A cikin dokar dajin da baka jin komai face kukan tsuntsaye sai kuma sautin mummunar muryar bokan cikin amo marar daɗin saurare. Bayan ya gama sambatunsa ya dube su ɗaya bayan ɗaya da jajayen idanunsa kamar garwashin wuta kana ya fashe da wata irin mahaukaciyar dariya.Sai da ya yi mai isar sa sannan ya saurara yana muzurai ya ce da su, "Na san cewa sakaci da tsabar mantuwa ne irin naku ya sa kuka manta makarin sihirin da na faɗa muku tun farko, cewar; da zarar yaron nan ya warke ɗaya daga cikin ku ne zai kwanta. . .
Yes