Skip to content
Part 8 of 30 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Wani sashen na zuciyar Anty Sakina sai sake-saken abubuwa da dama take yi, “mace Usman ya kawo mini cikin ɗaki? Iskancin ya wuce ya neme su a can waje sai ya dauko su har cikin gidana? Wannan wace irin ƙaddara ce take samu na?”

Ire-iren tunane-tunanen da take yi ke nan, ta jima sosai a zaune a wajen. Gabaɗaya ta rasa me ke mata dadi, sai kusan la’asar ta mike ta yi alwala ta gabatar da sallah sannan ta shiga kicin ta fara shirya kayan buɗa-baki. Bayan ta gama kuma ta ɗora abincin gida gabaɗaya. Ana kiran sallar magariba ta yi sallah ta zo ta zauna gaban kayan shan ruwan, sai ta ji sam ba ta sha’awar komai. Tsananin baƙinciki da tunanin da ke ranta sun hana ta jin yunwa, abincin ta zuba wa ido kawai tana kallo amma zuciyarta sam ba ta wajen.

Sallamar Usman ce ta katse mata zuzzurfan tunanin da ta nutsa, amsa masa ta yi fuskarta a murtuke tamkar ba ta taɓa sanin wani abu ba wai shi farinciki. Ɗaki ya fara wucewa ya sauya kayan da ke jikinsa sannan ya dawo falon. Zama ya yi bisa kujera ya dube ta, ta saka abinci a gaba. Nisawa ya yi tare da gyara zama sannan ya ce, “Ya ya dai lafiya kuwa?”

Shiru ta yi ba ta tanka masa ba, ya ci gaba da cewa, “Me ke damun ki ne, ko ba ki da lafiya ne na ga alamar kamar ma ba ki ci komai ba.”

Shirun dai ta yi ba ta ce komai ba, ko duban inda ya zauna ma ba ta yi. “Wai me ke faruwa ne kin ƙi magana, kuma na tambaye ki ko ba ki da lafiya duk kin yi shiru. Ya kamata idan wani abu ne yake damun ki ki faɗa mana, amma yin shiru da ɓata rai ba zai taɓa yin magani ba.”

Wata rarraunar ajiyar zuciya Anty Sakina ta sauke sannan ta ce, “Usman me na rage da shi? Me ka nema ka rasa a tare da ni? Mene ne kake buƙata wanda ba na yi maka shi a cikin gidan nan? Yanzu abin da kake yi a can wajen yawon daren bai isa ba sai ka ɗauko karuwa ka kawo min ita har cikin ɗakina a kan gadona na sunna? Usman ba zan taɓa yafe maka ba, kuma in sha Allahu sai Allah ya saka mini. Da yardar Allah sai ka ga sakayyar da Allah zai mini, na yi haƙuri da duk abin da za ka aikata a waje, a gabana za ka riƙa yin waya da karuwan da kake mu’amala da su tun ina nuna damuwa a kan hakan na gaji na haƙura na kau da kai, shi ne abin bai ishe ka ba sai ka keta mini haddi ta hanyar kawo mace ka yi zina da ita a ɗakina, wallahi ba zan yafe maka ba.”

A fusace ya yunƙura kamar zai kai mata duka ya ce, “Ke dakata da Allah, waɗanne irin zantukan banza ne kike faɗa mini haka. Me kike nufi ne, wace mace na kawo miki? Kin daɗe kina mini irin wannan zargin fa! To bari ki ji ya ishe ki haka idan kika sake mini irin wannan zan ɗauki tsattsauran mataki muddin ba ki daina ba. Banza shashasha.”

Mikewa ta yi tsaye da zafinta tamkar za a dambace tana huci zuciyarta na mata ƙuna ta ce, “Kar ka raina wa kanka hankali, zargi nake maka a da can amma yanzu zargina ya tabbata ina da hujja babba idan ƙarya na yi maka ka zo ka gani, na amince idan sharri na yi maka ka yi mini Allah ya isa kamar yadda na yi maka.”

Tana faɗa ta nufi uwar ɗaki tana cewa, “Ka zo mana ka gani sai ka tabbatar ba zargi ba ne gaskiya ce, Allah ne ya tona maka asiri.”

