Skip to content
Part 4 of 16 in the Series Ko Wace Kwarya by Sadik Abubakar

Siririn murmushi ta yi tare da sakar masa wani kallo mai jefa zuciya cikin saƙe-saƙe kala-kala. Cikin lallausar murya ta ce, “Abban Khakil!”
“Waye Abban Khakil kuma, me ya faru da shi?”

Cikin ɗariya mai ɗauke da nishaɗi haɗi da walwala ta ce, “Wani kyakkyawan saurayi ne da aka jima ba a yi kamar sa ba a tarihin duniya, sai wata ‘yar almajirar yarinya ta yi sa’ar zama sarauniyar birnin zuciyarsa. Shi ne take fatan idan sun tsinci kansu a duniyar ma’aurata, Ubangiji Ya ba su da namiji, ya raɗa masa suna Khakil, sai ta riƙa kiran sa Abban Khakil.”

Kallon ta kawai yake yana sakin murmushi cike da mamakin kalaman da take furtawa, da ta ɗan tsagaita sai ya nisa ya ce, “Kai Ma Sha Allah! Amma sun birge ni matuƙa, musamman ma ita yarinyar da ta kasance mai ƙanƙan da kai. Hala ba a wannan zamanin suke ba ko?”
Ta sake aika masa da wani irin kallon ƙauna ta ce, “Ai kuwa a wannan zamani suke, yanzu haka ma suna tare da juna yana sakar mata ƙayataccen murmushi da kalaman da ke sawa ta ji ta tamkar wata sarauniya.”

Dariya ya yi sosai yana ji a ransa lallai wannan yarinyar ta musamman ce, ta haɗa komai. Ga kyau, ga iya magana mai ratsa zuciya. Cikin dariyar ya ce, “Ai kuwa ta fi sarauniyar ma a wajensa, yadda yake jin ta a ransa tamkar carbin ƙwai. Kuma indai wannan shi ne burinta, to ya lamince mata tun yanzu ma ta riƙa kiran sa Abban Khakil ɗin.”

Nishaɗi da fara’arta suka ƙara yalwatuwa sosai, yayin da shi kuma yake bin ta da wani asirtaccen kallo. Ta sunkuyar da kai ta ce, “Idan kuma mace ce na bar maka ka zaɓa mata sunan da kake so.”

“Idan mace ce sunan Umma za mu raɗa mata, kin ga mun samu Umma babba da Umma ƙarama.”

Murmushi ta yi kawai ba tare da ce komai ba. Sun jima sosai suna wannan hira mai cike da kauna. Da zai tafi ta rako shi har waje, ya dube ta ya ce, ‘To Maman Khakil ni zan wuce sai yaushe?.” Sunkuyar da kai ta yi cike da kunya ta ce “Kai ɗin nan ko! Ka gai da gida, kuma ka kula mini da kanka.”
Yayin da ta kawo nan a tunanin, sai ta saki ajiyar zuciya, ta miƙe da kyar ƙafafuwanta ke ɗaukar ta.

Banɗaki ta shiga ta watsa ruwa sama-sama. Fitowarta ke da wuya aka fara kiran sallar Azahar, alwala ta yi sannan ta koma ɗaki ta yi salla ta janyo jakarta ta Islamiyya da nufin ta bibiyi darusan baya. Amma sam sai abin ya gagara, da zarar ta fara ko layi guda ba ta kaiwa sai tunani ya katse ta. Ta yi ƙoƙari kauda tunanin amma abin ya gagari Kundila. Tattarawa ta yi ta ajiye ta ɗan kwanta bisa sallayyar, wani barci marar daɗi ya yi awon gaba da ita.

“Assalama alaikum wai ana sallama da Zaliha?” Murya wani yaro ce da ba zai wuce shejara goma sha biyu ba, lokacin da ya shigo tsakar gidan.
“In ji wa?” Umma ta tambaye shi.
Yaron ya ce, “Wani mutum a mota yana waje.”

“To je ka ce tana zuwa.”

Yaro ya fito ya faɗa masa abin da aka ce. Mutumin ya zaro naira dari biyu sabuwa kar ya miƙa masa, daidai lokacin Umma ta leƙo ta ga ko waye? Alhaji Saminu ta gani yana jayayya da yaron ya karɓi alherin da ya yi masa ya ƙi, yana cewa, “Wallahi an hana ni karɓar kuɗin wanda ban sani ba, na gode ka bar kuɗinka.”Yana faɗa ya wuce abinsa.

