Skip to content
Part 2 of 8 in the Series Kudi Ko Rai by Mustapha Abbas

A cikin dokar dajin da baka jin komai face kukan tsuntsaye sai kuma sautin mummunar muryar bokan cikin amo marar daɗin saurare. Bayan ya gama sambatunsa ya dube su ɗaya bayan ɗaya da jajayen idanunsa kamar garwashin wuta kana ya fashe da wata irin mahaukaciyar dariya.
Sai da ya yi mai isar sa sannan ya saurara yana muzurai ya ce da su, “Na san cewa sakaci da tsabar mantuwa ne irin naku ya sa kuka manta makarin sihirin da na faɗa muku tun farko, cewar; da zarar yaron nan ya warke ɗaya daga cikin ku ne zai kwanta a madadinsa, abinda dukkan mu ba mu sani ba shine, wanene daga cikin ku zai kamu da ciwon?”

Nan take gumi ya fara karyo musu duk da sassanyar iskar dake kaɗa ganyayyakin bishiyar da suke zaune a ƙarƙashinta. Tsayin wasu ‘yan mintuna babu wanda ya iya cewa komai sai boka Ƙazurgu da ke ta sambatunsa.

Habib ne ya kawar da shirun, “To yanzu ranka ya daɗe meye mafita?”

“Mafita ɗaya ce.” Cewar bokan yana zare idanu, “A kawar da shi gaba ɗaya kamar yadda Hajiya ta nema tun farko ku ka ƙi bata goyon baya.”

Idan ka ɗauke Suraj, su biyun nan shawarar boka Ƙazurgu ta gama samun karɓuwa a zuƙatan su. Matuƙar Alhaji zai ci gaba da ɓarnatar da dukiya wajen neman lafiyar Mashkur, babu amfanin Mashkur ɗin ya ci gaba da rayuwa a haka, cikin biyu dole a yi ɗaya, ko dai ya warke ɗayan su ya kwanta ko kuma ya mutu kowa ya huta.

Sun ɗauki tsawon lokaci suna tattataunawa a junansu ba tare da sun samu wata ƙwaƙƙwarar mafita ba, don haka suka yanke shawarar komawa gida su yi tunani a kan mafitar da Zinatu ta kawo. Wannan shawarar Suraj ce, don shi bai taɓa jin yana so a kashe ɗan ɗan uwansa ba.

A falon Zinatun dai suka sake yada zango don sake tattaunawa, zuciyar Suraj cike da saƙe-saƙe ya dubi Zinatu cikin ƙarfin hali ya ce da ita, “Me ye abin yi yanzu Aunty?” Ta numfasa, “Ai ni na gama magana, na faɗa muku abinda ya dace a yi tun farko, ka tsaya wasa da damarka Suraj, a wasu lokutan sai in ga kamar ba ka san ciwon kanka ba, har yanzu ka kasa gane matsayinka a wajen Alhaji, ka gaza fahimtar shi fa ba a matsayin ɗan uwa yake kallonka ba, ya fi so ka kare rayuwarka kana bauta masa, na ga alama kai ma hakan ka ke so.”

Habib ya taso daga kujerar da yake zaune ya dawo kusa da Suraj ya zauna tare da dafa kafaɗarsa, a nutse ya fara yi masa magana alamun yana so maganar ta shige shi sosai, “Abokina baka buƙatar dogon tunani a kan wannan maganar, yadda muka fara komai tare ka bari mu ƙarasa.” Ya ɗan yi shiru kana ya ci gaba, “Ka fahimci cewa Aunty Zinatu gaskiya take faɗa maka, ita mai ƙaunarka ce, dalilin kenan da ya sa take so ta ga ka ‘yanta kanka daga bautar da ka ke a gidan nan kaima ka zama wani abu a rayuwa.”

Sai da ya goge ɗigon ƙwallar da ke ƙoƙarin suɓutowa daga idanunsa sannan ya ce, “Habib ɗari bisa ɗari na yarda aninda Aunty Zinatu ta faɗa game da yadda Alhaji ya yi watsi da ni, shi da ɗansa suke ninƙaya cikin dukiyar da na yi imanin ba za a rasa kaso na a ciki ba.

Sai dai abinda nake so ka fahimta ita fa Aunty Zinatu so take na sa hannu a kashe Mashkur tare da ni, abu ne wanda ba zai yiyu ba, ba zan taɓa iyawa ba har abada, Mashkur tamkar ɗana ne na jini, kai ko babu alaƙar komi tsakaninmu ba na jin zan iya aikata kisan kai, na nemi tsari da hakan.”

A fakaice Zinatu ta wurga masa wani mugun kallo mai ɗauke da harara, ji take tamkar ta tashi ta rufe shi da duka don haushi, sai kuma ta yi ƙoƙarin dai-daita nutsuwarta, cikin kwantar da murya ta ce, “Suraj ya kamata ka dawo cikin hayyacinka ka fahimci me nake nufi da kai, ni fa ina son ɗora ka hanyar da za ka bi ka amfani rayuwarka ne, bautar da ka ke a ƙarƙashin Alhaji ta isa haka, kai da kanka ka yi tunani matsayinka a wajensa sa da irin dangantakar da ke tsakaninku ka fi ƙarfin ka ƙare a direban ɗansa.”

