Skip to content
Part 13 of 16 in the Series Ko Wace Kwarya by Sadik Abubakar

Cikin sigar mamaki ta ce, “Yaya kin ga halin da take ciki kuwa? Yanzun nan fa daga wajenta nata nake, yarinya ta rame ta lalace ta firgice duk ta sauya kamar ba ita ba, ana aure a samu kwanciyar hankali, yaro ya murje ya gyagije amma ita sai dai akasin haka. To ina amfanin auren ke nan? Kuma na tambaye ta sarai ta ce ita ba ta son sa ko kaɗan biyayya ta yi akan tilastawar da kika yi mata. To idan so kike sai an kawo miki ita a gadon asibiti ciwon zuciya ya kama ta ko kuma an haukata ta sannan za ki yarda, to mu ba za mu bari a kai ga hakan ba. Na zo ne na sanar da ke zan yi duk abin da ya dace domin na saka farinciki a ranta.”

“To wai banda abin ki, ke ma kina neman zama marar tunani. Ina kika taɓa ganin gidan da ba mace ɗaya ba an zauna lafiya? Ai da ma abin da ake tsammani ke nan, shirin da nake yi wajen jibi zan je na karɓar mata ɗan taimako da maganin miyagu na kai mata.”

Wani irin kallo mai cike da tuhuma Anty Maryam ta yi mata, da ta fuskanci ba za ta fahimce ta ba sai ta ce, “Shike nan yaya sai anjima ni zan koma!”

“Ki dakata ba abin fishi ba ne, ya kamata ki fahimci yaran zamanin nan idan aka riƙa biye musu da zaɓin nasu cutar da kansu za su yi, su cutar da wani ma.”

Anty Maryam ba ta sake tanka mata ba, a ranta kawai ta ce, “Ai ke yanzu ga shi nan a matsayinki na uwar zamani kina cutar da ‘yarki saboda kuɗi, kin zaɓi abin duniya sama da farincikinta. Ta Zama Haja! Ta jikinta za ki samu dukiya, to ba ki isa ba wallahi. Yarinya sai ta shaƙi iskar ‘yanci kamar kowacce ‘ya, mu zuba ni da ke!”

Nan ta fice ranta a ɓace sosai, tana tafe tana tunanin yadda za ta tinkari lamarin. Yini biyu ta kwashe tana saƙe-saƙen hanyar da za ta bi, daga ƙarshe ta yanke cewa za ta sake komawa ta tattauna da Abba. Shi dayake namiji ne zai fahimce ta sannan kuma abin zai fi kyau a ce maza ne za su magantu a kai.

Bayan kwanaki uku da zuwan anty Maryam gidan Zalihar, ta sake shiryawa ta koma kamar yadda ta alƙawarta mata. Ita ma ɗin ta fi son rabuwar, to sai dai abin da wahala. Daga yin aure ba a ci Talata bare Laraba a ce an rabu, abin babu daɗi wai mahaukaci ya ci kashi.

Da yake zuwan hantsi ta yi iske ta ta yi tana aikace-aikacen gida, ga gida har gida, komai ga shi nan a wadace washasha amma babu kwanciyar hankali. Cike da farinciki Zaliha ta ɗauki Ilham tana cewa, “Anty ba don makaranta ba ai bar mini ita za ki yi a nan.”

Cikin murmushi ta ce, “Ai kam dai da sai ku yi zamanku, da ma kullum cikin tambayar ki take.”

Nan da nan Zaliha ta hau kici-kicin yi musu girki, ta ɗora ta komo falo suka fara hira. Suna cikin hirar sai wayar Zaliha ta shiga ruri, dubawar da za ta yi ta ga sunan Umma na harbawa, ta dubi Anty Maryam ta ce, “Umma ce.”

Sannan ta ɗaga kiran da sallama, bayan ta amsa mata ta ce, “Kin gan ni nan a ƙofar gidan naku.”

Mamaki ne ya kama ta ta ce, “To sannu da zuwa bari na fito.” Ta faɗa tare da sauke wayar ta sake duban Anty Maryam ta ce, “Kin ji wai Umma ce ta zo tana waje.”

