Ibina dake kwance a sume da mugun sauri Fu’ad ya nufi inda take kwance, wani sauran ruwa ya rarumo ya fesa mata a fuska. Wata irin zabura sukai su duka ganin Nurse d’in da Zuzuuh ta cafke ma wuya itama ta fara wata irin mik’a k’asosuwan jikinta na bada wani sauti, k’as-k’as.
Ninaah ce ta matsa kusa dasu Fu’ad dake bakin k’ofa, tana k’ank’ame Fu’ad dake tsaye rik’e da Ibina, zazzare ido sukai ganin Ammar da Zuzuuh da Nurse sun mik’e suna wata irin jijjiga bakinsu da hak’uransu sunyi wani mugun tsini, kwayar idonsu ta zama fari fat ta koma irin na horror, jikinsu da fatar jikin nasu tayi wata irin kala kamar yalo, kamar an shafa masu tuka. Banko k’ofar d’akin da akai ne yasa suka zabura sukayi waje a da mugun gudu. Shugaban hotel d’in ne ya zo, kai tsaye d’akin ya kutsakansa a ciki, wadda yaje ya sanar dashi jikinsa na kyarma da harshan turanci ya ce “ranka ya dad’e karfa ka shiga d’akin nan, wallahi gwajin nan an samu matsala,kamar wata annoba ce ke shirin tunkaro mu in….. “Ka rufe ma mutane baki na ce ko” da sauri ma’aikacin hotel d’in ya tushe bakinsa da tafin hannunsa yana zare ido. Kai tsaye shugaban hotel d’in ya Banga k’ofar d’akin dasu Ammar ke ciki. Ai da mugun sauri ya fara ja baya, ganin yadda suka nufo k’ofar gadan-gadan suna faman mik’a hannunsu gaba, suna son kamoshi. Da gudu ya juyo zaiyo waje, sai dai akwatin maganin da Nurse d’in nan ta shigo dashi ya tade shi ya zube a k’asa. Ammar ne yayi kukun kura ya fad’a kansa yana neman kaima wuyan sa cizo. Kokowa suka shiga yi yana ihun taimako, gasu Zuzuuh dake gaf rufe sa suna wani gurnani da shinshine-shinshine. Motar asibiti ce ta k’araso tare da doctors wadda ma’aikacin hotel d’in ya kira su cikin sauri. Wani mugun k’arfi ne ya zo mai ya jawo akwatin maganin yana kwad’ama Ammar shi a saman kai, ai ko danda nan ya zube a sume. Sai dai yana k’ok’arin tashi su Zuzuuh suka turmushe shi, wata irin kokowa suka kamayi dashi, Zuzuuh ce ta samu sa’ar sa y’an yatsunta masu d’auke da farce mai mugun tsini ta karci wuyansa, danda nan jini ya kama zuba ta wuyan nasa. Ma’aikacin hotel d’in ne yayi hanzarin d’aukar wani k’arfe ya daddage iya k’arfin sa ya kwad’ama Zuzuuh a kai, ai ko Nurse d’in nan data rage ganin ta nufo shi yasa baiyi wata-wata ba itama ya kwad’ama shi itama ta zube a sume. Wata irin zabura shugaban hotel d’in yayi yana rungume ma’aikacin hotel d’in, rik’e wuyansa yayi yana sauke ajiyar zuciya, da sauri ya kalli doctors d’in dake tsaye ya ce “ku kwashe su mu tafi asibiti, ayi bincike mike damunsu, tunda nake ban tab’a ganin masifa irin wannan ba” Da sauri Doctors suka sasu akan gadon aka daure su tare da yin asibiti dasu. Fu’ad dasu Ibina suka rungume ya janye su daga jikinsa yaja hannunsu da nufin subi su asibitin, sai dai Haris dake tsaye ya dakatar dashi yana cewa “mun shiga uku, wannan wacce irin masifa ce?, ina kuma zaku je naga kana niyar binsu?” “Zamu bisu asibitin ne ai, domin hankalin mu bazai tab’a kwanciya ba, har sai an duba mike dumunsu” Da sauri Haris yaja baya yana cewa “kutumelesi inbisu su cinye ni, kana ganin yadda suke cafke mutane suna neman cizon mutum, gaskiya ni tsoro nake ji” Da sauri Ibina ta dafa shi tana cewa “haba! Haris tare fa mukazo dasu bai kamata dan wani abu ya sami y’an uwanmu mu kuma mu juya masu baya ba, sorry muje kawai” Jikinsa ne yayi sanyi, ganin Fu’ad yayi gaba, yasa suka rufa masa baya
