Ibina dake kwance a sume da mugun sauri Fu'ad ya nufi inda take kwance, wani sauran ruwa ya rarumo ya fesa mata a fuska. Wata irin zabura sukai su duka ganin Nurse d'in da Zuzuuh ta cafke ma wuya itama ta fara wata irin mik'a k'asosuwan jikinta na bada wani sauti, k'as-k'as.
Ninaah ce ta matsa kusa dasu Fu'ad dake bakin k'ofa, tana k'ank'ame Fu'ad dake tsaye rik'e da Ibina, zazzare ido sukai ganin Ammar da Zuzuuh da Nurse sun mik'e suna wata irin jijjiga bakinsu. . .