Skip to content
Part 6 of 16 in the Series Ko Wace Kwarya by Sadik Abubakar

Cikin kukan ta ce, “Yaya Abdul…” Ya katse ta da cewa, “Babu wata magana da za ki sake faɗa mini, ki sakar mini ƙafa na tafi.”

Ƙara sautin kukan ta yi ta ce, “Don Allah ka tsaya ka saurare ni, yaya Abdul yanzu ashe ba ka fahimce ni ba duk zaman da ka yi da ni? Ka tuna fa tun ban san kaina ba kake reno na, idan har akwai wanda zai faɗi haƙiƙanin halin mutum to babu shakka malaminsa ne. Yaya Abdul ban yi tunanin ko a mafarki za ka iya furta waɗancan kalamai a kaina ba. Amma babu komai, ba na so ka sake yarda da ni ɗin. Ina so ka sani na rantse da Ubangijin da numfashina ke hannunSa ina son ka, wannan soyayyar taka a raina ba za ta fita ba sannan ba ban zan taɓa roƙon Allah Ya cire mini ita ba, sai dai na roƙe Shi da Ya ƙara mini koda za ta zama ajalina.”

Zantukan nata sun daki zuciyarsa matuƙa, bai taɓa yin shakku akan son sa a zuciyarta ba, amma abin da yake masa tuƙuƙi a rai shi ne, ta ya ya lokaci guda ta zo masa da wannan batu ba tare da an kai ruwa rana da ita ba? Ya kamata aƙalla ko za ta ba da kai bori ya hau, to a ɗan tayar da ƙura mana.

Kuka kawai take kashirɓan, shi ma kukan yake amma na zuci, fuskar nan murtik babu annuri.

Umma na ta jira ta ga Zaliha ta dawo amma shiru, miƙewa ta yi ta leƙo domin gane wa idonta. Karaf sai ta yi tozali da da Zaliha durƙushe tana kuka, “Zaliha mene ne haka? Me ya faru?”

Gabɗayansu suka firgita da jin muryar da ba su yi zato ba. Da sauri ya matsa kusa da ƙofar ya durƙusa tare da cewa, “Sannu Umma ina yini?”

Maimakon ta amsa masa gaisuwar sai ta zarce da faɗin, “Abin da nake so da kai, ka saurare ni da kyau. Zaliha an yi mata miji, don haka ka fita sha’aninta na ɓangaren soyayya. Yanzu ka kalle ta a matsayin ɗalibarka kamar sauran ‘yammatan. Da ma na ƙyale ka ne kawai ka kula ta na wucin-gadi, amma Zaliha ba sa’ar aurenka ba ce kana a wannan matsayin. Idan har auren kake so da gaske ga ‘yammata nan daidai kai, ko kuma ka koma can cikin dangi a ƙauye ka zaɓo. Saboda haka idan ita tana jin nauyin faɗa maka, to ni na isar maka yanzu sannan na yi maka togaciya da zuwa ƙofar gidan nan da sunan zance.”

Cikin risinawa da girmamawa ya ce, ”To shike nan Umma ba komai, na gode Allah Ya saka da alkairi sai anjima.”Ya faɗa tare da miƙewa ya bar ƙofar gidan.

Zaman dirshan Zaliha ta yi ta ci gaba da kuka da dukkan ƙarfinta, “Za ki taso ki shigo ko kuwa sai na fizgo ki?” Umma ta faɗa fusace.

Tamkar da gini take maganar, ko gizau ba ta yi. Babu shakka a yanzu tana jin matuƙar haushin uwar tata, duk da taka-tsantsan ɗin da take na gujewa saɓa mata amma ya zama tilas a wannan karon ta nuna mata ɓacin ranta. Don me za ta aikata wannan abin kunyar na zubar wa kai girma da martaba, duk irin girmamawa da biyayyar da yake mata amma ta rufe ido akan kuɗi?

“Ba za ki taso ba ko? To ki zauna a nan ko kuma ki bi shi ku tafi na bar masa ke tunda ban isa da ke ba!”

Ƙememe Zaliha ta kafe ta ƙi motsawa daga wajen, ci gaba da kukanta kawai ta yi. Ta jima tana kuka sannan ta yi shiru.

Tana nan zaune, zuciyarta ta fara ba ta wasu shawarwari, “Ki tashi ki bi shi ɗin kawai tunda dai shi ne masoyinki na asali, shi kike so. Idan Abbanki ya dawo ta san me za ta faɗa masa, tunda ta ƙi ta fahimci abin da take so ba lallai ba ne ya zama alkairi ba, amma ta kafe a kai.”

