Skip to content
Part 10 of 18 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Da dare ya yi bayan Abba ya dawo ya gama cin abinci yana falo zaune ana hira Humaira ta dauko teller ta biyan kudin registration ta mika masa, Mummy ta dube ta ta ce, “Kai Humaira kin fiye zumudi wallahi ki bari ya huta sosai mana, sai ka ce yanzu za ki koma makarantar.”

Abba ya yi murmushi tare da cewa, “Rabu da ita, ai tunda dai tana son karatun Alhamdulillah. Ina fatan dai za ki mayar da hankali sosai banda wasa ko biyewa kawaye shashashai. Yanzu gobe ne za ki je biyan kudin ko kuma yaushe?”

“E Abba gobe nake son na je kada ya zama late registration ana karawa mutum kudi idan ya makara.”

“To babu damuwa da safe sai ki karba a wajenta zan bata naira dubu ashirin (₦20,000), dubu goma sha-biyar (₦15,000) kudin registration dubu biyar (₦5,000) kuma sai ki sayi takalmin ko.”

Cikin yanayin shagwaba Humaira ta tabe baki ta ce, “Abba dubu biyar fa sun yi mini kadan, bani da jaka ma kuma akwai departmental registration wajen dubu biyar ne su ma sannan kuma zan sayi littafi da ake saye na karatu da na rubutu fa.”

“Humaira ke nan, ku ba kwa gane mene ne ke faruwa yanayin kasuwar yanzu ba kamar da bane. Ciniki ya yi baya sosai, shike nan zan kara miki dubu biyar.”

“Abba don Allah ka bani dubu bakwai kawai shike nan.”

“Ba ki da tausayi Humaira ga uwarki nan ba za ki tambaye ta ba sai ni kadai, ita ta cika miki dubu biyun mana ai tana da su.”

Humaira ta mayar da kallonta ga mummyn sannan ta ce, “Mummy dama ke ma kin ce za ki ba ni wani abin sai ki hada ki bani dubu biyar kawai.”

Mummy ta yi dariya tare da cewa, “Wa? Yaushe na yi miki alkawarin hakan, ke Humaira ki kiyaye ni da wannan kashe-kashen kudin naki fa. To wai mene ne za ki saya din haka?”

“Haba mummy na fada miki fa, kin manta ne har ki ka ce za ki ba ni.”

“To shike nan Allah ya kai mu goben lafiya.”

Nan take Humaira ta saki ranta har da dariya tana cewa, “Mummy, Abba na gode muku sosai, Allah ya saka da alkairi.”

Mummy ta ce, “Dubi ja’ira marar kunya, da kin bata rai kin yi fishi ko, sai yanzu za ki dariya saboda rashin ta ido ko.”

Sun dan jima sosai suna taba hira, daga karshe Humaira ta mike ta yi musu sallama ta nufi dakinta, ranta cike da farin ciki hade da annashuwa.

Washe gari da safe bayan sun gama karin kumallo, Humaira ta gyara gidan tsaf duk ta yi aikace-aikacen da ta saba yi ta yi su sannan ta shiga toilet ta yi wanka ta yi kwalliya. Bayan ta gama ta iske mummy a daki tana dan taba baccin hantsi, tashin ta ta yi da cewa, “Mummy mummy zan tafi, tashi ki ba ni kudin.”

Mummy ta farka tare da cewa, “Har kin shirya?”

“E wallahi ina son na je da wuri ko za a samu cinkoso kafin rana ta yi sosai na gama.”

Mikewa mummy ta yi ta bude loka ta dauko naira dubu ashirin da biyar (₦25,000) ta mikawa Humaira tare da cewa, “To ga su Allah ya taimaka ya kuma ba da sa’a, ki kula sosai kin ji.”

Ta karbi kudin ta ce, “To mummy insha zan kula kuma na gode.” Ta zuge zif din karamar jakarta ta-hannu (pause) ta saka kudin sannan ta ce, “To sai na dawo mummy.”

Ta fada tare da mikewa ta baro dakin mummy ta dawo dakinta, ta kwashe wayarta ta boye a dakin sannan ta fice daga gidan. Nan da nan ta nufo titi ta tari mai Adaidaita Sahu, sai unguwar su Anty Sakina kamar yadda suka yi alkawari da Usman cewa za ta je gidan yau din. Har daidai kofar gidan Mai Adaidaita ya kai ta, ta sallame shi ta fito da sauri ta shige ciki. Sallama ta yi da karfi kafin ta isa daf da kofar falon, Usman dake kwance kan kujera a falon idonsa biyu, lambarta ma yake ta faman laluba amma sai ji yake ana fada masa cewa a kashe take.