Tamkar ta yarfa masa tafasashshen ruwan zafi, zuciyar sa tana suya. Har kullum yana jin takaicin abin nan a ran sa wai shine direban Mashkur, tsawon lokaci wannan ke sa ya ji gaba ɗaya ya tsani rayuwarsa.

Cikin kwantar da murya Zinatu ta ci gaba da amfani da damar da ta samu a ɗan lokacin tana cusa masa mummunar aƙida kan Alhaji da ɗansa, sai dai abu guda da ya gaza yin tasiri a kansa har yanzu shine yadda zai yarda a ɗauke ran Mashkur tare da shi.

“Tunda boka ya ce ba zai yi yu a kawar da shi da asiri ba, sannan ba za mu iya samun shiga inda yake ba sakamakon matakan tsaron dake kula da shi a aaibiti, gashi Alhaji ya ƙi amincewa kowa ya zauna tare da shi, Suraj kawai ka bamu haɗin kai, ka bar komai a hannunmu ni da Habib ka koma gefe ka ga jira yadda lamarin zai kasance.”

Ya isa Zinatu.” Suraj ya tari numfashinta da rarraunar muryarsa, kana ya ci gaba, “Yanzu bana buƙatar jin waɗannan kalaman don Allah, ni fa kawai ina son mallakar wani kaso ne daga dukiyar Alhaji, ina son ‘yanta kaina a gidan nan, amma ba ta wannan hanyar ba.”
“To ta wacce hanya Suraj? Zinatu ta buƙata a fusace, “Ai baka da wata hanya da ta wuce wannan, yes mun yarda kai ƙaninsa ne da ku ke uba ɗaya, amma muna ganin yadda yake nuna maka ‘yan ubanci, kar ka manta kai da bakinka ka faɗa mana da kuɗin gadon mahaifinku ya tara duk wata dukiya da yake rayuwa a cikinta, ƙarshe dubi yadda ya maishe ka bawa, abu na ƙarshe da zan faɗa maka Suraj, ka je ka yi tunani wataƙila ka samo mafita, ya rage naka.”

Da waɗannan kalami Zinatu ta rufe tattaunawar ta su ta miƙe tsam ta bar su a wajen cikin fushi. Abu ƙalilan ke sa ta ɓacin rai. Shima Habib ficewa ya yi ya bar gidan ran shi babu daɗi sosai ganin yadda ran ‘yar uwarsa ya sosu, Suka bae Suraj cikin tagumi.
Har ga Allah yana so ya samu dama ya wataya da dukiyar da ya yi imanin akwai kasonsa a ciki kamar yadda mahaifiyarsa ta tabbatar masa, kuma wannan dalilin ne ya zaunar da shi a gidan don ya kwashi rabonsa. Ya jima yana takaicin yadda Alhaji Ahmad ya haye kan dukiyar gadon su ya bar su fanko, sai dai ya zagayo ya riƙa yafa musu abinda bai taka kara ya karya ba, irin tunanin da aka ɗora shi a kai kenan, kuma ya hau ya zauna.

Abinda yake gaskiyar lamari kuwa; tun Suraj na goye mahaifinsu ya rasu kuma tun a wancan lokacin aka raba gado na dukiyar da ya bari. Yau da gobe suka lamushe nasu gadon, shi kuwa Ahmad ya faɗa kasuwancin mahaifin su da shi kaɗai ya iya a lokacin, kasancewar ana fita da shi kasuwa yana ganin yadda harkoki suke kuma a lokacin duk ya saba da Costumers ɗin mahaifin nasu.

Da yake dai Allah ya rubuta masa ƙaddarar arziƙi sai kasuwancin ya yi ta bunƙasa har kawo yanzu da yake kan wani mataki mai ban mamaki, wannan sai ya haddasa ƙyashi a zuciyar sauran ‘yan uwansa da kaf cikinsu babu mai arziƙinsa, mahaifiyar Suraj da ta kasa gane cewa iyakar kason shi kawai yake juyawa, ta fi yarda da cewa akwai wata a ƙasa.

Hajiya Sabuwa ita ce mata ta biyu da Alhaji Mukhtar ya aura, tsohon ma’aikacin banki ne sannan tsohon ɗan boko, ya haifi ‘ya’ya sama da goma. Bayan rasuwarsa ne tsabar rashin haɗin kai ya raba kan iyalan kowa ya kaɗi gaban sa. Ko da yake tun a wancan lokacin dama babu cikakken zaman lafiya da ƙaunar juna tsakanin su.

Suraj shine ɗa ɗaya da Hajiya Sabuwa ta haifa, kuma daga shi bata sake haihuwa ba har inda yau ke motsi, don tunda mai gidan na su ya rasu bata yi aure ba. Tun da fari ta ɗauki son duniya ta ɗora wa Suraj, kasancewar sa mai biyayya ne yasa duk abinda ta saka shi baya tsallake maganarta.