Wata zuciyar kuma ce mata ta yi, ‘Kada ki bi shi, ki tashi ki shiga gidan, amma ki taurare mata akan wanda kike so. Domin ke za ki zauna da shi ba ita ba. Kuma ƙila ita ɗin ba auren dole aka yi mata ba amma ga shi ke za ta tilasata miki, sam kada ki yarda.’

Zuciya ta uku kuwa cewa ta yi, ‘Kada ki tashi ki ci gaba da zama har Abbanki ya dawo ya same ki a nan, zai tambaye ki me ya faru sai ki warware masa zare da abawa. Domin mafi yawan abubuwan da suke faruwa ba sani yake ba, idan har tana taƙamar ita ta haife ki, to shi kuma mahaifinki ne. Da ita da ke duk a ƙarƙashin ikonsa kuke, da kai da kaya duk mallakar wuya ne. Shi zai san yadda zai ɓullo wa lamarin, ki yi haƙuri kowa da yadda jarabawarsa take zuwa daga wajen Ubangiji.’

Wannan shawarar ta ƙarshe ita ta fi kwanta mata a rai, domin babu shakka lamarin Umma ya fi ƙarfinta. Duk yadda ta so na ƙin kai ƙarar ta abin ya ci tura, tilas ne ta sanar da Abban nata.

Tana zaune sai ga hasken fitilar mashin nan ya karyo kwanar layin. Wani sanyi ta ji ya dira a tsakiyar zuciyarta. Yana ƙarasowa daf da gidan ta miƙe da dukkan kuzarinta ta buɗe masa ƙofar ya shige. Mamaki ne ya kama shi na ganin ta a wajen da wannan dare. “To ko me ya fito da ita?” A ransa ya yi wannan tambayar.

Ta bi bayansa yana tsayawa ya saukko da tambayar, “Lafiya dai Zaliha me kika fito yi yanzu?”

Rungume shi ta tana sakin ajiyar zuciya wata na korar wata, ta gaza magana.

“Ina Umman taki ne?” Kuka sosai ta fara tana rungume da shi. Dayake ya san ta da shagwaɓa, rarrashin ta ya riƙa yi ya kamo hannunta suka shigo ciki.

Umma na zaune bisa kujera ta dube ta ta ce, “Au ashe ba ki cika mai zuciya ba, ai na yi zaton kin bar gidan ke nan!”

“Wai me ke faruwa ne Saratu?
“Akan dai Abdullahi ne, ya zo ya yi kiran ta ƙofar gida sai ƙarya da gaskiya yake shirya mata, ga wanda yake son ta da aure ta ƙi sauraren sa. Shi ne na je na faɗa masa ya rabu da ita tunda ta samu miji, to don me zan hana shi ɓata mata lokaci shi ne ta ja tunga a ƙofar gida take kuka.”

Cikin ɓacin rai Abba ya ce, “Saratu ba kya kyautawa, sam wannan ba huruminki ba ne raba su. Ba ki san lokacin da Allah Ya haɗa su ba, ina gudun sauyawar al’amari fa! Yadda kike nuna wa yaron nan ƙiyayya komai zai iya faruwa, daga ƙarshe kuma ki zo kina jin kunya.”

“Allah ma ya tsare ni da wannan baƙar ƙaddarar da zan ji kunyar sa, duk abin da zai sa na ji kunyar sa ba na fatan Allah Ya kawo mini shi.”

“To wannan kuma burinki ne, amma ki sani iyakacin abin da za ki iya yi ke nan, tabbatuwar abin ko akasin haka wannan ikon Ubangiji ne. Idan ya yi nufin Zaliha matarsa ce babu yadda za ki yi, kina ji kina gani kuma a gabanki da hannunki za ki wanke ta ki kai ta gidansa. Don haka idan za ki yi sara ki riƙa duba bakin gatarin ko don watan-watarana.”

Ya ɗan numfasa kaɗan sannan ya juya ya dubi Zaliha, ransa ya ƙara ɓaci ganin yadda ‘yarsa ɗaya tilo ta lalace ta rame. Nisawa ya yi sannan ya ci gaba da faɗin, “Yanzu duba ki ga yadda ta faɗa saboda tunani da tsangwama. Shin wai ba ki san cewa su ‘ya’ya amana ce ba kuma kiwo ne Allah Ya ba mu ba? Sannan sai ya tambaye mu yadda muka kiwace su, ya yi hisabi?”

A fusace ta ce, “Cutar ta nake yi ko? Watau kana nuna mata cutar da ita zan yi Allah zai saka mata ko? Tun ba yau ba na sani kana ƙoƙarin nuna mata kai ne kake son ta, ni ƙin ta nake ina ƙuntata mata. To gaskiya ka daina yi mini haka.”