“Je ki shigo da ita to.” Anty Maryam ta faɗa ba tare da wani armashi ba.
Cikin rashin karsashi ta fito babbar kofar gidan, ta shiga da shiga mahaifiyar tata.

“Ikon Allah! Ashe ku ma kuna nan ke nan?” Umma ta faɗa bayan sun haɗa ido da Anty Maryam.

“Ai kam dai kin gan mu! Sannu da zuwa, ina kwana?” Suka gaisa. Zaliha ma ta gaishe ta cikin girmamawa. Jim suka yi babu wanda ya sake magana, ba don ba su da abin faɗar ba. Kowa na son wani ya buɗe babin tattaunawar. Zaliha ta miƙe ta nufi kicin ta zubo abinci ta kawo ta aje sannan ta sake komawa ta kawo kayan ruwa da lemuka.

Umma ta ɗan muskuta ta fito da wani ƙullin magani ta dubi Anty Maryam ta ce, “Kin ga hayaƙin da na ce miki zan karɓo mata ta riƙa turarawa, babu abin da zai same ta sai alkairi.”

Murmushin takaici ta yi tare da cewa, “Gaskiya yaya abin naki sai an haɗa da roƙon Allah, yanzu a yanayin da kika iske yarinyar nan ba ki ji tausayin ta ya kama ki ba? Har kike mata sha’awar cigaba da zaman ƙaddarar nan, wai yaya ko sai kin ga gawarta sannan za ki yarda tana cikin damuwa? Ba don yarinyar mai biyayya ba ce ai da tuni ta yi duk abin da za ta yi ta kuɓutar da kanta, tsantsar biyayya ce kawai take zaune da ita. Zaliha tana cikin damuwa, ki fahimce ta, ki yi haƙuri ki ba ta dama. Wannan mutumin ba sa’an aurenta ba ne, sannan waɗannan guzumayen ko ni sun fi ƙarfin na iya kishi da su, azzalumai ne marasa tsoron Allah.”

Umma ta yi murmushi ta ce, “To ai ni duk yadda kike zuzuta abin ban ga ya kai haka ba. Idan kina batun rama ne, tun tana gida ta rame. Ta ƙi cin abincin arziki sai tunani ta ajiye a ranta, to kin ga kuwa ai babu laifin aure a nan. Ta cire tunani daga ranta ki ga idan jikinta bai dawo ba.”

“Yaya ke nan! Ba musu ko jayayya zan yi da ke ba, amma kafin zuwan wannan mutumin cikin rayuwarta ai ba haka take ba. Shi ne ya rikita mata lissafi, domin jininsu bai haɗu ba, koda ma kishiyoyin na gari ne, to shi kansa maigidan ba ta son sa, ba ya ranta don haka zaman zai yi wahala a samu yadda ake so. Kina ji dai kullum a kafafen yaɗa labarai yadda auren dole ke jefa yara cikin tasku, wasu har hallaka kansu suke yi, wasu kuma su hallaka mazajen. To mu Alhamdulillah! Tamu ba irin su ba ce, ta yi haƙuri kin lanƙwasa yadda kike so. Allah Ya nuna mana haɗarin da zamanta a gidan zai fuskanta, to don me za mu kyale ta? Ba za mu fahimci damuwarta ba? Ban yi niyyar sake tattauna wannan maganar da ke ba, don dai mun haɗu a nan ne. In Sha Allahu yau nake shirin komawa na samu Abbanta na yi masa bayanin halin da take ciki, domin na tabbata bai san wainar da ake toyawa ba. Matuƙar kuwa ya ji to babu shakka ba zai bar ‘yarsa cikin ƙunci ba, farincikinta shi ne abu na farko a wajensa, saɓanin ke da kika mayar da ita HAJARKI.”

“To na ji duk abin da ke ranki, yanzu me kike so a yi ke nan? Kina nufin raba auren za a yi?

