Skip to content
Part 3 of 8 in the Series Kudi Ko Rai by Mustapha Abbas

Cike da al’ajabin abinda kunnuwansa suka jiye masa ya ja ƙafafunsa zuwa ɗakinsa ya shiga ya kulle kansa a ciki, yana kwance akan gado ya ji takun tafiyar su suna ficewa daga gidan suna surutai ƙasa-ƙasa.

(Kasancewar idan zaka fita daga falon dole sai ka wuce ƙofar ɗakinsa dake hanyar fita)
Rayuwa ba ta da tabbas, haka nan ɗan adam ma a kan samu mara tabbas a ko ina, Riƙon amana ya yi ƙaranci a wannan zamani da muke ciki, a iyakar tunanin Suraj bai taɓa zato ko tsammanin makircin Zinatu da Habib ya kai haka ba, rashin imanin nasu ya yi yawa, ashe Alhaji ma so suke su ga bayansa? Ƙwarai biri ya yi kama da mutum.
A baya yana yiwa Mashkur kallon tamkar kishiyarsa, a zaton sa shi kaɗai ne katangar da ta gindaya tsakaninsa da kamfatar arzikin Alhaji. Ko da yake Alhajin da bakinsa ya sha furta cewa Mashkur ɗin shine magajin dukiyarsa ko bayan ransa, wannan ta sa yake ganin matuƙar Mashkur ba shi da kataɓus shine zai kasance madadinsa, dalilin da ya haddasa bayar da goyon bayansa ɗari bisa ɗari aka jefa rayuwarsa cikin wani hali, ya kasance ba shi da amfanin da zai iya jan ragamar komai, sannan a lokacin idon su ya rufe daga shi har su Zinatun, sam ba su yi tunanin irin dulmiyar da dukiyar da Alhaji zai yi ba a kan neman lafiyarsa wanda kuma daga kwanciyarsa rashin lafiya zuwa yanzu kuɗaɗen da aka kashe ba kaɗan ba ne.
Da fari abin sam baya damun su, sai daga baya lokacin da aka fara fita da Mashkur ƙasar waje, sam babu alamar Alhaji zai saurara wajen fitar da maƙudan kuɗaɗen tamkar a ƙasa yake kwaso su duk da cewa wannan ba komai ba ne a wajensa, amma suna jin ƙyashin irin yadda yake kwasar dukiyar yana ɓatar da ita a kan mutumin da sun yi imanin ba zai warke ba. Baya ga haka ma zara ba ta barin dami, yau da gobe kuma ta fi karfin wasa.
A wani kasaitaccen gidan cin abinci suka yada zango, an kawo musu list ɗin abinda za su zaɓa don kaiwa tumbin su, sun zaɓa ɗin ne kawai amma ba don suna buƙata ba, musamman Zinatu da hankalinta ya gaza kwanciya da Suraj tun sa’ar da Habib ya ankarar da ita cewa shine yake musu laɓe a bakin ƙofa, wannan ya tabbatar mata ya ji wani abu da ba sa so ya ji daga cikin abubuwan da suka tattauna.

*****
Misalin ƙarfe biyar na yammaci motar Habib ƙirar Honda Civic ta sako kai farfajiyar gidan mai shuke da launikan furannin da suka haɗu suka yiwa harabar gidan ƙawa. Maigadi na ƙoƙarin rufe get wata motar daban ta sake kunno kai, don haka ya saurara sai da ita ma ta shigo sannan ya ja ƙofar ya rufe. Suraj ne a cikin mota ta biyu.

Maimakon Zinatu da Habib su fito daga cikin ta su motar sai suka yi zaman su har zuwa lokacin da Suraj ɗin ya kammala parking a bayan su, dai dai lokacin da ya buɗe motar ya fito ne, Habib shima ya yi saurin ɓalle murfin tasa motar ya fito har wayarsa na faɗuwa ƙasa ya duƙa ya ɗauka, da sauri ya tari gabansa, Suraj ya ja ya tsaya yana dubansa, hannu Habib ɗin ya miƙa masa suka gaisa.

“Daga ina haka Suraj?” Habib ya tambaye shi yana ƙoƙarin haske shi da murmushi.

“Na je a kan maganar Visa ta ina son yin tafiya a satin nan.”