Bai sake duban ta ba, sai ya juyo kan Zaliha, cikin lallausan harshe ya ce, “Ki kwantar da hankalinki, zan yi bincike akan mutumin idan ba na gari ba ne ba zan amince ba. Ba zan sa mata ido ba ta kai ki wajen da za a cutar da ke. Ki daina kuka kuma ki ci gaba da yi mata biyayya, kada koda wasa ki mayar mata da magana ko ta faƙa ki faɗa. Sannan idan Abdullahi ya yi miki magana ki saurare shi, kada ki taɓa yi masa wulaƙanci.”

Cikin dukkan ladabi ta ce, “Abba ya yi fishi fa sosai wallahi! Ba na jin ko a makaranta zai sake shiga sabgata, abin da Umma ta faɗa masa ya ce ya ji kuma zai yi aiki da shi.”

“To shike nan ki bari ni zan neme shi zan yi masa bayanin da zai fahimce al’amarin. Kin dai ci abinci ko?”

“E, na ci.”

“To ki je ki kwanta, Allah Ya yi miki albarka.”

Miƙewa ta yi ta nufi kicin ta ɗauko masa abincinsa sannan ta wuce ɗakinta. Umma na bin ta da harara har sai da ta shige.

Abba kuma ya dube ta cike da jin takaici ya ce, “Watau Saratu na lura so kike ki zama marar godiya ga ni’imar da Ubangiji Ya yi miki, kuma ina mamakin lokacin da kika sauya haka. Kin tsangwami yarinya babu gaira babu dalili, kawai don biyan buƙatar kanki. Idan wata matsala kike gani a tattare da yaron ai ba shi kaɗai ba ne ke son ta, sai ki ba ta dama ta fitar da wani, ba ki ce lallai sai ta auri wanda ke kike son shi don cim ma buƙatarki ba. To ki sani ba zan laminci wannan abin ba, ina kallo ba zan bari ki jefa mini yarinya cikin ƙunci da damuwa ba.”

Sama ta taso tamkar bubukuwa ta ce, “Yo akwai ƙuncin da ya wuce inda take burin kai kanta? To ka sani ni ma ai ina da hakki a kanta, don haka ba zan bari ta shiga cikin matsala ba. Kuma da kake cewa don buƙatar kaina nake so ta auri mai kuɗi, ai ba ni kaɗai zan ci arzikin ba, kai ɗin da kake faɗin haka sai ka fi kowa zaƙewa, a lokacin duk ka manta da haka.”

“Wa? Allah Ya rufa mini asiri, ai ni ba girman kai ba, babu sirikin da zan buƙaci abin hannunsa. Alhamdulillah, na gode wa Ubangiji da abin da Ya ba ni. Ke dai da zuciyarki talaka ce har kika mayar da ‘yar cikinki HAJA, kike neman kuɗi da ita, kika fifita ƙazantar duniya akan walwala da kwanciyar hankalinta sai ki je.”

Daga haka bai sake tanka mata ba, nan ta ƙaraci sababinta ta yi shiru. Shi kuwa abincinsa ya ci yana gamawa ya miƙe ya nufi ɗaki ya yi kwanciyarsa.
*****

To a ɓangaren yaya Abdul kuwa, tafe yake babu laka a jikinsa. Jin lamarin yake kamar a mafarki. A haka ya isa gida, sallama ya yi cikin sassanyar murya. Inna na sauraren radiyo, ta amsa masa.

Kai tsaye ya shige ɗakinsa. Kwanciya ya yi ya gaza tantance wane irin yanayi yake ciki, baƙin ciki ne ko kuwa? Zuciyarsa ta gaza tsayar masa da tunani guda ɗaya tartibi, da ya fara wannan tunani sai wani kutso. Juyi kawai yake bisa shimfiɗarsa.

“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN! Wace irin ƙaddara ce wannan? Wane irin tunani Umma take yi a kaina? Shin me take nufi da kalamanta na cewa Zaliha ba sa’ar aurena ba ce? Da ma fuska biyu ce da ita? A Baki Musa a zuci Fir’auna? To me na yi mata har da za ta yi mini wannan hukunci? Ire-iren tambayoyin da suke ta sintiri a ransa ke nan.

Kimanin mintuna goma sha zuwa sha biyar yana kwance a wannan yanayi. Ya miƙe zaune daidai lokacin zuciyarsa ta shiga tariyo masa wasu al’amuran da suka gabata a tsakaninsa da Zaliha da kuma mahaifiyar tata.

“To Zaliha kin ga dai halin da muke ciki a yanzu, Abbanki an rike masa albashi har watanni uku, don haka kawai ki yi haƙuri da makarantar nan. Ni da ma tun asali na san tsarabe-tsarabenta yawa ne da su, ni kuma kin ga ba wani abin nake ba bare na biya miki.”

