Binta ta ce: “Kin ganni nan kofar gidanku na zo wajenki yanzu mummy ta ce wai kema kin tafi gidanmu.”
Cikin rawar baki da kame-kame Humaira ta ce: “E e a e hakane, amma da na zo ban same ki ba sai... Sai na tafi gidan su wata kawata.”
“Okay, to ba komai ina ne gidan sai na zo mu hadu a nan din ko?”
Humaira ta sauke wani irin numfashi me cike da firgici sannan ta ce: “Aa ki bari kawai ba sai kin zo ba, gobe Lahadi zamu hadu kawai.”
“Lafiya dai na ji kamar kina yin. . .