Gaban Habib ya faɗi! Amma sai ya dake ya ce, “Ok Alhaji ya neme ka ne?”

Suraj ya ɗan taɓe baki haɗi da watsa hannuwa, “No kawai dai zan je ne, akwai abinda nake son yi.”

Suka ɗan tsaya jim, kowa da tunanin da ke zuciyarsa, Suraj ne ya fara takawa a hankali, “Ni zan wuce ciki.” Habib ya ce, “Ok nima bari in ƙarasa gida, dama na kai Aunty unguwa ne.”

Zinatu da ke cikin mota a zaune ta buɗe ta fito fuskar nan tamkar an aiko mata saƙon mutuwa, ba tare da ta dubi inda suke ba ta fara takawa ta shige ciki.

*****
“Mu san abin yi Habib tun kafin yaron nan ya aiwatar da abinda yake nufi da mu, na fahimci ya jefar da makamansa kuma yana son komawa tsagin ɗan uwansa, a taƙaice yana shirin tona mana asiri.”

Cikin tsananin fushi da tashin hankali Zinatu take duban Habin har inda ya sa aya a maganarsa.

“Shakka babu sai yanzu na gane mun tafka babban kuskure da muka haɗa hannu da shi, ko da yake ban taɓa tunanin zai mana haka ba, ya mamaye mu irin yadda ban yi tsammani ba, sai dai zan nuna masa wace ce Zinatu, wallahi ni ba kanwar lasa ba ce, na fi ƙarfin ya ja dani, na rantse da sarkin da ke busan numfashi zan ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kansa.” Ta ƙare furucin da miƙewa tsaye a fusace tare da kama hanyar fita daga ɗakin.

“Dakata Aunty Zinatu.” Habib ya dakatar da ita cikin ɗaga murya sai ta tsaya cak riƙe da labule ba tare da ta juyo ba.

“Me kike shirin aikatawa ne? Calm down, dawo ki ji.”

Duk halin da ake ciki da wuya ta tsallake maganarsa. Tun suna yara shi mutum ne mai kwanya, mafi yawancin lokuta da tunaninsa suke aiwatar da wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu, dole yana da wata mafitar da ta fi abinda za ta aiwatar yanzu, don haka ta dawo ta zauna bakin gadon kamar yadda ta tashi, sai dai har yanzu fuskarta na nuna ranta a matuƙar ɓace yake.

Ya sassauta murya, “Na tambaye ki me kike shirin aikatawa Aunty Zinatu?” Bata bashi amsa ba, ya kuma san mawuyacin abu ne ta iya buɗe baki ta yi masa magana a dai-dai lokacin matuƙar ba hucewa ta yi ba.

“Na san idan kin fita bai wuce ki je ki yi hayaniya da shi ba, wannan shine faɗar da ki ke cewa kin fi ƙarfin sa? Ai idan har da gaske kin fi ƙarfinsa bai dace ki yi ko da cacar baki da shi ba, kuma hakan ba zai amfanar da ke komai ba, ya kamata ki riƙa tunani kafin zartar da hukunci Zinatu, ki saki ranki in dai a kan Suraj ne bai isa komai a kan mu ba waye shi? Me a ka yi a ka yi shi?”

Shekaru Bakwai Da Suka Wuce

Tana jin dirin motarsa a ƙofar gidan ta yi saurin shigowa falon inda yake kwance kan doguwar kujera yana ta sharar barcinsa, ta kira sunan sa. A hankali ya buɗe ido yana dubanta cikin magagin barci.

“Tashi maza ka shige cikin ɗaki ka kwanta ga Ahmad nan zai shigo yanzu na ji motar tsayuwar motarsa a ƙofar gida. Ya miƙe zaune shima tuni ya warware daga magagin barcin da yake, ya tashi ya shige ƙuryar ɗakin kamar yadda ta umarce shi.

Ta dawo tsakar gidan a dai dai lokacin da ya kwararo sallama. Da fara’a ta amsa, ta sake shiga ɗakin ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa masa, ya zauna.

