Misalin karfe 5:30pm na yammaci ranar, Anty Sakina ta shirya za ta koma gida, wasu kudade ta dauko cikin jakarta ta ba wa Mummy, sannan shi ma Abbansu ta bayar aka ajiye masa hade da sakon gaisuwa dayake lokacin da ta zo ya riga ya fice kasuwa, kuma lokacin dawowarsa bai yi ba. Humaira na can dakinta ta ki fitowa bare ta raka Antyn ta ta kamar yadda ta saba, har sai da Mummy ta aika aka fada mata cewa, ta zo ta raka Anty Sakina za ta tafi. Alatilas ta fito, ganin yanayinta kamar ba ta so yasa. . .