Skip to content
Part 16 of 16 in the Series Ko Wace Kwarya by Sadik Abubakar

Misalin ƙarfe huɗu na yammaci (4:00pm) ya gama shirinsa cikin wata dakakkiyar shadda fara fat! Mai tsananin sheƙi da ɗaukar ido, ya sa takalman sandal farare da tsadadden agogo, sannan ya bi da hula ƙirar Zeeta, ruwan hanta. Ya fesa turare mai daɗin ƙamshi. Ya yi wa Inna sallama ya fice. Addu’a ta yi masa tare da fatan nasara.

Tafe yake bisa mashin ɗinsa cikin walwala, babu wata damuwa a ransa. Kafin ya isa ya ratsa ta wani kantin sayar da kayan ciye-ciye dangin alawoyi da cincin ya haɗa wa Ilham ƙwalam da maƙulashe tuli guda sannan ya ƙarasa. Wayar Anty Maryam ɗin ya kira ya sanar da ita cewa yana iso.

Ba jimawa ta leƙo ta ce ya shigo da mashin ɗinsa, shigar ya yi suka ƙarasa cikin falon. Kunya ta lulluɓe shi gabaɗaya, ya zube ƙasa ya gaishe ta cikin tsantsar biyayya da risinawa.
Bayan sun gama gaisuwar, Anty Maryam ta ce, “Zaliha, kawo ruwa.”

Mamaki ne ya kama shi, har ya ɗan tafi gajeren tunanin, “Me ke faruwa ne? Shin ita ma kiran ta ta yi nan don mu haɗu ko kuwa?”

Cikin ƙasa da minti ɗaya sai ga Zalihar nan sanye da wani zumbulelen hijabi ɗauke da faranti da kwanukan abinci, kanta sunkuye ta ajiye gabansa. Ta juya ta sake dawowa da wani farantin cike da kayan ruwa shi ma ta dire a gabansa. Ta koma ɗaki.

Anty Maryam ta ce, “Ga abinci nan ka fara da shi tukunna.”

Ta faɗa, ta miƙe da nufin ta ba shi wajen ya samu sukuni. Kafin ta kai ga miƙewar ya ce, “A wallahi a ƙoshe nake fa!”

“Ban gane a ƙoshe kake ba? Nan dai ba wajen da za a yi jayayya da kai ba ne. Ilham zo mu tafi ƙyale shi ya ci abinci tukunna.”

Haka nan ya ɗan taɓa abincin don kada a ce bai ci ba. Bayan ya gama, Anty Maryam ta dawo ta zauna kan kujera ta fuskance shi sosai sannan ta ce, “Ba wata doguwar magana ba ce, duk abubuwan da suka faru, sun riga sun faru sai dai a kiyayi gaba. Abin da zan faɗa maka ka riga ka san shi, kawai tunasar da kai zan yi. Komai dai da ka gani a sararin duniyar nan, linzaminsa yana riƙe a hannun Ubangiji; babu wani abu da zai faru face Allah ne Ya tsara faruwarsa. Bawa ba shi da wani iko na tsarawar bare wargazawa. Amma hakan ba ya nufin cewa ba a yin kuskure, babu shakka an yi muku laifi; an ɓata muku matuƙa. To a zahirin gaskiya wasu abubuwan ban san sun faru ba sai bayan da komai ya dagule. Saboda haka yanzu a dunƙule dai ina ba ka haƙuri bisa duk wani abu da ya faru a baya; ina son ka manta da komai. Na je can gida mun tattauna da Inna, ta ce za ta sanar da kai, kuma ta ba ni tabbacin ita a ɓangarenta babu komai ta yafe. To kai ma ina son ka yafe ɗin, kai aka yi wa ba daidai ba; ka yi haƙuri. Babu shakka idan alhaki ne, to tabbas hakkinka ya kama mu, ina fatan kamar yadda Inna ta ce komai ya wuce, kai ma ɗin ya wuce a zuciyarka.”

Cikin matsakaiciyar murya mai nutsuwa ya ce, “Babu komai waLlahi, kuma duk abin da ya faru ba laifinku ba ne, kamar yadda kika faɗa a farko komai tsarin Allah ne. Shi ya nufaci faruwar hakan; don haka babu yadda za a yi dole sai abin ya faru. Na gode sosai Allah Ya saka da alkairi Allah Ya ƙara girma.”

