Cike da al'ajabin abinda kunnuwansa suka jiye masa ya ja ƙafafunsa zuwa ɗakinsa ya shiga ya kulle kansa a ciki, yana kwance akan gado ya ji takun tafiyar su suna ficewa daga gidan suna surutai ƙasa-ƙasa.
(Kasancewar idan zaka fita daga falon dole sai ka wuce ƙofar ɗakinsa dake hanyar fita)Rayuwa ba ta da tabbas, haka nan ɗan adam ma a kan samu mara tabbas a ko ina, Riƙon amana ya yi ƙaranci a wannan zamani da muke ciki, a iyakar tunanin Suraj bai taɓa zato ko tsammanin makircin Zinatu da Habib ya kai haka. . .