Tuni wasu daliban sun fara zuwa sosai har an kafa layi. Binta cike take da mamakin Humaira, tambayoyi ne makil a ranta, daya kawai ta iya yi mata dangane da zuwan da Mai Adaidaita Sahu ya fara daukar ta sannan su wuce gidan su Humairan. Ta yaya hakan za ta kasance? Ita da ba waya ce da ita ba?
Murmushi Humaira ta yi sannan ta kada baki ta ce, “Kada ki damu wannan abu shi ya fi komai sauki, yanzu idan mun gama da nan za mu je a sayi layin waya sabo a yi miki register da sunanki idan. . .