Amsa sallamar ya yi sannan ya ce, “Shigo mana ranki ya dade ke da gidanki sai kin tsaya wani neman izini.”

Ya fadi hakan ne saboda ya fahimci muryarta ce, bude labulen ta yi ta shiga yayin da shi kuma ya mike zaune ya ce, “Sannu da isowa, lafiya dai na ji wayarki  a kashe. Yanzu nake ta kokarin kiran ki sai na ji ta ki shiga.”

Cikin sigar murmushin jin kunya Humaira ta ce, “Wallahi matsala aka samu ne, jiya da rana bayan na duba sunana na hayo Adaidaita Sahu na manta wayar a ciki ban sani ba, kuma tun jiyan na yi ta kiran layin amma a kashe.”

“Ayya! Allah sarki, ai mafiya yawan masu Adaidaita Sahun nan ba su da amana, wasu ma har fata suke su dauko mutane su manta kayansu a ciki, shike nan sai su rike ba za su kai wajen hukuma ba ayi cigiya. Babu matsala za a mayar da wata insha Allah.”

Murmushi kawai Humaira take yi, ya ci gaba da cewa, “Ya gidan ya su mummy da Abba da fatan duk kowa lafiya.”

“Lafiyarsu kalau wallahi.”

“To ya yi kyau, me kike so a kawo miki ruwa ko lemo? Koda yake ma na daina kawo miki komai, nan gidanki ne duk abin da kike so ki je ki dauka da kanki.”

Murmushin ne dai har yanzu a fuskarta ta ce, “Hmm! Na gode ma ba na bukatar komai wallahi a koshe nake.”

“To shike nan ki cire hijabinki mana ki sha iska ko bakya jin zafi? Don Allah ki saki jikinki babu wata matsala. Humaira na dade ina son ki wallahi, ni da ma can ke nake so kawai dai Allah ya kaddara zan auri Sakina ne.”

Murmushi mai sauti Humaira ta yi sannan ta ce, “To sai dai ina dan yin sauri ne”

“Kada ki damu, nawa ne kudin registration din naki?”

“Hmm! Dubu goma sha-biyu ne.” Ta fada tare da mika masa takardar biyan kudin.

“To babu matsala, yanzu ya ya za ayi?” Ya fada tare da yin mika sannan ya ci gaba da cewa, “Ki dawo kan wannan kujerar mana.”

Babu musu ta mike ta koma kan kujerar da yake zaune, 3 seater ce ta zauna kusa da shi. Nan fa ya fara sumbatar ta yana tattabe ta. A nan kan kujerar suka yi romancing din juna, suka yi duk sha’anin da za su yi a nan falo, bai yarda sun shiga bedroom ba bare su hau kan gado, 3 seater din ta ishe su komai. Bayan sun gama duk abin da za su yi, ya kawo kudi naira dubu ashirin ya ba ta ya ce, “Ga kudin registration din.”

Ta karba, ya ci gaba da cewa, “Wayar kuma wace iri kike so?”

Kanta sunkuye ta ce, “Irin tawa ma ta da ta isa.”

“Okay, to nawa ake sayar da ita?”

“Ina jin ba za ta wuce dubu biyar ba.”

Ya kirgo dubu bakwai ya sake bata ya ce, “To ga shi ki saya har swapping din layin ma ki je ayi miki a yau.”

Ta karba tana masa godiya, “Na gode sosai Allah ya saka da alkairi.”

“Hmm! Ai kin cancanci abin da ya fi haka a wajena, babu abin da ba zan yi miki ba. Yadda kike faranta mini rai dole ne nima na saka miki da abin da zai saka ki farin ciki.”

Yana fada ya kama ta ta mike yana ci gaba sumbatar ta ya rungume ta a jikinsa, ita kuwa ta kwanta ta yi lif da ita tamkar mijinta na halak. Ya jima yana rungume da ita kamar kada su rabu, amma haka nan ya sake ta, ta saka hijabinta ta fice daga gidan. A unguwar akwai wata kawar Anty Sakina da ta ga fitowar Humaira daga gidan, sai ta ce a ranta “Lafiya kuwa yau Sakina ba ta fita aiki ba har ma ta yi bakuwa? Bari na leka na ji ko lafiya.”

Gidan ta shigo da sallama, Usman ya amsa tare da lekowa, matar ta gaishe shi, “Ina kwana ashe kana ciki ba ka fita ba. Ina Sakinar?”