Cikin nutsuwa ba tare da nuna rashin jin daɗi ba Zaliha ta ce, “To shike nan Umma ba komai, ai na san da akwai za a biya mini. Amma don Allah ki yi mini alfarma ɗaya, a maimakon na daina karatun gabaɗaya, ina ga zai fi a mayar da ni maƙarantar gwamnati ko?”

“E haka ne, amma ita ɗin ma dole sai an kashe kuɗi. Ko banza sai an ɗinka miki wani uniform ɗin da kuma ɗan abin da za a miƙa.”

“Shike nan Umma ba komai Allah Ya shige mana gaba.”

Kwanaki biyu ke nan Zaliha ba ta shiga maƙarantar boko ba a sakamakon hukumar makarantar sun dakatar duk ɗaliban da ba su biya kuɗin makaranta ba.

A rana ta uku na zamanta a gida, yaya Abdul yake tambayar ta a Islamiyya wacce take zuwa bayan La’asar zuwa Magariba, game da fashin da take a boko.

Ƙarya ta yi masa da cewa, “Wallahi ba ni da lafiya ne.”

Murmushi ya yi mai cike da mamaki sannan ya ce, “Ikon Allah! Wace irin rashin lafiya ce ba ta tashi sai da safe, idan rana ta yi kuma sai a warke?”

Kunya ta lulluɓe ta ta rasa yadda za ta yi, wannan rarraunar ƙaryar tata ko ƙaramin yaro ba zai yarda ba. Ita da kanta ta yi mamakin ya aka yi ma bakinta ya suɓuce ta furta ta?
“Ki dai faɗi gaskiya abin da ya sa ba kya zuwa.”

Shiru ta yi kanta sunkuye har yanzu kunyar ba ta sake ta ba, sannan kuma ba za ta iya faɗa masa gaskiyar abin da ya hana zuwa ba. “Kin ƙi yin magana, ko sai anjima da marece idan na zo gidan?”

Kai ta girgiza masa kawai cike da zaƙuwar su rabu ko ta samu sauƙin jin kunyar da ta sa ko motsawa ba ta son yi.

“To shike nan ki gai da gida, ki gai da mini da su Umma, sai na zo ɗin.” Ya faɗa tare da juyawa ya koma cikin maƙarantar.

Sai da ta tabbatar ya shige sannan ta yi gaba. Dariya ita ma ta riƙa yi wa kanta akan wannan ƙarya wacce ko a cikin labaran littafi ba a cika jin ta ba. Shi ma dariyar ya riƙa yi mata, ya san ta yi ƙaryar ne don ta ɓoye masa wani abin. Halinta na jin kunya ya sa bai matsa akan lallai sai ta faɗa masa ba. Ƙila da daren ta iya fada masa.

Yana zama kwatsam sai tunaninsa ya kai kan kuɗin makaranta, dayake shi yake biya wa ƙanwarsa Jamila. Take sai ya ji a ransa ba mamaki rashin biyan kuɗin ne ya zaunar da ita a gida, kasancewar ya lura da rashin zuwan ba ita kaɗai ba ce.

Bayan sallar Isha ya isa gidan kamar ya saba, yaro ya nema ya aika, tana zaune a falo ta gama shiri, zuwansa kawai take jira. Miƙewa ta yi suka fito tare da yaron. Tana haɗa ido da yaya Abdul ɗin sai ta ji kunya ta sake tamke ta. Haka dai suka juya ciki tana gaba yana baya har zuwa falo. A ƙasa ya zube ya fara gai da Umma, ta miƙe ta ba su waje.

Murmushi kawai suke musaya a junansu kimanin minti ɗaya sannan ta ce, “Sannu da zuwa, ina yini?”
Ya amsa mata da cewa, “Lafiya ƙalau, ya ya jikin namu? Au ashe fa sai da safe ne ba mu da lafiyar!”

Kunya ta sake tamaimaye ta, sunkuyar da kai ta yi. Ya ci gaba da cewa, “Gaskiya wannan cuta tamu ta musamman ce, ya kamata mu gayyaci ‘Yan Jarida su zo su yi hira da mu, domin wannan labarin zai ba da citta.”
Cikin shagwaɓa sosai ta ce, “Allah zan tafi na yi barcina tunda tsokana ta kake yi.”

Ya kwashe da dariya sannan ya ce, “Allah Ya ba mu haƙuri, ai ba tsokana ba ce. Sannu da jiki nake yi mana, wanda ba shi da lafiya kuma idan aka ce masa sannu daɗi yake ji.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ko Wace Kwarya 5Ko Wace Ƙwarya 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×