Cikin ɗakin ya bi ta, ta nuna masa shimfiɗar gadon ta ce, “Me ya kawo wannan, ko da ma a haka na bar shi?”

Saboda tsananin rashin ta ido a tattare da Usman sai ya ce, “To mene ne hakan? kwanciya na yi ne kafin na fita, ko da ma ba don a kwanta ba aka kawo miki gadon ba?”

Wani irin murmushi mai cike da takaici ta yi tare da ɗaukar zanen gadon tana nuna masa wajen da sperm ɗin ya zuba ta ce, “Wannan ma duk a kwanciyar ne ka zubar da shi ko?”

Fusata ya sake yi tare da cewa, “Ke ya ishe ki haka, idan kuma kin ƙi ji ba za ki ƙi gani ba, ya ya za ki titsiye ni kina tuhuma ta kamar wani ɗan cikinki. Idan ba ki san waye ni ba zan nuna miki zahirin halina, ki tsaya a matsayinki ki daina shigar mini rayuwa.”

Yana ƙare zancen ya juyo ya komo falo ya zauna yana huci kamar wani bijimin sa. Ita kuwa Anty Sakina zama ta yi a ƙasa zuciyarta kamar za ta fita saboda tsananin baƙinciki. Ta rasa wane irin miji ne Allah ya haɗa ta da shi, a ranta take cewa, “Wannan ita ce tawa kaddarar kuma, Duk waɗannan miyagun halaye na rashin mutunci da rashin kunya da keta alfarmar aurensu da Usman ɗin yake yi mata, ba ta taɓa kai karar sa wajen kowa ba, sawa’un wajen iyayensa ko kuma wajen nata iyayen. Babu shakka abin yana matuƙar ci mata tuwo a ƙwarya, idan da a ce za ta faɗa wa wani ƙila ta samu sauƙin tuƙuƙin da ranta yake mata. To amma sam ba ta da sha’awar fitar da sirrin da ke tsakaninta da mijinta, mutum ɗaya ne take ɗan faɗa masa damuwarta. Shi ɗin ma ba komai take faɗa masa ba. Idan suna hira ne a wajen aiki ta riƙa tsokanarsa da cewa, “Ai ku maza ba ku da tabbas, duk yadda ake kyautata muku ba kwa gani ba kwa yabawa, sai kun ƙure mutum duk haƙurinsa.”

To bayan Usman ya koma falo, jim kaɗan ya miƙe ya nufi kicin ya ɗauko abincinsa da kansa domin ya san yadda suka yi hayaniyar nan da wahala ta sake bi ta kansa. Yana gama cin abincin ya yi wanka ya fice abinsa.

Anty Sakina na can uwar ɗaki zaune ta haɗa kai da gwiwa, daina jin motsi a falon ya tabbatar mata ya fita daga gidan. Falon ta dawo ta sake zubewa yunwa ta fara kama ta sosai domin tunda ta kai azumi babu abin da ta saka a bakinta, gudun kada yunwa ta yi mata illa ya sa alatilas ta riƙa tura abincin da kyar ta samu ta ɗan ci wanda za ta iya ci ta bar sauran. Tana gamawa ta miƙe ta yi alwala ta yi sallar Isha, ta jima sosai goshinta na ƙasa a sujjadar ƙarshe tana roƙon mahallicin kowa da komai da ya kawo mata mafita, ya kuma ba ta juriya da haƙuri bisa wannan jarabta da ya yi mata.