“Ba abin da nake nufi ba ke nan, amma kuma idan hakan ma ta kama me zai hana, domin ni gaskiya ba zan iya barin yarinyata ta ci gaba da ƙunsar baƙin ciki ba, tun da kuruciyarta ciwon zuciya ya kama ta. Abin da nake so shi ne, a tsaya a tambaye ta haƙiƙanin gaskiya idan tana son sa shike nan sai a kafa masa sharuɗan da matansa ba za su gan ta ba bare ma su yi yunƙurin cutar da ita. Idan kuma ba ta son sa to babu tilas fa, sai ya haƙura. Ita kuma a ba ta dama ta zaɓi wanda za ta zauna da shi, wannan shi ne abin da ya zai haifar da abin da ake buƙata, saɓanin haka kuwa babu abin da zai haifar sai ɗimbin nadama, Allah Ya kiyashe mu.”

Sun jima suna ta musayar yawu ba tare da ɗaya ya fahimci manufar ɗaya ba, daga ƙarshe Umma ta ce, “Za a duba amma dai ba maganar rabuwa.” Ita ta fara tafiya ta bar Anty Maryam a nan.

Sai da ta sake mantar da Zaliha duk wata damuwa sannan ita ma ta tafi. To wannan ke nan!
*****
Kimanin kwanaki biyar ba a ga maciji tsakanin Hajiya Sabuwa da Hajiya Lami, ta san ba ta kyauta, to amma babu yadda za ta yi idan ba hakan ba. Ta ƙyale ta ne ta ɗan huce ɓacin ran, domin idan ta matsa da yi mata magana a lokacin, to abin yana iya muni. Saboda haka tana jin wataƙila yanzu da sakko.

Har sashenta ta iske ta, sallama ta yi mata amma ba ta amsa ba. Harara ta bi ta ita tare da faɗin, “Me kuma kika biyo ni ki yi mini sakaina sarkin iya ruwa? Ki fitar mini daga waje!”

Dariya Hajiya Lami ta yi sannan ta ce, “Mayar da makaman Hajjaju! Komai ya wuce ai.”

“A ina ya wuce? Ai idan maye ya ci ya manta, uwar ɗa ba za ta taɓa mantawa ba. Wallahi ban taɓa sanin ke macuciya ba ce sai yanzu, da ma sakarcina ne ya sa har na amince da ke.”

Hajiya Lami ta yi dariya tare da cewa, “Do Allah ki bar wannan magana, komai ya wuce. Ɗan tsautsayi ne fa ya gifta, kuma na ga kuskurenki da har kika bari aka kama ki dumu-dumu da maganin a hannu. Ai da sauri za ki yi ki naɗe shi cikin zanenki sai ki basar kawai.”

“Da ma ai dole ki ce haka mana, tun farko hakan kike buƙatar ta faru domin na nuna miki ba zan iya ba amma kika kafe. To hankalinki ya kwanta an sake ni sai ki zuba ruwa a kasa ki sha.”

Shiru Hajiya Lami ta yi ta ƙyale ta ta gama fesar da abin da ke bakinta, sai da ta yi shiru don kanta sannan ta ce, “Na ji duk abin da kika ce kuma na yarda na yi kuskure, amma ki yi haƙuri. Yanzu ya ake ciki?”

Hajiya Sabuwa ta taɓe baki cikin sigar rashin yarda ta ce, “Wa? Ki rufa mini asiri. Idan kika gan ni a maƙabarta maza suka kai ni. Haihuwa ɗaya horon gaba. Kin yi da wata amma ba ni ba, ba zan sake amincewa da ke ba. Kowa ya je ya ji da abin da ke gabansa.”

Hajiya Lami ta sake yin dariya ta ce, “Haba do Allah! Kada ki ba da mata mana! Daga ihu ɗaya sai murya ta dashe, ai yaƙin ko farawa ba a yi ba. Ki manta da wancan abin tsautsayi ne kamar yadda na faɗa, yanzu kwatakwata salo ma za mu sauya. Ina jin idan kin lura kwana biyun nan sai kawo mata ƙafa ake yi, ba mu san wace tsiyar ake ƙullowa ana shigo mana da ita ba. Don haka ki manta da komai, abokin cin mushe ba a ɓoye masa wuƙa. Mu sake yin shiri mu tinkare ta, idan kika lura tun daga yadda take fiƙala da zaƙalkala na san da abin da ta taka, uwarta gwana ce wajen bin ‘yan tsibbu.”

