Skip to content
Part 11 of 20 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Tuni wasu daliban sun fara zuwa sosai har an kafa layi. Binta cike take da mamakin Humaira, tambayoyi ne makil a ranta, daya kawai ta iya yi mata dangane da zuwan da Mai Adaidaita Sahu ya fara daukar ta sannan su wuce gidan su Humairan. Ta yaya hakan za ta kasance? Ita da ba waya ce da ita ba?

Murmushi Humaira ta yi sannan ta kada baki ta ce, “Kada ki damu wannan abu shi ya fi komai sauki, yanzu idan mun gama da nan za mu je a sayi layin waya sabo a yi miki register da sunanki idan mun koma gida zan ba ki wayata ki saka layin sai ki kira Mai Adaidaita Sahun ki yi masa bayani, ina fatan kin gane?”

“To shike nan babu damuwa.”

Layin su ma suka hau, bayan kamar mintuna arba’in (40 minutes) suka isa wajen me karbar kudi (cashier), suka biya kudin aka ba su Scratch Card, wanda da shine za su yi Online Registration su fitar da jadawalin darussan da za su karanta a wannan shekara ta farko. Fitowarsu keda wuya suka sake tare wani Mai Adaidaita Sahun, babu inda suka zame sai kasuwar sayar da wayoyi ta Beirut. A nan Humaira ta sayi sabuwar waya irin tata komai da komai sannan kuma suka sayi sabon layi wanda za a ba wa Binta kamar yadda ta yi alkawari. Daga nan kuma kai tsaye unguwar su Humaira suka yo wa tsinke, babu jimawa suka iso.

Suna shigowa cikin gidan, Mummy ce da kannen Humaira sun dawo daga makaranta suna cin abincin. Sallama Humaira ta yi Mummyn ta amsa tare da cewa, “Har kin dawo? Babu cinkoso ke nan?”

“E wallahi kuwa Mummy babu mutane sosai.”

Binta ta durkusa har kasa ta gai da Mummyn cikin ladabi da girmamawa, sannan suka wuce dakin Humairan. Daki ne madaidaici da ke dauke da gado da sif da lokoki, Humaira kadai ke kwana cikin dakin. Kana shiga za ka tabbatar da hakan domin a gyare yake da abubuwan kawata daki, kamshi ne kawai ke tashi. Shiga suka yi Humaira ta cire hijabinta ta fito kitchen ta zuba musu abinci ta koma suka ci sosai sannan suka huta.

Humaira ta mike ta dauko tsohuwar wayarta da ta boye kafin ta fita daga gidan, ta mikawa Binta ta ce, “Karbi wannan wayar ki saka layin nan a ciki ki ci gaba da amfani da ita.”

Cike da mamaki Binta ta zaro idanu tana duban Humaira, ta gaza magana. Wani dan gajeren tunani ta afka, a ranta take cewa, “Wai wannan mafarki nake ko kuwa a ido biyu nake? Ni ce da waya yau? Ba ma wannan ba, shin dama har yanzu ana samun kawaye irin wannan? Ba mu dade da haduwa ba amma sai kyautuka take mini haka?”

Wani bangare ke nan na tunanin da Binta take yi wanda ya tsananta shirun da ta yi, Humaira ce ta dakatar da shirun da cewa, “Ya ya dai lafiya na ga kin yi shiru kamar kina tunani? Ko ba kya karbar kyauta ne?”

Nisawa Binta ta yi hade da murmusawa sannan ta ce, “La! Kodaya wallahi, kawai na ma rasa da wadanne kalmomi zan yi miki godiya ne. Haduwarmu ba ta yi nisa ba amma kin fara sauya mini rayuwata, abubuwan da ban taba sa ran zan samu ba koda a mafarki amma ga shi ina samu a wajenki. Na gode sosai Allah ya saka da alkairi, Allah ya bar zumunci na gode matuka.”

Cikin murmushin martani Humaira ta ce, “Mene ne kuma abin yin godiyar, kada ki damu. Ita rayuwa haka take, duk yadda ta same ka haka za ka karbe ta kuma duk me rai baya fitar da rabo.”

“Ai kam godiya ta zama tilas, ban san ki ba fa, daga haduwa a makaranta ki ka biya mini kudin makarantar masu yawa, wanda ni har na hakura da yin karatun ma. Sannan kuma yanzu ga shi kin ba ni waya, saboda haka ya zama dole na gode miki, dan halak baya manta alkairi. Na gode, Allah ya saka miki da mafificin alkairi.”

“Hmm! To amin, ki saka layin mu gwada yin kira mu ga ko register ta yi.”

Binta ta bude wayar ta cire batir sannan ta saka layin, ita ma Humairan fito da sabuwar wayar ta yi ta saka layinta ta hada komai sannan ta kunna ta. Nan dai suka gwada yin kira dukkan wayoyin babu wata matsala. Sun jima sosai suna hutawa, sai kusan la’asar sannan Binta ta yunkura tare da cewa, “Zan wuce.”