“Yawwa! Allah Ya yi maka albarka, Allah Ya jikan Malam. Yanzu a nan wajena take zaune, sai ta gama iddarta tukunna.”

“To babu damuwa Anty, Allah Ya taimaka, Ya ƙara rufa mana asiri. Ni zan koma.”

“To madalla, ka gai da gida, Allah Ya yi albarka.”

Ya miƙe ya zaro sabbin ‘yan hamsin-hamsin ya miƙa wa Ilham tare da cewa, “Ga kuɗin makaranta ko, sai a riƙa yin karatu sosai banda wasa da yawa.”

“Oh! Har da kuɗi haka? Banda waccan ɗawainiyar da ka yi kuma? To an gode.”

Zuciyarsa tas ya fito, yana tafe yana fatan Allah Ya sa ƙarshen wahalar tasu ke nan. Yana kuma ji a jikinsa tabbas abin zai tabbata, kasancewar shigowar Anty Maryam ɗin cikin lamarin. Sai da dare yake sanar da Inna abin da suka tattauna. Kodayake tun kafin ma ya je ɗin Inna ta labarta masa buƙatarsu kuma ta nuna masa ita ba za ta hana shi ba.

Amma duk da haka sai ya ce mata, “Na ji ƙudurinsu, sai dai ina son zan yi Istihara kafin na yanke hukunci.”

Ce masa ta yi, “Yawwa ka ko kyauta, da ma abin da ake son bawa ya lazimta ke nan a duk lokacin da wani al’amari makamancin wannan ya taso.”

Haka nan ita ma Innar ta ci gaba da fatan alkairi da roƙon Allah Ya tabbatar da alkairi. To wannan ke nan!


A cikin kwanakin iddar Zaliha sakamakon jarabawarsu ya fito, kuma Alhamdu Lillah, an samu abin da ake so. Ƙawayenta sun rubuta jarabawar shiga jami’a, amma ita ba ta samu damar rubutawa ba, kodayake tuni ma ta yanke ƙauna daga ƙaratu.

Kasancewar ta fafa gidan da ta gaza samun kwanciyar hankali bare har ma ta fahimci karatun ma.

To sai dai yanzu abubuwa za su sauya, tana jin burinta na yin karatun zai tabbata. Domin a yadda yaya Abdul ɗin ya tsara, bayan ta kammala sakandire za su yi aure, daga nan kuma sai ta ɗora da karatun har sai sun ga abin da ya ture wa Buzu naɗi.

BAYAN WATANNI UKU
Kawo yanzu dai Zaliha ta kammala iddarta, ta samu cikakken ‘yanci. Ta ɗan ƙara girma, ta kuma mayar da jikinta, hankalinta kwance yake.

Sannan kuma Anty Maryam ta ce ba za ta koma gida ba, a nan za ta ci gaba da zama har lokacin da aurenta zai tabbata da yaya Abdul.

A ranar da zai fara kai mata ziyara a karon farko bayan fitarta daga idda, dukkansu sun yi shiri da kwalliya ta musamman, kusan ba su taɓa caɓa ado irin wannan ba. Misalin ƙarfe 4:30pm na yammcin Juma’a ya isa gidan, har ƙasa ya zube ya fara gai da Anty Maryam sannan ya zauna bisa kujera, Ilham ta faɗa kansa da murna, ya rungume ta. Tsakar gida Anty Maryam ta fito ta ba su iska su ɗan sarara.

Ya kalli Zaliha kanta sunkuye, shigar da ta yi ta birge shi matuƙa gaya.

Atamfa ɗinkin doguwar riga ce wacce ta haɗu da ƙwararren tela, ga wani ƙunshi jan lalle da aka yi mata a ƙafa a hannu kuma baƙi. Sai ta zama tamkar amarya, bai taɓa ganin ta cikin shigar da ta ƙayatar da shi ba irin wannan.
“Amaryar Alhaji!” Ya faɗa cikin sigar tsokana.

Ta ɗago kai fuska a shagwaɓe ta ce, “Allah ba na so!”

Dariya marar sauti ya yi sannan ya ce, “Gaskiya gidan Alhaji ya karɓe ki, ai ni ban gane ki ba sai da kika ɗago kai.”