“Allah ni fa ba ruwana da wannan harkar, ki je ki yi ke kaɗai. Allah Ya ba da sa’a.”

“Do Allah ki bar wannan wasan haka, ke daɗina da ke idan aka zo da maganar arziki ba kya ɗauka sai an kai ruwa rana da ke.”

“Ai shi ya sa ma don kada a kai ruwan na ce ba zan yi ba, ke dai da kika ga za ki iya hana Allah ikonSa to bisimillah!”

“Hmm! Ya kamata dai ki yi tunani kada ƙankanen ɓacin rai ya sa ki haifar wa kanki babba.”

A hankali sai da Hajiya Lami ta ga ta sake rinjayarta, suka ajiye magana akan za su sake komawa wajen bokan, amma ba za su yarda da duk wani magani da zai ba su ba ya ce a zuba wa Zaliha ta taka ko ta ci ba. Idan har zai taimake su to ya yi musu abin da zai saka tsantsar ƙiyayyarta a zuciyar Alhajin har ya kai ga ya sake ta.

Haka dai suka sake shiryawa a tsakaninsu tamkar ba su taɓa samun saɓani ba.

Sai dai a hunnu guda Hajiya Sabuwa ta ƙudurce sai ta rama, ba za ta bar wancan abin ya bi shanun sarki ba, za ta ɗauki fansa koda kuwa za ta sake kwaɓewa.
*****
Wani sabon ƙalubalen kuma da ya kunno wa Zaliha kai shi ne batun Anas, da gaske son ta yake yi. Bai yi la’akari da matsayinta na matar ubansa ba, hasalima shi murna yake da abin, sai ya ci karensa babu babbaka. Fatansa ɗaya dai Allah Ya sa ita ma irin sa ce mai gurɓatacciyar zuciyar da za ta ba shi haɗin kai su aikata lalata. Tunda dai uban nasa ya tsufa ba zai iya tafiyar da yarinya ɗanya sharaf irin ta ba. A bahagon tunaninsa idan har ta waye, to za ta ba da kai bori ya hau da wuri ba tare da an kai ruwa rana ba.

Bari ya yi sai da Alhajin nasu ba ya gari, sai ya tattara dukkan wata dabara tasa ya tinkari sashen Zalihar, da yammaci ne kuwa misalin ƙarfe biyar. Sai da ya faki idon mutane ya ga babu wanda ya ganshi sai ya yi wuf ya shige.

Tana zaune a falo ta ɗan yi kwalliyarta gwanin sha’awa, kamshi ne kawai ke tashi. Kamar wani mutumin kirki ya shiga da yin sallama.


LCike da mamaki ta amsa tare yin tunanin, ‘shi me kuma ya shigo da wannan?’

Murmushi ya fara yi sannan ya ce, “Amaryar Alhajinmu, mun zo ne mu kwashi gaisuwa, tunda kika zo kusan sati biyu ke nan ba mu gan ki ba.” Yana faɗa ya nemi waje ya zauna bisa kujera da ke daura da ita, ya ci gaba da kallon ta zuciyarsa na kawo masa abubuwa iri-iri, sai murmushi yake ta saki.

Kallo ɗaya ta yi masa ta kauda kanta ba ta sake tanka masa ba.

“Sunana Anas, ni ne babba a gidan nan a sahun ‘ya’ya. Ba lallai ba ne ku yi zaman lafiya da Hajiyata, amma ina son na zame miki garkuwa ta ɓangaren abin da za ta yi miki, ina nufin ni da ke mu zama abokai.”

Da sauri ta ɗago kai ta watsa masa wani kallo mai cike da tuhuma.

Dariya ya yi ya ci gaba da fadin, “E, haka nake nufi. Alhaji zai ba ki duk wata kulawa ta kuɗi, amma ki sani ba shi da kulawar soyayya. Lokacinsa ya wuce ya tashi daga aiki. Idan babu damuwa ni zan ba ki ita kulawar soyayyar.”