Da sauri Umma ta koma ciki, Zaliha na ɗakinta ta ji lokacin da yaron ya shigo da abin da ya faɗa. Kuma ta tabbata Alhaji Saminu ne ya zo. Kai tsaye Umma ta nufi wajenta ta ce, Maza ki shirya, Alhaji ne ya zo. Saura kuma idan ya ba ki kuɗi ki ƙi karɓa kamar yadda kika yi a waccan ranar, za ki ga yadda zan yi da ke a gidan nan.”
Uffan Zaliha ba ta ce mata ba, sai dai takaici da ke cin ranta. Ita ta rasa yadda aka yi mahaifiyar tata take masifar son kuɗi haka, ba a cikin wahala suke ba.

Abbanta ya tsaya musu tsayin daka, babu wata buƙata da ta taɓa gagarar su a iya saninta, to saboda me Umma za ta riƙa yin haka? Tambayoyin da ke kai kawo a zuciyarta ke nan, wanda kuma ba ta da amsarsu sai dai addu’a.
Nan ta miƙe a wulaƙance ta fito wajen Alhaji Saminu, sallama ta yi masa tare da gaishe shi, “Ina yini?”
Ya amsa da sauri, jin alamar kamar yau akwai sauyi a yadda suka saba, tunda ga shi har gaishe shi ma ta yi. Sai dai daga kalmomin can guda biyu ‘ina yini’, ba ta sake furta komai ba. Shi kaɗai ya yi kiɗansa ya yi rawarsa.

Kamar dai wancan zuwan, ashe yau ma Umma ta biyo ta zaure tana laɓe tana kallon su, ganin yana ta magana ta ƙi tanka masa ya fusata Umma. Komawa ciki ta yi ta sako hijabi ya fito, kai tsaye wajensu ta tinkara ta fara zazzaga wa Zaliha ruwan masifa, “Zaliha ba na son rashin mutumci da rashin albarka, wannan ai iskancin banza ne! Ya ya za ki tsaya ƙerere a gaban mutum yana miki magana kin yi banza da shi idan ba ki yi a hankali ba akan wancan yaron sai na tsine miki”

Kafin ƙiftawar ido jama’a sun kewaye wajen, sun yi musu kuri, ciki har da yaya Abdul.

Alhaji Saminu ya durƙusa har ƙasa yana cewa, “Baba a yi haƙuri ba komai, ai lamarin yaran zamani sai a hankali za ta gane.”

“Wannan ai sakarci ne, ga mutanen kirki sai ta biye wa mayaudari wanda ba auren ta zai yi ba. To daga yau kin daina zancen a waje, na ga ta iyashegen. Alhaji idan ka zo ka rika shiga ciki kawai, ai kai ma ka zama ɗan gida. Kuma indai Zaliha ce na ba ka ita halak malak!”

Cike da murna ya ce, “To Baba na gode sosai, Allah Ya saka da alkairi Allah Ya ƙara girma. Ni zan koma.” Ya saka hannu cikin aljihu ya zaro wasu kuɗaɗe masu yawa ya miƙa mata tare da cewa, Ga wannan, a gai da mini Abba idan ya dawo.”

“To ikon Allah! Har da ɗawainiya kuma, to an gode Allah Ya ƙara arziki.”
Ya buɗe mota ya shiga ransa fes, ita ma Umma ciki ta koma ranta wasai, tana jin burinta ya fara cika.

Ita kuwa Zaliha tunda ta tsugunna ta haɗa kai da gwiwa take wani irin kuka marar sauti amma sai azabar raɗaɗi a zuci, irin kukan nan ne mai illata zuciya. Mutanen da ke wajen sai mamakin abin suke, wasu na cewa, “Me yasa Umma za ta aikata wannan ɗanyen aiki na zubar wa kai ƙima da mutumci?” Wasu kuma suka riƙa ba wa Zaliha haƙuri da nasihohin ta bi mahaifiyarta kada ta saɓa mata.

Kowa ya watse aka bar Zaliha durƙushe, yaya Abdul ya matsa kusa da ita ya tsugunna tare da cewa, “Ina son ki yi duk abin da Umma ta umarce ki matuƙar bai saɓa wa shari’a ba, idan har kika saɓa mata to kada ki ce kin taɓa so na. Saboda haka idan har da gaske kike so na, to ki bi zaɓin da ta yi miki, ki aure shi ni na bar masa. Yanzu ina son ki tashi mu shiga gidan ki ba ta haƙuri bisa ɓata mata rai da kika yi.”

Sam ba ta yi tunanin yana wajen ba uwar ta yi haukan da ta yi, da irin miyagun kalaman da ta furta a kansa, sai yanzu da ta ji saukar sautin muryarsa a masarrafar sautinta. Ji ta yi da ma ƙasa ta tsage ta shige, ya fi mata sauƙi akan ta sake haɗa ido da shi. Cin mutumci da cin fuskar da Umma ta yi masa ya yi yawa. Shin wai me ya yi mata ne haka? Wannan ne tunanin da ya game Ilahirin zuciyarta, ta gaza koda motsawa.

