Skip to content
Part 9 of 16 in the Series Ko Wace Kwarya by Sadik Abubakar

Kimanin sati biyu ke nan rabon yaya Abdul da gidan su Zaliha, kuma ko waya ma ya daina yi mata, idan ta je makaranta tsakaninsa da ita kallo kawai. Lokuta da dama ma ba ya taɓa yarda su haɗa ido, idan aka tashi a yanzu takan jira shi a waje, amma sai dai ta gaji ta tafi.

A zahiri ne ya daina sauraren ta amma cikin zuciyarsa fal ƙaunarta ce, babu abin da ya ragu face ƙaruwa, daurewa kawai yake yana dannar ƙirjinsa. Saboda abin da ya gani kuma ya fuskanta da Umma zai yi matuƙar wahala wani mahaluki ya iya sauya mata tunani akan ‘yar tata, ko shi Abban ya dai faɗi haka ne kawai don ya kwantar masa da hankali.

To ita ma dai Zalihar, abin da ke gidan Ƙaura shi ne a gidan Goje. Son yaya Abdul a ranta ƙaruwa ya yi sosai, tsantsar biyayya da rashin son saɓawa mahaifiyarta ne ya sa ta amsa mata akan za ta rabu da yaya Abdul kuma ta auri Alhaji Saminu. Babban abin da ke ƙara ɗugunzuma mata rai shi ne irin yadda ya yi watsi da ita cikin ɗan ƙanƙanen lokaci ko fuskarta ba ya son gani ya yi sha’awar jin muryarta.

Wannan tunani wani lokacin har shakku yake sa mata game da son da yake mata, “Anya da ma ba sama-sama yake so na ba? Daga yin wannan ɗan artabun sai ya ɗauke ƙafa, bayan ba ni na ce ba na son sa ba.” Tana gama wannan tunani sai wani kuma ya kutso kai, “Amma ban ga laifinsa ba, kowaye aka yi wannan cin fuskar zai iya rabuwa da yarinyar koda kuwa ‘yar Santanbul ce. Umma ta yi rashin kyautawa, dole ma ya ji tsoron ci gaba da kula ni, wacce duk ta iya yi wa saurayin ‘yarta wannan tijarar, to wataran abin da za ta yi sai ya ninka wannan ɗin.”

Wannan ne aikin da zuciyar Zaliha ta samu duk lokacin da ta yi tunani makamancin wannan.

To a hannu guda kuma Alhaji Saminu ya samu karɓuwa sosai a wajen Umma, duk lokacin da ya zo zance bayan sun gama da Zaliha sai ya nemi Umma ta fito su gaisa kafin ya tafi, yana yin haka ne sakamakon ya buga ya raya Zaliha ta riƙa karɓar kuɗin da yake ba ta ta ƙi. To idan suka gaisa sai ya ajiye mata kuɗaɗen ya miƙe.

Duk zuwan da yake bai taɓa haɗuwa da Abba ba, kasancewar yakan zo da wuri kuma ya tafi da wuri tunda abokiyar hirar ba wani haɗin kai take ba shi ba. Sai ya daɗe da tafiya sannan Abban yake dawowa. Wannan dalili ya sa Alhaji Saminu ya buƙaci yadda zai gana da shi domin ya ga karɓuwar da zai yi a wajensa.

Umma ce ta tsara tare da sanar da Abban zai yi baƙi don haka ya dawo da wuri, bai yi ja-in-ja da ita ba, cewa ya yi Allah Ya kai mu lokacin. Haka aka yi kuwa da marece ranar da aka tsara Alhaji Saminu zai zo, zuwan ya yi tare da rakiyar wani abokinsa.

Suna isowa sallama ya tura a yi, Umma ta ce ya shigo. Da ma dai ta shirya tarbar su. A falo aka sauke su. Umma ta umarci Zaliha da ta kawo musu ruwa. Fuskarta a cushe ta kawo ta ajiye gabansu bayan ta yi musu sallama. Alhaji Saminu murmushi kawai yake, komawa Zaliha ta yi ta faɗa wa Umma cewa ta kai musu sannan ta wuce ɗakinta.


