Wani sashen na zuciyar Anty Sakina sai sake-saken abubuwa da dama take yi, “mace Usman ya kawo mini cikin ɗaki? Iskancin ya wuce ya neme su a can waje sai ya dauko su har cikin gidana? Wannan wace irin ƙaddara ce take samu na?”
Ire-iren tunane-tunanen da take yi ke nan, ta jima sosai a zaune a wajen. Gabaɗaya ta rasa me ke mata dadi, sai kusan la'asar ta mike ta yi alwala ta gabatar da sallah sannan ta shiga kicin ta fara shirya kayan buɗa-baki. Bayan ta gama kuma ta ɗora abincin. . .