Fuskarsa a daure ya ce, “Zainab ba ki san yau Talata bane da za ki zo neman Sakina yanzu a gida?”

“Au yi hakuri wallahi na sha’afa ne, ashe tana makaranta fa, to sai anjima.”

Fitowa ta yi ba tare da ta yi wani mummunan zato ba, abin da ta yi tunani kawai shine watakila wani sakon Anty Sakinar ta bari Humairan ta zo ta dauka, wannan ne zaton da ta yi.

To ita kuwa Humaira tana kawowa bakin titi ta tsaida Mai Adaidaita Sahu ta ce masa, “Jakara za ka kai ni nawa zan ba ka?”

Ya ce, “To ki ba da dari biyu.”

“To shike nan mu je zan ba ka naira dari biyu da hamsin (₦250), idan ma wacce zan je wajenta ta shirya sai ka kai mu Sharada UBA Bank.”

“Okay to babu matsala.” Ya ja mashin suka tafi, babu jimawa suka isa ta ce, “To za ka jira na duba idan ta gama shirin sai ka wuce da mu Sharadan?”

Mai Adaidaita Sahu ya ce, “E babu damuwa shiga ki duba.”

Tana shiga gidan da sallama ta iske Binta zaune ita da Kakarta suna hira, Humaira ta gaida Kakar sannan ta dubi Binta ta ce, “Mu tafi ko, tare da Mai Adaidaita Sahu muke yana waje yana jiranmu.”

Binta ta ce, “To shike nan bari na dauko hijabina.

Mikewa ta yi ta sako hijabi, Baba Abu ta ce, “To Allah ya kiyaye Allah ya ba da sa’a, ku kula sosai.”

Fitowa suka yi suka shiga Adaidaita Sahun ya ja suka kara gaba. Suna fara tafiya Humaira ta ce, “Amma ina ga ba zai yi yu ba duk a yau mu je bankin har mu isa makaranta ayi mana screening ko, lokaci zai iya kurewa.”

Binta ta amsa mata da cewa, “E gaskiya kam ba lallai bane, kila a samu layi a bankin tunda an ce dole sai a branch daya kowa zai biya kudin. To kin ga kowa zai fito ne ya ga ya kammala da wannan bangaren.”

“Babu damuwa idan ba mu samu dama a yau ba gobe ma shiga makarantar.”

“Haka ne, Allah ya kai mu goben lafiya.”

“Wai na ce yaushe za ki je ki ga gidanmu?”

Binta ta yi murmushi tare da cewa, “Hmm! Duk lokacin da kika ce mu je sai mu je ai.”

“To shike nan yau za ki ga gidanmu, koda mun gama da banki da wuri gidanmu za mu koma ki gani.”

“Shike nan babu damuwa.”

Hira suka yi ta yi har Mai Adaidaita Sahun ya kai su, Humaira ta ce, “To yanzu nawa zan ba ka kenan duka?”

Ya ce, “Kawai ki bayar hajiya.”

Humaira ta yi dariya tare da cewa, “Wace ce hajiyar, mai niyya dai. Ka fadi abin da zan ba ka, ku haka kuke sai ku ce wai mutum ya bayar kawai, to idan na ba ka abin da bai kai kudinka ba fa?”

Murmushi ya yi sannan ya ce, “To ki ba da naira dari takwas.”

Humaira ta zaro naira dubu daya ta mika masa tare da cewa, “To ga wannan mun gode. Na ji dadin tukinka da za mu same ka gobe da ka zo gida ka dauke mu.”

Ya karbi kudin ya ce, “Hajiya ni ma na gode sosai. To a wace unguwa kike? Ba sai na ba ki lambar wayata ba idan kin shirya ki yi mini waya na zo.”

“Ba a unguwa daya muke ba, ni a Zaitawa nake ita kuma Jakara take, Polytechnic za ka rika kai mu kullum, wa za ka fara daukowa kenan?”

“Okay to ni kuma a Tal’udu nake, wacce take a Jakara ita zan fara dauka sai na iso Zaitawa na dauke ki mu wuce ko, hakan zai fi.”

“To shike nan yanzu wayoyinmu mun saka a caji, rubuta mana lambar ta ka, idan ya so gobe kafin ta gama shiryawa za ta maka waya sai ka taho.”

Haka suka tsayar da magana da Mai Adaidaita Sahu a kan zai rika zuwa yana daukar su kullum, suka sallame shi ya wuce, su kuma suka shiga cikin UBA Bank Sharada.

<< Kuda Ba Ka Haram 9Kuda Ba Ka Haram 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×