Fitowa Umma ta yi ta zo suka fara gaisawa sannan ta koma ta ce wa Abba, “Ga su can sun iso, ka je ku gaisa ko?”

Mamaki ne ya kama shi sosai ganin yadda take haba-haba da rawar jiki tamkar wacce aka yiwa albishir da gidan Salama. Sun ɗan jima kamar mintuna goma sannan Abban ya fito, fuskarsa ba yabo ba fallasa ya isa. Zamewa suka yi daga kan kujera zuwa kasa, da sauri ya ce, “Ku miƙe, haba ku koma ku zauna kan kujera. Sannun ku da zuwa.”

Fuskokinsu cike da murmushi suka ce, “A’a ba komai wallahi!”

Suna durƙushen suka gaishe shi, ya amsa musu cikin karramawa sannan ya sake cewa, “Ku zauna kan kujera.”
Kan kujerar suka koma zauna. Abban ya ci gaba da faɗin, “An yi mini bayani zuwanku, abin da nake so da ku shi ne, kun riga kun san yadda lamarin aure yake. Wani ba ya taɓa auren matar wani, idan Ubangiji Ya ƙaddara matarka ce, babu wani mahaluki da zai hana. Hakan nan idan babu aure a tsakaninku to babu mai ikon haɗawa. Amma duk da wannan ƙa’idar, hakan ba ya hana neman yardar juna, ina nufin ku sasanta kanku kai da yarinya. Idan Allah Ya ƙaddara, to ka sani kai babba ne. Idan ka ji; ka toshe kunnuwanka. Idan ka gani; ka rintse idonka. Ka yi haƙuri ɗoriya akan wanda kake yi, ba zan tsawaita da yi maka bayanin yadda ake tafiyar da harkar iyali ba. Domin kai ma wataƙila ka bayar ko kana shirin bayarwa, Allah Ya shige mana gaba.”

Tunda ya fara maganar kansu sunkuye yake, sun tattara dukkan nutsuwarsu, sai da ya yi shiru sannan Alhaji Musa ya nisa tare da cewa, “Wannan haka yake, kuma mun gode sosai Allah Ya saka da alkairi, Allah Ya ƙara girma.”
“Ma Sha Allah!” Abban ya fada tare da barin falon.

Umma ta komo falon da sakin murmushi mai ɗan sauti ta ce, “Ikon Allah! Ko ruwan ba ku sha ba ai.”
“Hmm! Ba komai, tafiya za mu yi.” Alhaji Musa ya faɗa.

“To madalla! Bari na turo ta sai ku yi sallama.” Ta faɗa tare da juyawa ta nufi ɗakin Zaliha. Kwance take fuska a ɗaure, Umma ta ce, “Duk ɗaure fuskar da za ki yi sai dai ki yi, magana ta zo ƙarshe, tunda shi ma Abban naki da yake daure miki gindi yanzu ya fara fahimta. Ki tashi ki je tafiya za su yi.”

Miƙewa ta yi ta yo falon ta zauna ta yi turus kamar gunki, Alhaji Musa ne ya dube ta cike da murmushi ya ce, “Amaryarmu ki kwantar da hankalinki, nan ba wajen da za ki sha wahala ba ne. Waje ne da aka san ƙima da darajar mace, za ki samu dukkan wata kulawa. Babban burinmu dai a mallaka mana zuciyar nan mai daraja, mu kuma In Sha Allah za mu ba wa marar ɗa kunya.”

Wani ƙududun baƙin ciki da takaici ne yake mata tuƙuƙi a rai. Abin da ya fi soya mata zuciya shi ne, manyan mutane ne wanda sun yi sa’annin Abbanta, ga zawarawa nan daidai da su amma ba za su aura ba sai jikokinsu. Wannan wace irin budurwar zuciya ce haka?
Ya ci gaba da cewa, “To za mu tafi?”
Sai yanzu ta buɗa baki ta ce, “A sauka lafiya.”

