana tafiyar sanɗa hannunta riƙe da baƙar leda tana yaryaɗa magani.

“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!” Zaliha ta faɗa da dukkan ƙarfinta, hakan ya yi matuƙar razana Hajiya Sabuwa, garin neman hanyar gudu ta ƙetara maganin nan ta yi can ciki wajen Zalihar.

Da sauri Zaliha ta riƙa furta addu’ar, “A’uzu bikalimatullahi tammati min sharrin ma kalaƙa! Ta Allah ba taku ba, wallahi ba ku isa ku cutar da ni ba!”
“Don Allah ‘yata ki yi haƙuri ki rufa mini asiri, wallahi sharrin shaiɗan ki yafe mini.”

“Wace ce ‘yarki? Wallahi ni ba ‘yarki ba ce, ke ba uwata ba ce. Kushiyata ce mai shirin cutar da ni.”

Suna tsaka da haka sai ga Alhaji ya shigo, gaban Hajiya Sabuwa ya yanke ya faɗi ta kama rawar jikin razana.
“Tunda sauran girmanka da ƙimarka a idona ka sawwaƙe mini zama da kai, wallahi ban dace da zaman gidan nan ba. Indai ba cutar da ni kake so ka yi ba, to ka yi haƙuri kafin matanka su haukata ni ko su hallaka ni.” Zaliha ce ta yi wannan maganar cikin rarraunar murya.

“Wai mene ne yake faruwa?”
“Ita za ka tambaya, ga shi nan kana gani magani take zuba a ƙofa.”

A fusace ya juyo kan Hajiya Sabuwa kafin ya yi magana ta fara faɗin, “Alhaji don Allah ka yi haƙuri wallahi ba laifina ba ne, laifin Hajiya Lami ne ita ce ta sani.”

“Yi mini shiru munafukar banza! Kamar ke za ki ce wata ta saki ki aikata mugum abu. Ina take ita Lamin?” Daga nan ɗin ya ƙwalla mata kira da ƙarfi har sau biyu.

Ashe tunda ta ji shiru Hajiya sabuwa ba ta dawo kawo mata rahoto ba, ta yi tunanin kodai ba ta je ba ne? Don haka sai ta fito daidai lokacin ne ta hangi Alhajin ya shiga wajen Zalihar.

Laɓewa ta yi, saboda haka ta ji duk abin da ya faru kuma ta ji kiran da ya yi mata.

Komawa baya ta yi kaɗan, shi kuma ya sake ƙwalla mata wani kiran da ya fi na farko ƙara. Sai ta amsa sannan ta ƙarasa da faɗin, “Alhaji lafiya kuwa kake ta kwaɗa uban kira haka? Maganar take ba tare da ta yarda sun haɗa ido da Hajiya Sabuwa ba, Alhaji huci yake tamkar wani bijimin sa, yana fesar da wata zazzafar iska ya ce, “Wannan makirar ce take shirya wa wannan ‘yar baiwar Allahn wani mugun abin, Allah Ya toni asirinta. Amma bari ki ji daga bakinta.”

Ya juya ya dube ta ya ce, “Wa kika ce ta sa ki?”

Cikin kukan nadama ta dubi Hajiya Lami ta ce, “Ba ke ba ce tun washegarin kwananta na bakwai kika ce sai mun tashi tsaye a kanta, shi ne muka je wajen boka muka karɓo wannan maganin kuma kika ce ni zan zo na zuba mata.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ko Wace Ƙwarya 10Ko Wace Ƙwarya 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×