Zinatu

Kyakkyawa ce ita sosai, amma irin kyawun da ake kira kyan ɗan maciji, fara ce tas tsaɓanin zuciyar ta, za ta dace sosai a kira ta balbela, shekarun ta na haihuwa talatin da bakwai, bata da fara’a ko kaɗan, sai dai a duk lokacin da ta yi murmushi ta kan ɗauke hankalin mazaje. Iyakar zaman da za ka yi da ita ba zaka taɓa gane sirrinta ba face wanda ta bankaɗa maka.

Shekaru biyu kenan da auren su da Alhaji Ahmad, kuma duk waɗannan shekarun ta yi su ne da mummunan ƙuduri a kansa, bai taɓa gane hakan ba, ba ta jin kuma zai gane har abada. Tana da burika da yawa a rayuwarta, tana kuma da tabbas kan cikar burikan nata, don ta sha yin alfaharin cewa tunda take bata taɓa sa wani abu a ranta tana so ba tare da ta same shi ba.

Tun kafin ta auri Alhaji Ahmad take da burin mallake tarin dukiyarsa ko ta wacce hanya. Hakan ba wani abu ba ne mai wuya a wajen ta bisa la’akari da irin son da yake mata kuma zahiri tana nuna tana matuƙar taya shi son ɗansa Mashkur.

Habib

Ƙaninta ne da suke uwa ɗaya uba ɗaya da take matuƙar ƙauna, faranta masa yana ɗaya daga cikin burikan rayuwarta, shi kaɗai ya rage mata a duniya. Tun suna ƙanana mahaifansu suka rasu. Sun taso hannun ƙanin mahaifinsu, mutumin da ya yi sanadiyyar ɗai-ɗaita rayuwar su, mutumin da ya fara kawo baƙin ciki cikin rayuwarsu, shima ɗaya ne daga cikin waɗanda Zinatu ta ci burin ɗaukar fansa akan su, ɗaya ne daga cikin dangin su da suka guje su a lokacin da duniya ta juya musu doron bayanta.

Alhaji Ahmad

Tun bayan rasuwar tsohuwar matarsa, kuma uwar ɗansa sama da shekaru ashirin da suka shuɗe, Zinatu ita ce mace ɗaya tilo da ta samu shigewa zuciyarsa, ba don kyawunta kaɗai ba, har da tsananin ƙaunar da take nunawa Mashkur, in banda wannan zai iya zama babu aure har duniya ta tashi, don ba ya jin zai samu madadin tsohuwar matarsa.
Tun tasowar Mashkur bai buɗi ido da ganin mahaifiyarsa ba, ya samu labari ta rasu tun bayan da ta haife shi, sai dai ya taso cikin tsantsar gata da kulawar mahaifinsa, har zuwa lokacin da mahaifin nasa ya auri Zinatu matar da ita ma take nuna masa tsantsar kulawa a zahiri.

*****
“Habib yaron nan Suraj fa yana son ba mu matsala.” Zinatu da ke zaune a gefen faffaɗan gadonta a ɗakin barcinta ta faɗa.
Habib ya gyara zama daga inda yake zaune saman durowar gado yana dubin yadda lokaci ƙalilan kyakkyawar fuskar ‘yar uwarsa ta juye zuwa yanayin damuwa da ɓacin rai ya ce, “Tun farko mun yi kuskure da muka shirya kawar da Mashkur tare da Suraj kai tsaye, kamata ya yi yadda muka ɓoye masa batun kawar da Alhaji shi ma kawar da Mashkur ɗin mu rufe shi, sai dai kawai ya ga babu su ba tare da ya san mu muka aika su barzakh ba.”

Zinatu ta girgiza kai, “Tabbas dama ya zama wajibi mu ɓoye masa wasu sirrikan, kamar dai wannan, ko ba komai mutum ne shi mai raunin zuciya da tausayi.”

“Ƙwarai kuwa, sannan na yi imanin tun farko da a ce Alhaji ya ɗauke shi ya ɗora shi kan wata harka aka wayi gari ya ga kuɗaɗe suna shigo masa babu abinda zai ƙara nema a wajen Alhajin, za su iya zaman su lami lafiya ba tare da mun ji kansu ba, kin ga kenan akwai tarin bambanci tsakanin mu da shi.”

“Wannan maganar haka take Habib, yanzu meye abin yi, meye shawararka?” Cewar Zinatu tana duban sa cike da gamsuwa.
“Shiit! Dakata Sister.” Ya faɗa a razane bayan ya ɗora yatsansa saman laɓɓan bakinsa alamar ta yi shiru, me yiyuwa saboda motsin da ya ji a bakin ƙofa.

Suraj da ke laɓe jikin ƙofar ɗakin yana sauraren duk abinda suke tattaunawa ya yi saurin barin gurin.

Zinatu ta tsare Habib da ido, “Me yake faruwa ne?”

“Akwai wanda ya ke yi mana laɓe.”

<< Kudi Ko Rai 1Kudi Ko Rai 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×