Kuɗaɗe da yawa ya zaro ya ajiye, suka miƙe suka fito.

Umma da sauri ta fito idonta akan kuɗaɗen nan, kai tsaye wajensu ta yo ta ɗauka tana sakin murmushi daidai lokacin Abba ya fito falon, duban ta ya yi yana faɗin, “Wannan ba ya nufin cewa na amince da shi, sai na yi bincike a kansa kuma zan ji ta bakin yarinya tukunna. Na lura buƙatarki ce kawai, wannan ƙazantar duniyar kike kwaɗayi.”

“Girma dai bai ce haka ba, baki biyu ba halin dattako ba ne. Mutum ya tako har gida ya gaishe ka, ka amince amma ka ce sai ka yi bincike a kansa.

Da ganin wannan bawan Allahn ka san ba zai yi wasa ba, kuma yarinya indai za ta kwantar da kai ta yi masa biyayya babu abin da ba zai yi mata ba. Kai dai addu’a kawai ya kamata ka yi Allah Ya tabbatar da lamarin.”


“Addu’a kullum ina yi amma ba irin wacce kike so ba, idonki ya rufe saboda kuɗi kike burin auren ya tabbata, ba kya hangen abin da zai iya biyo baya.

A maimakon yin addu’ar Allah Ya tabbatar da auren, me zai hana ki ce Allah Ya tabbatar da abin da ya fi zama alkairi? Wannan ita ce addu’ar muminin ƙwarai, watau ya ba wa Allah zaɓi, ba ya zaɓa wa kansa ba ɓangaren da yake buri ba, wataƙila ya kasance ba alkairi ba ne.”

“Kai dai har kullum idan zan yi addu’a sai ka kawo Ƙauli da Ba’adinka. Mene ne abin rashin alkairin a tare da wannan mutumin? To In Sha Allah alkairin ne zai biyo baya.”

Haka dai ya gaji ya ƙyale ta, duk inda ya ɓullo sai ta zille.

Alhaji Saminu suna tafe da abokin nasa ya ce, “Ka ga dai yadda ‘yar gidan tawa take, ta ki sakin jiki.”

Cikin sigar ƙwarara gwiwa Alhaji Musa ya ce, “Haba! Kada ka damu da wannan fishin, na ɗan lokaci ne. Ka manta Zainab lokacin da muka fara zuwa wajenta, wane irin nau’in wulaƙanci ne ba ta yi mana ba? Amma da Allah Ya yi sai na mallake ta yanzu ga shi kamar ba a yi turmin danyar da ita ba. Ai su irin waɗannan yaran ƙanana sai an bi a hankali, haka za mu riƙa jure duk abin da za su yi mana. Yo kai ai matsalarka da ita mai sauƙi ce, fishi ne da rashin son yin magana, idan za ka iya tunawa Zainab har maye marar zuciya sai da ta ce mini. Amma dayake na san zuciyar tawa ba za ta iya haƙura da ita ba, ai dariya ma na yi lokacin da ta faɗi hakan.”

Ya ɗan tsahirta kaɗan kafin ya ci gaba Alhaji Saminu ya ce, “Haka ne!”

“Sannan abin da na lura da shi uwar yarinyar tana son al’amarin sosai, wanda nake ganin kamar zai ba da matsala uban ne. Amma tunda uwar tana so to shi ma za ta tanƙwara shi dole ya so.” Ya ƙarasa maganar da sakin dariyar ƙeta.

Haka suke tafe suna tattaunawa har ya kai abokin nasa gida sannan shi ma ya nufi nasa gidan.

Bayan sati ɗaya da zuwansa, ya tura magabatansa su nema masa auren Zaliha bisa al’ada. Irin zuwan nan ba bai-ɗaya aka yi, watau nema haɗe da sa rana. Ƙanen Abba wanda ke amsa suna Ibrahim, da wan Umma ana kiran sa Malam Jibrin sai wasu maƙwabta mutum biyu su ne suka tarbi waƙilan Alhaji Saminu.

