Skip to content
Part 1 of 5 in the Series Kowa Ya Debo Da Zafi by Fatima Rabiu


Ƙarar saukar ruwan sama me haɗe da iska yayi sanadin farkarwarta, a firgice tana me maƙurewa can ƙarshen gado tare da sakin a jiyar zuciya. Mummunan mafarkin da tayi ne ya dawo mata sabo fil, tamkar yadda mirror ke maido ma mutum ainahin suffar shi. Tuntsurewa tayi da dariya sakamakon tunawa da tayi da ƙudirinsu, sai dai saurin haɗiye dariyarta tayi sakamakon turo ƙofar ɗakinta da ta ji anyi. “Ninaah! Dariyar me kike yi haka? Ke tsaya ma! Me ya hanaki rufe ƙofa duk da ruwan nan da ake tsalawa?” “Umma bacci ne ya sace ni ina gama sallah, amma yanzu zan rufe” kallon tuhuma Mahaifiyar ta ke mata sakamakon hango rashin gaskiya ƙarara a fuskarta. Ganin Mahaifiyarta zata karbo jirgin ta ya sakata saurin kawar da zancen “Umma Abba ya dawo?” “A’a bai dawo ba ke ya ke jira” Umma ta ƙarasa maganar tare da ficewa daga ɗakin. Murmushi ta sake saki a karo na barkatai tare da ɗaukar wayarta tana tafiya cikin sanɗa. Jin mahaifiyarta ta shige ɗaki hakan ya bata damar shiga ɗakin da mahaifinta ke ajiye kudi ta kwashi adadin da zai isheta. Ƙarar shigowar sako a wayarta yasa ta firgita tare da saurin kallon screen “Lokaci ya na tafiya, ki tabbatar kin kasance cikin shiri” dariya ta saki tare da daka tsalle ta rungume wayarta, cikin sanda ta koma daki tare da fara haɗa kayanta bakin ta ɗauke da wakar Umar m Sharif mai taken gamu nan dai…

Cikin nutsuwa ta sauke wayar daga kunnenta ta na kallon tagar dakin ta da iska ya bude da ƙarfi. Walkiyar da aka yi ce ta saka ta saurin duƙewa tare da ambaton Sunan mahaifiyar ta. Ta share daƙiƙu kafin ta ɗago cikin tashin hankali don in akwai abinda take tsoro to bayan ruwan sama yake. Kiran Ninaah ne ya shigo wayar ta cikin hanzarin ta dauka. “Yanzu haka cikin shiri nake, ruwan nan ne ya tsayar dani, kin san dai ba zamu fita ba sai su Hajiya sunyi bacci” “Ban gane sai munyi bacci ba” Mahaifiyar ta da shigowar ta kenan ɗakin ta karasa maganar tare da kafe Zainabu kamar yadda take kiranta da ido. Dabur-burcewa Zuzuuh tayi kamar yadda kawayena ke kiranta. “Hajiya dama yanzu nake shirin zuwa in duba in ga shin kinyi bacci?” ” Ke kada ki mayar da ni shasha mana, ina za ki je kike fadar sai munyi bacci?” Hajiya ta ƙarasa maganar cikin haɗe fuska. “Dama… Dama, gobe ne zamu je wani bikin kawarmu shine na ce a bari da safe zan fada miki yanzu ina zanje tunda kinyi bacci”ƙure ta da ido Hajiya tayi tare da jefa mata kallon tuhuma don ko alama bata gamsu da wannan zancen ba, girgiza kai tayi tare da ficewa daga ɗakin. “Haba Hajiya! Sai ma gari ya waye kin nemeni kin rasa lokacin zaki gane karya na miki” Zuzuuh ta ƙarasa maganar tare da bude akwatin da ta zuba kayanta. Kudi ne barbaje da tayi nasarar kwasowa a dakin mahaifiyarta. Alamar shigowar sakon da taji ne ya saka ta daukar wayar “Ki fito yanzu, muna jira” kallon ƙofa tayi taga ruwan ya fara lafawa don haka daukar akwati ta tayi cikin sanda ta bar gidan ba tare da kowa ya sani ba.

Shurun da taji ita ta tabbatar mata da yan gidansu sunyi barci, don haka cikin natsuwa ta janyo katon akwatinta tana niyyar barin gidan. “Laaa! IBINA ina za ki je cikin daren nan ga ruwa anayi.” Gabanta ne ya yi mummunar faduwa ganin asirinta na shirin tonuwa. A fusa ce ta kalli ƙaramin ƙaninta “zan kai kayana dakin Momy ne uban yan sa ido, me ya fiddoka cikin daren nan?” “Motsinki na ji na fito” cikin dabara ta mayar da akwatinta daki tare da jan hannun ƙaninta taje ta kwantar da shi sai da ta tabbatar yayi bacci sannan ta fito tare da ja masu dakin kasancewar ita ce babba duk dare sai kannena sunyi barci take yi. “Shukurah bakiyi bacci ba har yanzu ?” “E Momy yanzu dai zan kwanta” ta karasa maganar da sauri ta shige dakinta. Jin tsit! Da tayi hakan ya tabbatar mata kowa yayi barci don haka cikin sauri ta bar gidan. “Ke kadai muke jira” shine sakon da ta gani kwance a screen din wayar ta. Murmushi tayi tare da bin wata hanya, don tana da tabbacin suna can suna jiranta…

Kowa Ya Debo Da Zafi 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×