Ta sake taɓe baki kamar za ta yi kuka ta ce, “Yaya Abdul ka daina tausayi na ko! Shi yasa kake ambaton abin da na fi tsana a rayuwata!”

Ganin yadda yanayin nata ya sauya, lallai ba ta son a tuna mata wancan baƙar rayuwar da ta baro, sai ya kyautata murmushinsa ya ce, “Afuwan Umman Khalil! Yayanki ba zai taɓa daina tausaya miki ba.”

Sunan da ya ambace ta da shi ya yi matuƙar daɗaɗa mata rai, dariya ta yi ta ce, “Nan kuma ka koma ko?”

Hira suka sha mai tsayi, duk wani ɓacin rai da damuwarsu sun kauce. A gidan ya yi sallar Magariba da Isha. Da zai tafi kamar kada su rabu, kowa na tsananin kewar ɗan uwansa.

To haka dai wannan soyayya ta sake dawowa ɗanya sharaf sannu a hankali maganar aure ta tsayu sosai har aka yi baiko. Watanni bakwai aka sanya bikin.

Kwanci tashi ba wahala a wajen Mai jujjuya dare da rana, komai aka ƙayyadewa lokaci to tamkar ya zo ne. Kawo yanzu saura wata guda bikin Zaliha da yaya Abdul, shirye-shirye sun kankama.

Ya gama haɗa wadataccen lefen da aka jima ba a ga irin sa ba, duk wanda ya zo ganin kayan sai ya yaba da fatan alkairi. Ko mahassadi ya ga abin da aka haɗa wa Zaliha sai ya yaba koda a cikin ransa ne.

Satin biki ya zo aka fara shagali da kamun amarya, wanda guda ne cikin al’adar bikin auren Malam Bahaushe. Bayan kamu sai daurin aure ya biyo baya, wanda aka yi a ranar Juma’a a babban Masallacin Juma’a na Sheikh Isyaka Rabi’u da ke unguwar Gwauron Dutse.

Yinin biki na mata shi ya biyo baya, wanda ya haɗa dukkan dangi da abokan arziki na kusa da na nesa. Aka yi shagali cikin kwanciyar hankali da farinciki da aminci. Luguden nasihohi da jan kunne haɗi da nuni, suka tumfaye kunnuwa da ƙwaƙwalwar amarya.

Wata tsohuwa wacce ta kasance mafi tsufa yayar Inna ce, ita ce ta rufe nasihar da cewa, “Ki sani yanzu za ki shiga wata sabuwar rayuwa, abin da kike so ba shi za ki samu ba. Sinadarin yin wannan rayuwa shi ne haƙuri. Yi na yi; bari na bari, waɗannan su ne sirrin zaman aure idan kika riƙe to za ki zama matarsa har ranar gobe kiyama. Allah Ya yi miki albarka.”

Kai tsaye aka ɗauke ta zuwa ɗan matsakaicin gidanta wanda ya kasance mallakin yaya Abdul ne. Babu wanda bai yi sha’awar gidan nan ba, yanayin yadda tsarin gidan yake da kayan da aka shirya a ciki su suka fi ƙayatar da jama’a.

Kwatankwacin irin nasihar da aka yi wa ango ke nan, aka nuna masa cewa, yanzu ya girma, ga wani gagarumin nauyi nan ya dira a kansa, haƙuri da kauda kai su za su rage masa jin nauyin.

Haka dai aka bar amarya da angonta suka fara sabuwar rayuwarsu cikin so da kƙauna. Ɗimbin nasarori kuma suka riƙa biyo baya.

Da ma dai haka abin yake, Hausawa na cewa, ‘Bayan duhu sai haske.’ ‘Bayan wuya sai daɗi.’ Wannan magana kuwa ta yi daidai da ayar nan ta cikin Kur’ani Mai tsarki inda Allah Ya ce, “Haƙiƙa dukkan tsanani yana tare da sauki.”

Alhamdu Lillah! Duk nisan gona akwai kunyar ƙarshe. A nan na kawo ƙarshen wannan ɗan littafi nawa mai suna KO WACE ƘWARYA… Ina roƙon Ubangiji Ya karɓi wannan aiki Ya ɗora mini a mizanin awon kyawawan ayyuka, amin summa amin.

Wassallama Alaikum!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ko Wace Ƙwarya 15

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×