Bayan an gaisa manema suka gabatar da buƙatarsu, mai bayarwa watau ƙanen Abba ya amince. Nan take aka gabatar da dukiyar aure tare da tsayar da rana. Wata guda kawai aka saka ranar, ya kama bayan mako guda ke nan da kammala jarabawar sakandire wacce Zalihar ke shirin farawa. Daga ƙarshe aka yi addu’a fatan alkairi kowa ya watse.

Umma farinciki da murna kamar su kashe ta, ji take tamkar ita zai aura. Shi ma a nasa ɓangaren, ya yi murna sosai. To wannan ke nan!


*****
Masu hikimar magana na cewa, “Zancen duniya ba ya ɓuya.” Wannan batu haka yake ba shakka. A wayewar garin daren da aka kawo kuɗin auren Zaliha, tuni zancen ya dira a kunnuwan yaya Abdul da ɗumi-ɗuminsa.

Labarin ya daki zuciyarsa matuƙa. Dauriyar da yake yi sai ya ji ba zai iya ba, ashe raɗaɗin da yake ji a baya sam ba komai ba ne. Wasa farin girki! Yanzu ne ya tabbatar da cewa ya rasa Zaliha. Ranar Juma’a ne aka kawo kuɗin, washegari Asabar babu makaranta, boko sai Islamiyya kuma yanzu ba ta zuwa. Ga shi yana masifar son su haɗu da ita, ba don komai ba sai don ya amayar mata da wasu martanai.

A da can bai cika ganin laifinta ba, to amma yanzu lokaci ya yi da ya kamata ya buɗe mata aiki, tunda dai ta kufce masa babu sauran tausayawa. Alatilas ya yi haƙuri zuwa ranar Litinin, wadda ta kasance ranar da za su fara rubuta jarabawa. Da wuri ya fita daga gida ya nufi hanyar da ya san tana bi, zuwa makarantar ya tsaya. Babu jimawa kuwa sai ga ta nan tana tafe cikin nutsuwa. Ba ta waige-waige idan tana tafiya, takan fuskanci gabanta ne kawai, don haka har ta gota shi ba ta lura da shi ba yana tsaye kan mashin ya juya baya. Kafe mashin ɗin ya yi, ya taka ya bi bayanta. Daf da ita ya ce, “Babu shakka na yarda da abin da zuciyata ta riƙa haska mini game da ke, yau ga shi kin tabbatar mini. Amma ina so ki sani Allah sai ya saka mini.”

Jin maganar ta yi kamar daga sama, cak ta tsaya tare da waigawa. Ya ɗauke kansa bai yarda sun haɗa ido ba, ya ci gaba da faɗin, “Na gode wa Allah da ya nuna mini haƙiƙanin halinki kafin na aure ki. Zaliha ke maci amana ce, soyayyata a ranki ƙarya ce.

Mahaifiyarki ta kira ni ɗan yaudara a gabanki, kalmar ta ƙona mini rai, matsayin uwa na ɗauke ta har gobe. Aure kuma ina miki fatan alkairi.”Yana faɗa ya juya zai tafi, ta yi sauri ta riƙo masa hannu ta ce, “Wannan ba ita ce maganar da ta sa ka tako ka zo har nan don mu hadu ba, idan ka koma to ka yi asarar ƙafarka da lokacinka. Idan kuwa ita ce ta kawo ka, to a iya sanina kai ɗin adali ne. Kana ba wa kowa damarsa ya faɗi abin ke ransa, ka faɗi abin da harshenka ke so, amma ni ka ƙi ba wa nawa bakin dama ya fesar da abin da ya gumtse. Shin ka yi hakan ne a matsayin sakayyar cin amanar da na yi maka?”