Humaira ta ce, “Har tafiya za ki yi, ba za ki dan kara hutawa ba?”

Murmushi Binta ta saki tare da cewa, “Ai na ga yamma ta fara yi ne shiyasa ko za ki yi aiki ko?”

“To shike nan babu damuwa, bari mu je na raka ki titi.”

Hijabansu suka saka suka fito falo, Humaira ta dubi Mummy ta ce, “Bari na raka ta za ta tafi.”

Mummy ta ce, “To madalla ki gaida manyan Allah ya yi albarka.”

Suna fitowa daga lungun suka tari Mai Adaidaita Sahu Humaira ta ce, “Jakara za ka kai ta.”

Mai Adaidaita Sahu ya amsa da cewa, “To babu matsala ta shigo mu tafi.”

Binta ta dubi Humaira ta ce, “To shike nan na gode sosai Allah ya bar zumunci.”

“Hmm! Ba komai karbi wannan ki biya shi kudin idan ya kai ki, za muyi waya anjima da dare.” Naira dari biyar (₦500) ta mika mata amma sai ta ki karba saboda kunya da nauyinta da take ji.

Bata rai Humairan ta yi tare da cewa, “Ba na son haka kin ji, ai na ga ba tambayata kika yi ba, ko kin rena ne?”

Murmushi Binta ta yi tare da karbar kudin sannan ta ce, “ Na gode.”

“To a sauka lafiya.” Mai Adaidaita Sahu ya ja suka tafi yayin da Humaira kuma ta juyo ta koma gida.

Ita kuwa Binta tun shigar ta Adaidaita Sahun ta sake tsundumawa cikin kogin tunani game da hidimomin da Humaira take mata. Ga shi dai ta ga gidan nasu ba wasu masu karfi bane sosai, rufin asiri ne kawai. To abin da ya tsaya mata a rai shine yadda ta ga kudade a hannun Humairan sosai da yadda ba ta jin kyashin kashe su. Dukkan wadannan abubuwan mamakin da suka baibaye mata zuciya tana bukatar karin haske dangane da su, to sai dai samun hakan na da matukar wahala, wai ‘Zaman akuya a dakin kura.’

Humairan ce kadai ke da amsoshin wadannan tambayoyin, wanda kuma da wuya Binta ta iya buda baki ta tambaye ta  game da yadda abin yake. Tana tsaka da wannan tunani Mai Adaidaita Sahu ya isa da ita gida, ta sallame shi ta shige gida. Kwance ta iske Kakarta tana hutawa, sallama ta yi kaka ta amsa tare da cewa, “Sai yanzu ki ka dawo? Sannu lallai an sha rana.”

“Yawwa, amma da wuri muka gama da banki, mun je gidan su kawata ne.”

“To madalla, ga abincinki can ki dauko.”

“Hmm! Baba kenan, ni na koshi na ci abinci a gidan su kawar tawa. Ba ma wannan ba tukunna, albishirinki?”

“Goro, me kuma ya faru?”

“Abban kawata ya biya mana kudin makaranta tare da ni, gobe za mu je makaranta ayi mana tantancewa ta karshe kuma kin ga ta ba ni wayarta ita ta sayi sabuwa.”

“Kai don Allah! Masha Allah, Ubangiji Allah ya saka musu da alkairi.”

“Amin ya Allah, wallahi Baba ni dai da har na hakura da yin karatun tunda na ji an ce sai an biya dubunnan kudade, amma kin ga ikon Allah ya hada ni da ‘yar arziki.”

“Haka ne, ai dama haka abin Allah yake. Shi bawa ba ya taba yanke kauna da samu, duk wanda zai tashi ya nema a wajen Allah, to babu shi babu rashi sai dai jinkiri.”

“Tabbas haka ne Baba, kuma kin ga ita za ta rika biya mana kudin mota kullun. Wani Mai Adaidaita Sahu ta dauka zai rika zuwa nan yana dauka ta sai ya biya ta gidansu daga can sai ya kai mu makarantar.”

“Alhamdulillah! Haka ake so, Allah ya ba da sa’a, sai ku mayar da hankali ku yi karatu sosai. Babu ruwanku da kula samari shashashai, ku yi abin da ya kai ku akan lokaci ku gama. Ku mata ne rayuwarku gajeren zango ne da ita, don haka ku yi kokari ku mori kuruciyarku da karfinki kafin girma ya riske ku.”

“To Baba Insha Allahu za mu kiyaye.”

Bayan Isha misalin karfe 9:00pm Humaira ta kira Binta, kamar yadda ta yi alkawari, hira suka sha a wayar sosai. A nan Binta ta kara yi wa Humaira godiya har ta yi amfani da damar wajen isar da sakon godiyar Baba Abu. To wannan kenan.