Motor hospital su duka suka shiga harda shugaban hotel, dake rik’e da wuyansa yana yamitse baki, saboda wani irin zafi da yake jin wajan na mai, gani yayi wajan jini ya daina zuba, sai wani irin jini kalar ruwan ganye dake zuba, wani iri ya fara ji cikin jikinsa, ya fara wani irin gurnani da tari yana tushe bakinsa, ji yayi ba abunda yake bala’in so irin yaci nama, ko wanne iri ne, bai dai idasa kamuwa da cutar ba, sai yayi saurin gyara wuyan rigar tasa dankar wani ma yaga wajan yadda ya koma. Har suka isa asibiti ba wadda yayi magana kowa d abunda yake sak’awa a ransa. Babban asibiti ne mai girman gaske, mai cike da marassa lafiya, kota ina da y’an uwan marassa lafiyar cike da hospital d’in. Kai tsaye da motar asibitin ta tsaya, wasu doctos ne da Nurses suka nufo wajan da gadon d’aukar marar lafiya guda hud’u, saboda shugaban hotel d’in, su duka sakkowa sukai akasa su Ammar dake a sume har yanzu basu farka ba. Kai tsaye cikin ainahin asibitin aka wuce dasu, wani d’aki mai girma da tsari da kyau aka kwantar dasu. Wani doctor ne ya shigo ya fara zuwa wajan shugaban hotel d’in yana kallon sa ya ce “George, kai ne a nan, mi yake faruwa ne?” Dan ya mutse fuska George yayi yana k’ara dafe wuyansa da yake jinsa yanzu kamar ana tsikara masa allura, bai amsa ba saima damk’e hannun doctor da yayi da mugun k’arfi. Ba shiri doctor ya sake juyowa yana duban George, ganin yadda yake wata jijjiga akan gadon, gadon na girgiza kamar zai rabe gida biyu, k’asusuwan jikinsa ne suka fara wata irin k’ara kamar ana kakkaryarsu, idonsa a rufe, can aka ji ya daina wannan jijjiga, da sauri Fu’ad ya ce “anya George shima ba komawa irin su Ammar zaiyi ba, izuwa yanzu na gane duk wadda suka ciza ko suka karceshi zai iya komawa irinsu” Danda nan Haris ya k’ara ja da baya, wani irin tsoro ya k’ara rufe sa, yana gaf fita k’ofa Ibina ta cafke hannunsa, wata irin zabura yayi yana kiran “na shiga uku na, shikenan tawa ta k’are” Jijjigasa Ibina tayi tana cewa “kai Haris nifa ce, ina kake niyayar zuwa naga kana niyar fita” Tana rufe baki suka ji ihun doctor, su duka da mugun sauri suka kai dubansu a inda suke, ganin yadda George ya koma shiga ya cafke hannun doctor ya kai mai wani mugun cizo, jini sai zuba yake a hannun nasa, ba shiri Fu’ad ya tuna idan ka buga masu wani abu a kai suna suma, kuma suna dad’ewa basu farka ba, yasa ya d’au wani k’arfe yana nufar inda suke, yana zuwa ya shammaci George ya kwad’a mai shi a kai. Suma yayi, inda doctor ganin ya sakar mai hannu yasa ya fara yamutse fuska yana rik’e hannunsa dake zubar jini, kallonsa Fu’ad yayi da tausayi, yana sharce gumi. Haris dake tsaye Ibina rik’e da hannunsa, ya fisge yana cewa “cika ni na ce, na rantse bazan zauna a nan ba, haka kawai idan zaku iya zama ku zauna kunga tafiya ta” Yana shirin b’ude k’ofar ya fice yaji muryar doctor na magana cikin wata irin murya me kama da saukar aradun…