Ta ɗan tsagaita ba don ya ba ta amsar tambayar da ta yi ba, sakin hannunsa ta yi sannan ta ɗora da cewa,

“Kodayake bai kamata na hana ka tafiya ba, je ka. Amma ni ma ina son ka sani tafiyar taka ta tabbatar mini da abin da nake zargi a kanka. Ban taɓa gaskatawa ba, duk lokacin da na ji zuciyata ta fara mini hasashen hakan, nakan nemi tsarin Allah daga shaiɗan don na san sharrinsa ne. To ashe gaskiya zuciyata take nuna mini, na gode da fatan alkairi. Kafin na tafi zan jaddada matsayin zuciyata a kanka, ba wai don ka yarda ba. Yaya Abdul, tunda Allah Ya sa na kawo munzalin fahimtar abin so da abin ƙi, ban taɓa jin son wani ɗa namiji ba face kai, kuma ba zan taɓa jaraba son wani ba a yanzu. Kai nake so! Kai zan ta so a kowanne irin yanayi, son ka ne a zuciyata. Idan Ubangiji Ya ƙaddara ba za ka zama mijina ba, to ina roƙon Sa Ya tsayar mini da wannan ƙaddarar a iya nan gidan duniya, a lahira ina roƙon Sa da ya haɗa ni da kai a gidan Aljanna. Ina da tabbacin zai amsa mini roƙona, domin duk abin da bawa ya kyautata niyya ya roƙi Mahaliccinsa a nan duniya ya ga bai ba shi ba, to tabbas Ya yi masa tanadin sa a dawwamammen gida wanda ya fi nan alkairi.”

Gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi liƙis, zantukan nata sun ratsa masa zuciya matuƙa. Tausayin ta ne ya kama shi sosai, babu shakka yarinyar tana son sa so na haƙiƙa, kuma kamar yadda ta faɗa babu wani namiji take so sai shi, shi ɗin shaida ne akan haka.

Cikin rarraunar murya ya ce, “Na gaza samun sauƙi da sukuni ne a raina! Tun ranar da Asabar ban rintsa ba, ko na kwanta babu abin da nake sai tunanin yadda zan yi rayuwa ba tare da ke ba, ba zan iya ba! Ba da son raina na faɗa miki waɗannan kalaman ba, kawai na ga kin nuna kamar ba ki damu da rabuwar tamu ba, ko nema na ba kya yi.”

“Yaya Abdul ke nan! Yanzu ni ban yi wannan ƙorafin ba sai kai? Gabaɗaya ka janye mini lokaci guda, duk abin da zai haɗa mu magana ka dakatar da shi. Wani lokacin kafin a tashi daga makaranta ka fice kuma duk don kada mu haɗu ne. Idan ka shigo ajinmu ba ka taɓa yarda mu haɗa ido, ni har tsoron ka na fara yi. Zuciyata ni kaɗai na san abin da nake ji.”

Hawayen da take ta jarumtar riƙewa suka cika mata idanu fal! Ɗumin saukarsu ta ji a kuncinta, cikin dabara ta juya ta share sannan ta ɗora da faɗin, “Kuma tun daga ranar da Umma ta faɗa maka wannan maganar ka rufe lambata, ka hana kirana shiga wayarka, ko saƙo na tura ba ya tafiya.”

Cikin sautin kuka maganar ta riƙa fita, abin da ya ƙara ɗaga masa hankali ke nan. Ya dube ta sosai ya ga yadda ta faɗa ta lalace, duk wanda ya san ta a baya yanzu ya gan ta zai yi tunanin lallai wani abin yana damun ta, kodai rashin lafiya ko kuma damuwa ta samu muhalli a zuciyarta.

Murya ƙasa-ƙasa ya ce, “Ya isa, ki daina kukan haka. Mu ci gaba da faɗa wa Allah kukanmu, babu abin da ya fi ƙarfinSa. Ki saki ranki, yau za a fara jarabawa. Mu tafi.”

Ya janyo mashin ɗin ya karkata mata ta haye ya ja suka tafi. Suna tafe yana ci gaba da yi mata lafuzan tausasa zuciya, sai da ya kawar mata da damuwarta kafin su isa makarantar.

To wannan ke nan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ko Wace Ƙwarya 8Ko Wace Ƙwarya 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×