Ya ci gaba da cewa, “Ki tashi mu shiga ba komai, kuma ba na son ki sa wannan abin a ranki, komai ya wuce.”
Shiru ba ta ce uffan ba kuma ba ta da niyyar tashi daga wajen, “Kowa ya tafi fa, daga ni sai ke. Ki tashi mu shiga.”
Da kyar ta miƙe kanta sunkuye suka shiga, Umma na zaune a falo ta baje kuɗin nan tana ƙirgawa tana sakin fara’a.

“Me kuma ka biyo ta ka yi maye?” Umma ta faɗa tare da aika masa wata mummunar harara.

Murmushi ya yi sannan ya ce, “Yi haƙuri Umma, da ma na zo ne na ba ki haƙuri kuma na sanar da ke cewa Zaliha ba ta da laifi. Kamar yadda kika ce ni ne mai laifi, amma ki sani ni ba yaudarar ta nake ba, Zaliha kanwata ce ba zan taɓa so ta shiga damuwa ba, hakazalika ba zan taɓa zama sanadin da za ta saɓa miki ba. Saboda haka ni na haƙura, Allah Ya ba su zaman lafiya, ke Zaliha ki ba wa Umma haƙuri kin ji. Ni na tafi.” Yana faɗa ya juya ya fice.

“Munafiki, ka ji da shi. Zaliha ce dai ƙwaleken ka. Yo ban da tsaurin ido ma irin naka, ina kai ina wannan tsaleliyar yarinya? Kawai don ka karantar da ita sai ka ce sai ka aure ta. Nawa ka ajiye a asusunka? Ta ya ya za ka iya riƙe ta? Zantukan da Umma ta riƙa yi ke yayin da take ƙirgar kuɗaɗen nan.

Raɓawa Zaliha ta yi za ta wuce ɗakinta tana kuka, Umma ta ce, “Ko kukan jini za ki yi sai dai ki yi, wannan yaron na raba ki da shi ke nan har abada. Kuma Allah Ya kai mu gobe Alhaji Saminu ya dawo zan ce masa ya turo a yi maganar auren, cikin sati biyu kacal tunda mai hali ne, na san zai yi miki kayan ɗaki duka.”
*****

Tun a waje aka tari Abba aka fara tsegunta masa abin da ya faru, to amma da yake ba a idonsa abin ya faru ba bai yi tunanin lamarin ya ƙasaita haka ba. Yana shiga gida bayan ya gama cin abinci ya ɗan huta sai ya ce da Umma, “Wani abin ne ya faru ɗazu? Na ji Malam Isa mai wanki ya fara yi mini maganar Zaliha.”

“Hmm! Kai ma ai ka san kwanan zancen! Akan dai wancan yaron ne da kuma shi Alhaji Saminu, amma na yi wa tufkar hanci.”

Abba ya ɗan gyara zama ya ce, “Wai mene ne ke faruwa Saratu? Shin wai ita yarinyar nan tana son shi Alhajin ko kuwa ke ce kike son shi.?

A wulaƙance ta dube shi ta ce, “Wace irin magana ce wannan? Shi yasa na ce kana goya mata baya. To bari ka ji daga yau maganar auren Zaliha ta fara, ka kwana da sani. Ya ce a shirye yake da wuri yake so a yi a gama.”

“To shi ke nan na ji, batun karatunta fa? Komai garaje ai a bari ta kammala sakandire ko?”

“A’a ba sai ta gama ba, zai bar ta ta ƙarasa a dakinta.”

“To shike nan Allah Ya tabbatar da alkairi.”
*****

Bayan kwanaki biyu, Alhaji Saminu ya sake dawowa, yaro ya aika ya yi sallama da Zaliha kamar yadda ya saba. Kai tsaye Umma ta leƙo ta ce, “Shigo mana Alhaji, ai ka zama ɗan gida.”

Shigar ya yi, Zaliha na zaune a falo. Ya durƙusa ya fara gai da Umma sannan ya zauna bisa kujera.

“Sannu da zuwa, ina yini?” Zaliha ta faɗa cike da takaici.

Umma ta ce, “To bari na shiga ciki, idan kun gama ki yi mini magana kafin ya tafi.

Mintuna kamar biyu babu wanda ya yi magana, zuwa can sai ya nisa tare da cewa, “Ya ya makarantar, yaushe za ku fara jarabawar ƙarshe ta kammlawa?”
“Ba a sanar ba.” Ta ba shi amsa a gajarce.

“Kafin ku fara ɗin ki sanar da ni duk abin da kike buƙata.”

Ba laifi hirar tasu, takan amsa masa wata maganar, wata kuma ba ta tanka masa. Jim kaɗan ya ce ta yi wa Umma magana zai tafi. A kufule ta miƙe ta nufi wajen Umma, “Ya ce zai tafi.” Ta faɗa ba tare da ta kalle ta, ta fito ta shige ɗakinta.