Tana nan zaune bisa sallaya ta fara gyangyaɗi, sai ta kishingiɗa har barci ya ɗauke ta. Sai ƙarfe ɗaya na dare Usman ya dawo, ya iske ta kwance kan sallaya a ƙasa, ko kallon arziki ba ta ishe shi ba, ya wuce ɗaki ya yi kwanciyarsa. Sai asuba Anty Sakina ta farka, sallah ta yi sannan ta ɗauki Al-Ƙur’ani mai girma ta ɗan taɓa karatu kamar yadda ta saba yi. Misalin ƙarfe 6:30am na safe ta shiga kicin ta haɗa abincin karin kumallo, shayi kawai ta ɗan kurɓa ta zuba abinci a flas ta tafi da shi wajen aiki. Har lokacin fitarta ya yi Usman bai tashi daga barci ba ita kuma ba ta tashe shi ba. Sai misalin ƙarfe tara 9:00am sannan ya tashi ya shiga bayi ya yi brush ya ɗauro alwala ya yi sallar asuba da rana tsaka koda yake da ma sabonsa ke nan. Bayan ya gama sallar kicin ya nufa bai tsammanin zai samu abinci ba, girkawa ya yi niyyar yi, amma sai ya tarar ta ajiye masa, ɗaukowa ya yi ya komo falo yana ci.

Anty Sakina kuwa da ke can makaranta wajen aiki da kyar ta iya shiga ajujuwa guda biyu, damuwa ce ta dabaibaye mata zuciya haɗe da ciwon kai, abin nan ne ya tsaye mata a rai. Kallon abin take a idonta, ta gaza ture shi a ranta. Zaune take a ofishin malamai ta kifa kanta bisa tebur, yanayinta kawai mutum zai duba ya fahimci tana cikin damuwa ko kuma rashin lafiya.

Anty Zara’u ce ta fito daga aji ta iske ta cikin wannan yanayi, tambayarta ta yi, “Lafiya kike kuwa?”

Anty Sakina ta ɗago kai idanunta jajir ta sauke wata nannauyayan ajiyar zuciya guda biyu a jere sannan ta ce, “Wai da ma haka wasu mazan suke Anty Zara’u? Allah ya jarabce ni da wani irin miji me halin ɗan akuya. Anty Zara’u rashin kunyar Usman ta wuce tunanin duk wani mai tunani, tanbaɗarsa nema take ta wuce gona da iri, cin mutuncin nasa ya wuce a can waje har cikin gida yake kawo min karuwai.”

Tana ƙare maganar wani marayan hawaye ya wanke mata kunci, cikin sigar tausayawa da rarrashi Anty Zara’u ta ce, “Subhanallah! Usman ɗin ne da kansa yake wannan mummunan aiki. INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHIR RAJI’UN. ALLAHUMMAJ AJURNI FI MUSIBATI WAKHLIFLI KHAIRAN MINHA. Kai kai! Abin ba daɗi gaskiya, Usman ya ɓata wayonsa.”

“Hmm! Anty Zara’u da ma can Usman ba mutumin ƙwarai ba ne, umarnin Abba na bi na aure shi. Amma sam Usman ba ɗan arziki ba ne.”

“Mtsww! Amma gaskiya Usman ya ba ni mamaki, wannan ba ɗabi’ar arziki ba ce, neman matan banza aiki ne na jahilai da mararsa amfani da ilimin da Allah ya ba su. Neman mata ɓata wa mutum rayuwa yake da tarihi, ko mutum ya daina abin yana nan a zukatan mutane suna kallon sa da shi. Ki yi haƙuri kin ji babu shakka wannan jarabta ce amma Allah zai ba ki sakammakon haƙurin.”

“Anty Zara’u Usman so yake ya kashe ni da ƙuruciyata, baƙincikinsa ne zai haifar mini da ciwon zuciya ko hawan jini, ki ba ni shawara don Allah.”

Tana faɗa wani kuka mai tsananin taɓa zuciya ya kufce mata, Anty Zara’u ta ɗan rungume ta tana rarrashinta tare da cewa, “Ki yi haƙuri ki daina kukan, haƙuri shi ne abin da za ki yi babu shakka Allah yana tare da mai hakuri kuma tabbas zai kawo miki mafita. Idan ma kika ce za ki kai ƙarar sa wajen manya ba lallai ba ne hakan ya yi magani sai ki tona wa kanki asiri kawai, idan kuma kika faɗa wa iyayensa ƙarshe ki yi baƙin jini su tsane ki, ki ci gaba da haƙuri kawai idan kin yi sallah kina faɗa wa Ubangiji. Ita rayuwa haka take kowa da irin jarabawar da Allah yake ɗora masa, haƙuri da juriya kuma su ne sinadaran da suke taimakawa wajen cin jarrabawar .”