A’uzubillahi Minasshaiɗnir Rajim! Ina neman tsarin Allah da kai! Ni ba fasiƙa ba ce, mahaifinka ma bai mini ba bare kai. Ka tashi ka fita kafin na kira mahaifiyarka.”

“Haba ‘yammata! Ki fahimce ni, tausayawa ce ta sa na shigo cikin lamarinki. Tun lokacin da aka kawo ki a matsayin matar Alhaji, na ji tausayinki ya kama ni domin an zalunce ki haɗa ki aure da wannan tsohon, tasa ta ƙare, babu abin da zai iya miki face ya jagwalgwala ki kawai. A wannan shekarun naki kina buƙatar ɗanyen jini iri na, wanda zai riƙa raka ki kiwo.”

Cikin tsiwa ta ce, “Na ce ka fita ko?”
“To, zan fita. Amma hakan ba yana nufin na haƙura ba, zan ba ki lokaci ki yi tunani. Wataƙila yanzu ranki a ɓace yake, sai anjima.” Yana faɗa ya miƙe kai tsaye ya fito ba tare da ya yi tunanin ko wani zai iya ganin sa ba.

Ai kuwa kamar a idanun Hajiya Sabuwa, suka haɗa ido, ya ringina kai ya ce, “To sa’idawa, ana zuwa kuna ƙirgawa, saura na ji wata maganar kuma kin san halina sarai.”

Cikin dabarar yaudara murya ƙasa-ƙasa ta yafice shi tare da cewa, “Yaka zo mana!”

Yana ciccijewa haɗe da shan kunu ya matsa kusa da ita ya ce, “Ga ni ya aka yi ne?”

“Ka ga kwantar da hankalinka, ni ba wanda zan faɗawa, so nake ma mu yi wata magana da kai yanzu.”

“Wace magana za mu yi da ke kuma?”
“Mu je can ɓangarena mana.”

“Kawai ki faɗa mini a nan wuce inda za ni.”

“Haba kai ko daɗina da kai ke nan! Tunda na ce maka mu je can ɗin mu je mana.”

Haka ta yaudare shi suka shige sashen nata, ya zauna kan kujera ya ce, “Ki faɗa mini ina jin ki sauri nake.”

Cikin salon bugun ciki ta ce, “Wane ƙorafi wannan yarinyar ta yi maka? Tunda aka kawo ta take kuka, wai ita ba ta son auren Alhaji.”

“Kin ga ni ba wannan ta yi mini ba, ba ma ita ce ta kira ni ba, ni na shiga don na gan ta, na lura ba ta fitowa ne.”

“Allah Sarki! Ka kyauta kuwa, yarinyar abin a tausaya mata ce. Ta yi mini ƙorafin ba ta son Alhaji, tana da saurayinta matashi kamar ka. Iyayenta ne suka tilasta mata auren Alhaji, da ma za ka taimaka ka riƙa shiga lokaci zuwa lokaci kana yi mata kalaman kwantar da hankali, sai ta rage damuwa.”

Wawan naku da jin haka sai ya washe baki ya ce, “Ai da ma abin da nake mata ke nan, Alhaji ba shi da lokacin yin waɗannan kalamai, ni zan cike mata wannan giɓin. Sai dai na ga kamar ba za ta amince ba.”

Ta sake zungurar sa da cewa, “Kamar ya ya fa? Ai dole ta so, ina jin dai ko tsoron ka take ji. Da sakin fuska za ka riƙa je mata, kuna ‘yan wasannin tsokana da haka za ta saba.”

“To shike nan zan ci gaba da da yi.”
“Yawwa ɗan gari, amma fa ka kula sosai ba koyaushe ba, idan za ka shiga kada bari wani ya gan ka.”

“Ba damuwa.” Ya faɗa tare da miƙewa ya fice, yana jin daɗin ƙwarin gwiwar da ya samu a wajen Hajiya Sabuwa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ko Wace Ƙwarya 12Ko Wace Ƙwarya 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×