Da sauri Umma ta nufo falon cike da fara’a ta ce, “Alhaji har tafiya za ka yi da wuri haka?”

Kansa sunkuye ya ce, “E wallahi akwai wani taro da zan halarta ne. “

“To Ma Sha Allah! Da ma ina son na faɗa maka, idan za ka turo babu matsala. Wannan karatun ba dole sai ta gama shi ba, ko tana gidanka ne ta ƙarasa.”

Cike da farinciki ya ce, “To Baba ba damuwa, In Sha Allah zan turo sai a yi magana gabaɗaya.”

“Yawwa, kuma koyaushe ma kake so a ɗaura auren sai a yi, koda ƙasa da wata guda ne. Allah Ya saka da alkairi an gode.”

“Amin Baba, ai ni ne da godiya, Allah Ya ƙara girma.
Wasu damman kuɗaɗe masu yawa ya zaro daga aljihun babbar rigarsa ya ajiye a gabanta sannan ya miƙe ya fice ransa fes tamkar an yi masa albishir da gidan tsira.

Don haka tun a kan hanya ya fara tsara yadda yake so abubuwan su kasance. Kamar yadda Umma ta buƙaci a yi bikin da wuri, makwanni biyu kacal aka tsayar kuma ya amince zai yi mata kayan ɗaki duka. Ba ya buƙatar komai sai ita din. Nan fa ya zuge bakin lalitarsa Umma ta riƙa zuƙar madarar naira.

Aka yi biki Zaliha ta tare a wani katafaren gidansa da ke rukunin gidaje na unguwar, masu yatsu da yawa, darajar gidan ta ninka wanda matansa ke ciki sau uku, bai haɗa ta da du ba.

Mako guda da tarewarta amma sam ta ƙi yarda ko abinci su ci tare bare ya kusance ta har mu’amalar aure ta gifta a tsakaninsu. Ya yi rarrashi da ban-baki amma fur ta ƙi, kullum cikin kuka take. Da abin ya ishe shi, sai ya wanki ƙafa ya kai ƙarar ta wajen Umma. Haƙuri ta ba shi tare da tausar ƙirjinsa.

Bayan wani mako gudan, ba ta sauya zane ba, babu abin da ya canja. In taƙaice muku zance dai sai da Zaliha ta shafe wata guda cir a gidansa ba tare da ya ga kalar ɗan kamfanta ba.

Wannan shi ake cewa ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Ga bikin zuwa amma babu zanen ɗaurawa. Ga abinci amma ya gagara ciyuwa.

Da ya ga abin ba na ƙare ba ne, wai kukan aure da salati, sai ya sake komawa wajen uwar, domin an ce ta inda ka hau ta nan kake sauka. Ƙorafin ya sake yi mata a karo na biyu, haƙurƙurtar da shi ta sake yi tare da yin alƙawarin za ta je har gidan ta same ta ta ja mata kunne.

Washegari da hantsi Umma ta shirya ta yi wa gidan Zaliha tsinke, kai tsaye ta shiga ta iske ta kwance akan kujera a falo. Ta gaishe ta cikin ladabi da girmamawa sannan ta nufi kicin ta kawo mata abinci.

“Ba wannan ba ne ya kawo ni! Watau ke ba a isa da ke ba, kin fi ƙarfin mutane ko? Tunda kika zo gidan nan mutumin nan yake kai mini ƙorafinki, kin ƙi ki canja. To tunda haka kika ce za ki yi, bari na kashe ki kowa ma ya huta da baƙin cikinki.”

Tana gama maganar ta miƙe ta zaro lafceciyr wuƙa daga cikin hijabinta ta yi kan Zaliha ta kafta mata a kahon zuci.

Firgigit Zaliha ta farka tare da faɗin, “INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN! SUBHANALLAH!” Ƙirjinta sai dugun uku-uku yake, tana waige-waige tana ƙarewa ɗakin kallo. Nannauyan numfashi ta riƙa saukewa, kimanin mintuna biyar tana a wannan yanayi na firgici, tana jinjina wannan mummunan mafarki da ta yi. Addu’ar neman tsarin Allah ta yi daga sharrin da ke ƙunshe cikin mafarkin. Tana gama addu’ar ta miƙe ta nufi dakin Umma, ta gan ta ba.

Tsakar gidan ta fito, ta iske ta tana ‘yan aikace-aikace. Kamar ta sanar da ita labarin mafarkin sai kuma ta tuna ba wani zaman daɗi suke ba, don haka sai ta bar abin a zuciyarta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ko Wace Ƙwarya 3Ko Wace Kwarya 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×