“Haka ne na gode sosai Allah ya saka da alkairi.”

Shiru suka yi kamar mintuna biyar ba wanda ya sake cewa komai, Anty Sakina ta ce, “Ga abinci mu ci.”

Nan ta buɗe flas ɗin abincin da ta tafi da shi suka fara ci  suna cikin cin abincin Malam Sadik ya zo wucewa ya hango su ta taga ya ce, “Ko bisimillah babu, kowa ya ci shi kadai, an ce shi kaɗai zai…”

Ɗago kai suka yi a tare Anty Zara’u ta ce, “Bisimillah zo ka ci mana.”

“Sai da na roƙa, ku ci abincinku na gode. Na ga mutuniyar ko magana ta gaza yi duk dadlɗin girkin ne haka, a ci dai hankali”

Anty Zara’u ta yi dariya sannan ta ce, “Tana jin ka dai.”

“To ai shike nan tunda ta ƙi magana, gaskiya maigida ya iya girki. Bari a kawo muku lemo ko?”

“Ai ko da ka kyauta wallahi.” Anty Zara’u ta faɗa yayin da Malam Sadik ya kira wata ɗaliba ya aika ta ta sayo musu lemo.

Daf da lokacin tashi Anty Sakina da Anty Zara’u suka fito, ba sa tsayawa sai an buga karantawar tashi saboda cinkoson yara ɗalibai sai ƙura ta turnuƙe makarantar. Fitowarsu daga staffroom daidai lokacin Malam Sadik ya fito daga wani aji, “Har tafiya za ku yi, ba kwa jiran lokaci ya cika ko, za mu ba ku query form fa.” Ya faɗa cikin sigar tsokana.

Anty Zara’u ta ce, “Ai mun riga mun gama aikinmu na yau officially, ba dole ba ne sai mun jira har lokacin tashi ya yi ba. Su ma masu ba da queryn tafiyarsu suke a duk lokacin da ransu ya so, zuwa aikin ma sai sun gadama.”

“Hmm! Lallai Zara’u ba ki da dama. Wai ni me ke damun mutuniyar ne ta yi shiru kamar kurma, duk yau na lura kamar wani abu na damunki.”

Murmushi Anty Sakina ta yi ba ta ce masa komai ba, Anty Zara’u ta ce,“Halinku ne mana na rashin tausayawa, duk abin da ake muku ba kwa gani sai kun ƙure haƙurin mutum.”

Murmushi ya yi sannan ya ce, “Haka ne abin dai sai haƙuri, a riƙa kai zuciya nesa komai yana da lokaci.”

Anty Sakina ta nisa tare da cewa, “Haka dai kuke cewa haƙuri haƙuri amma wasu mazan ba su san ana haƙuri da su ba. Idan ma suka fahimci mutum yana haƙuri sun fi yin abin da suka gadama. ”

“Babu shakka akwai masu irin wannan hali to amma idan aka rabu da su aka daina damuwa da abin da suke yi shike nan sai su je can su ƙarata. Haƙuri za ki yi ki daina nuna damuwarki a gabansa, ko ma ba a gabansa ba ki daina ajiye damuwa a ranki. Tunani ba shi da amfani, zai iya haifar miki da wani ciwon, ki yi haƙuri kin ji shi ne abin da za mu faɗa miki.”

“Shike nan duk ranar da haƙuri ya kashe ni za ku fahimci ni.”

Cikin murmushi ya ce, “Ki daina faɗin haka mana, insha Allah za ki samu mafita. Allah yana tare da ke, ki ci gaba da addu’a mu ma muna taya ki duk lokacin da mu ka yi sallah.”

“To shike nan na gode sosai Allah ya bar zumunci bari mu wuce sai gobe. Anty Zara’u mu tafi ko.”

“To ku gaida gida.” Malam Sadik ya faɗa sannan ya wuce ofis ɗinsa. Su kuma suka nufi gate ɗin makarantar suka fice.

<< Ƙuda Ba Ka Haram 7Kuda Ba Ka Haram 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.