To, a bangaren Anty Sakina kuwa, ta gaza magana. Kuka kawai take marar sauti, Mummy ta sake tambayar ta, "Sakina wai lafiyarki kuwa? Me ke faruwa ne ina ta magana kin ki ba ni amsa, sai kuka kike yi kamar wata karamar yarinya."
Cikin yanayin kukan ta ce, "Mummy Humaira, me na yi..." Sai kukan ya ci karfinta, maganar ta gagara fitowa.
"Humaira kuma, me ya samu Humairar? Hatsari ta yi ne?" Mummy ta fada cikin sigar zakuwa da jin halin da Humairar take ciki.
Anty Sakina ta karfafa muryarta ta ce, "Ita da Usman na gani a gida yanzu. . .