Bayan sun gaisa kamar yadda ya saba zuwa duk sati, idan kuma ya zo ya kan yi musu alheri mai yawa, hatta ci da shan su nauyinsa ne a mafi yawancin lokuta, suka buɗe babin hira sama sama, kamar ko wane lokaci yau ma ta soko masa zancen aure. Tunda tsohuwar matar sa ta rasu shekaru da dama ya gagara yin wani auren, kamar ko da yaushe ya kan ce mata za’ayi ne in sha Allah. Tun tana yarda da maganarsa har ta dawo sai dai ta ji shi kawai.

Ta kan tambaye shi ɗansa da yake ƙasar waje yana karatu ya kan faɗa mata halin da yake ciki cike da jin daɗin hakan. Daga soro wata buduwarwa ce matashiya ta yi sallama cikin gidan, su duka suka amsa mata. Bayan ta shigo ta durƙusa har ƙasa tana gaishe su cikin girmamawa.

Hajiya Sabuwa ta dube ta ta ce, “Hala kin biyo sahun mutumin naki ko?” Maryam ta sadda kai ƙasa cike da jin kunya. Hajiya sabuwa ta sake cewa, “Ai ko ina ganin bai dawo daga makaranta ba.”

Kamar ta yi magana sai kuma ta yi shiru da bakinta, ta ce, “To shikenan Mama bari in tafi na komo idan sun taso.” Daga can ƙuryar ɗakin ji yake kamar ya fito, yana jin lokacin da sahibarsa kuma aminiyarsa ta fice daga gidan. Babu yadda iya dole sai bayan tafiyar Ahmad ne sannan ya fito ya bi bayanta. A gidan su ya same ta, ta fito bayan ya aika yaro ya kira ta, ya haske ta da murmushi.

Madadin ta mayar masa da martani kamar yadda ta saba, sai ya ga ta kawar da kai tana faman shan ƙamshi. Ya kwashe da dariya, “Gimbiyar ya aka yi ne?” Ba ta yi magana ba face ta ƙara tamke fuska.

Ya san kwanan zancen, dole ya shiga rarrashinta da kalamansa masu daɗi har ya samu da kyar ta sauko.

“Ka san Allah Suraj ka yi wa kanka faɗa, mene ne hujjar ƙin karatun da kake?”
Ya ɗan sosa ƙeya haɗi da ɓata rai ya ce, “Mu bar wannan zancen Maryam, yanzu ba lokacin yin sa ba ne.”

Ta tsare shi da ido, “Ni kuma shi nake so a yi, sai me?”

“Sai ki yi ke kaɗai…”

Ya saki ajiyar zuciya. Duk lokacin da ya tuna irin waɗannan abubuwan da suka riga suka shuɗe, suka zama tarihi, sai ya ji duk ya tsani kansa. Lokutan sun wuce ne tare da damarsa. Wata zuciyar ta kan ce da shi, “Har yanzu fa kana da sauran damar da zaka gyara komai, kana da damar da zaka goge tabon da ya disashe haskenka a zuciyar yayanka Alhaji Ahmad, tabon da ya sa yake ganin, tuƙa ɗansa Mashkur a mota, ka kai shi duk inda yake buƙata shine ya fi dacewa da kai.

Ma’ana driven sana’a ce ta waɗanda damar fita da kyakkyawan kwalin karatu ta ƙwace wa. Ya jima da fahimtar rashin tsayawa ya mayar da hankali ga abubuwan da za su amfane shi ne ya sa mutane da dama suke masa kallon wanda bai san ciwon kansa ba, dalilin da ya sa Alhaji ya kange shi daga abubuwa da dama da yake kwaɗayi.

A baya ya tsaya masa tsayin daka kan ya dage ya yi karatu, wanda biyo bayan hakan ke ƙunshe da babban tanadin da yake wa rayuwarsa, a wancan lokacin ya kasa fahimtar haka sai yanzu, ko babu wannan haƙiƙa jahilci cuta ne, cutar da take shafar zuciya har ma ta makantar da ita. Wannan shi ake kira nadama.

Zinatu na sa ƙafafunta a falon suka yi ido huɗu da shi, yana zaune cikin kujera, ƙur suka tsaya suna kallon juna ko wanne da lissafin da ke kwanyarsa, har ta gota shi kaɗan sai kuma ta dawo da baya tana karkaɗa ‘ya ‘yan makullan hannunta.
“Sannu da hutawa Suraj.”

Bai tanka mata ba sanin cewa dole akwai abinda ta tanada a kansa.

