Bismillahir Rahmanir Raheem.
"Gafara dai! Gafara dai boka!" Cikin tsananin tsawa da ƙaraji bokan ya ce, "Su waye nan? Ku dakata kada ku sake motsawa ko da taku guda ne."
Cak! Matan suka tsaya ba wacce ta ɗara daga wajen wanda ya kasance gindin wata itaciyar tumfafiya ne. Mintuna kamar biyar suna tsaye, cikin garjin rana mai tsananin zafi, yayin da shi kuma bokan sai iface-iface da siddabaru yake irin nasu na 'yan tsibbu.
Zuwa can ya kurma wani ihu mai matuƙar razanarwa, wanda saboda tsananin firgici, matan biyu suka ƙanƙame juna kamar ɗaya za ta shige. . .
Da kyau. Muna biye.