                  ***         ***         ***

A bangaren Anty Sakina kuwa har yanzu dai zaman doya da manja ne tsakaninta da Usman, dangantaka ba ta saitu ba domin bai sauya halinsa ba. Abin na sa ma tamkar wanda aka sa wa hannu ko kuma me bakin uwa, kullum lalatarsa gaba take kamar wutar daji. Washe gari safiyar Laraba ce wato ranar aiki ce, Anty Sakina ta shirya ta fita, shi kuwa dama sai rana yake fita. Misalin karfe tara na safen (9:00am) ya kira Humaira, lokacin ta shirya tsaf! Tana jiran zuwan Mai Adaidaita Sahu da Binta kamar yadda suka tsara.

Daga kiran nasa ta yi bayan sun gaisa ya ce, “Da ma na kira ne na ji kin dora layin?”

“E wallahi na saka ka gan shi tun jiya da dare ma, ya yi sosai na gode Allah ya saka da alkairi.”

Murmushi ya yi tare da cewa, “Haba mene ne abin godiya kuma ai mun zama daya. Tsakanina da ke babu godiya, duk abin da kike bukata kawai ki sanar da ni. Ya ya registration din kin yi?”

“E na karbi Scratch Card din, ka ga yanzu haka ma na shirya zan je makaranta a yi mini Online Registration a fitar mini da Semester Form.”

“To Masha Allah, Allah ya taimaka. Yanzu ya ake ciki, akwai wata matsala ne?”

“Hmm! Ba komai wallahi.”

“Idan akwai ki fada mini kin ji.”

“Allah babu komai idan akwai zan fada maka.”

“To shike nan ya yi kyau. Na ce ko zamu iya haduwa a weekend idan kina da lokaci?”

Cikin fargaba ta ce, “A weekend kuma! To a ina ke nan?”

Murmushi ya yi sannan ya ce, “Kwantar da hankalinki ba a gida ba, ina nufin koda a hotel ne.”

“Okay to ba damuwa zan duba na gani.”

“Idan kin ga babu lokaci ki bari kawai ko ranar Monday ne sai ki zo gida ko?”

“A’a ba komai Allah ya kai mu weekend din.”

Suna gama wayar mintuna ba su wuce biyar ba Binta ta kira ta, ganin kiran ya tabbatar mata sun karaso ne. Mikewa ta yi ta saka hijabinta sannan ta yi wa Mummy sallama ta fito. Kai tsaye ta shiga Adaidaita Sahu suka tafi ba tare da bata lokaci ba. Fara tafiyarsu keda wuya suka fara hira bayan sun gaisa. Humaira ta ce, “Gaskiya kin shirya da wuri, ai ban yi zaton za ku karaso yanzu ba.”

“Hmm! Ai kam dai kin gan mu, zuwa da wurin zai fi, idan muka gama da duk tsarabe-tsaraben sa-hannu da sauransu sati me kamawa karatu kawai za a fara.”

“Hakane kuma fa, to Allah dai ya ba mu sa’a.”

“Amin kuma Allah ya saka miki da alkairi, Allah ya…”

Humaira ta yi sauri ta rufe mata baki da tafin hannu tare da cewa, “To ya isa haka komai ya wuce.”

Wata hirar suka kama suna yi har Mai Adaidaita Sahu ya isa har cikin makarantar suka sallame shi sannan suka karasa bangaren masu aikin computer na makarantar da ake kira village. Wata ‘yar kasuwa ce da ta hada masu aiki da na’urar computer da suke yi wa dalibai aikace-aikace kamar yin Online Registration, Assignment, Typing na Projects, daukar hoton gaggawa (One Minute Passport) da sauransu. Haka nan akwai rumfunan masu sayar da littattafai da takardu da alkaluma da dai sauran kayan koyo da koyarwa. Baya ga wadannan akwai masu sayar da abinci kala-kala me tsada da kuma me rahusa, ma’ana daidai kudinka daiadai shagalinka. Kazalika akwai sashen sayar da abinci mallakar hukumar makaranta da ake kira da Cafeteria.

Su Humaira na isa suka hangi wata ‘yar matsakaiciyar kwantaina an rubuta, SK INTERNET CAFE. Kai tsaye suka nufi gindin kwantainar, cike take fal! Da mutane ana ta hada-hada, sallama suka yi tare da cewa, “Don Allah Online Registration za ayi mana.”

Wata budurwa ce da ke can cikin kwantainar tana kan wata makekiyar computer tana aiki ta amsa musu cikin sakin fuska da cewa, “To sannunku da zuwa, amma za ku dan yi hakuri kadan a sallami wasu ga kujera ku zauna ku dan jira ko.”

Binta ta amsa da cewa, “To mun gode babu damuwa bari mu jira din.”

<< Kuda Ba Ka Haram 10Kuda Ba Ka Haram 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×