“Suraj me yasa kake yaudarar kanka, bayan ka san ba zaka iya ja da Zinatu ba?”
Ba tare da ya dube ta ba ya ce, Ke ce kike yaudarar kanki da zuciyarki da ba ta taɓa kitsa miki alkhairi ba, daga ƙarshe ki sani dole ita zata kai ki ta baro, domin da ke da mummunan shirinki ba za ku taɓa kai labari ba.”

Zinatu ta yi murmushi duk a lokaci guda ta fara ƙoƙarin sanya hannu cikin jakarta.
Kuɗin da ta fito da su daga cikin jakar sun matukar firgita shi, musamman da a rayuwar sa bai taɓa tozali da maƙudan kuɗaɗe kamar su ba, a hankali ta yi taku ɗaya biyu zuwa gab da shi ta zube su a kan hannun kujerar, kasancewar ba su zauna dai-dai ba, hakan ya basu damar zubowa saman cinyarsa, ya bi su da kallo, rafa huɗu ne ɗaure cikin kyauro.
“Ina ganin har yanzu kana da damar gyara kuskurenka na bijirewa buƙatarmu, ko ba komai hakan na iya jefa rayuwar ka cikin dana sani marar amfani, za ka yi asara biyu Suraj, bayan haka ina da tabbacin za ka jefa rayuwarka a tarkon da ba za ka iya fita ba.” Ta fara takawa cikin isa da izza. za ta haye sama.

“Kin ga ji mana!” Suraj ya faɗa da ɗaga sauti. Cike da gadara ta juyo ta kafe shi da ido tana tsumayen kalamin da zai fito daga bakinsa. Ta yi masa farin sani, mutum ne shi mai shegen kwaɗayi, inda su ka yi tarayya kenan, sannan ga shi da ƙarancin tunani, abu ƙalilan ke siye masa ra’ayi, bata jon cewa zai tsallake wannan tarko, shine Plan B ɗin su, kuma za su ba shi fiye da haka muddin zai ci gaba da basu haɗin kai a gudu tare, a tsira tare.

Abinda kawai suke buƙata bai wuce ya ture duk wani sani da sabo, ko ‘yan uwantakar jini da ke tsakaninsa da Alhaji ko Mashkur, ya manta akwai wata alaka tsakaninsu, ta wannan hanyar ne kawai zai samu damar tsaida hankalinsa waje ɗaya ya daina saƙar zuci da kokwanton da yake, sai dai yanayin da ta gani a fuskarsa ya sa ta fargabar abinda zai fito daga bakin nasa, kafin ta ankara kuwa ta ji saukar rafar kuɗaɗenta sun faɗi tim! a gabanta, ta bi su da kallo, wannan ya tabbatar mata ko kaɗan ba su ɗaɗa shi da kasa ba. Lallai da gaske yake.

“Kina iya ɗaukar tarkacen kuɗinki ki ƙara gaba, ba ni da buƙatar su, abinda kawai na sani kuma na yarda da shi ke ce za ki yi dana-sanin cin amanar da ki ke yiwa mijin da yake riƙon ki tsakani da Allah, ya ke zaune da ke matsayin matar da take kare haƙƙoƙinsa ta ko wane fanni. Har yanzu kuna da sauran damar gane illar abinda kuke son aikatawa, saɓanin haka kuwa ku guji RANAR NADAMA tana nan zuwa kan ku Zinatu.”

Ba watsa mata kuɗin da ya yi ba ne ya fi ba ta haushi irin kalaman da ya jefe ta da su, yaron da a baya ko kara ta gindaya ta ce kar ya tsallaka, bai isa ya tsallaka ba, saboda irin yadda a gidan kowa yake gudun saɓa mata, kasancewar ta ‘yar lele, matar son mai gidan, sai wani can banza raɓaɓɓe da shi zai nemi wulakanta ta don kawai tana neman wani abu a wajensa.

Idanun Zinatu suka rufe, ta dube shi da tsananin ɓacin rai a kan fuskarta, “Suraj ba ka isa ba, ka yi ƙanƙanta ka ja da ni Wallahi, don na fi ƙarfinka, ina mai tabbatar maka idan ka ci gaba da wasa da wuta zaka ƙone ƙurmus! A rasa ko da tokarka.”

<< Kudi Ko Rai 2Kudi Ko Rai 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×