Jami'ar Bayero Kano
Anwar matashi ɗan kimanin shekaru talatin, fari ne tas, yana da kyau dai dai nasa, ba a nan kaɗai ya tsaya ba, yana da matuƙar farin jini musamman wajen yammata, hakan ya sa shi yin fice sosai a cikin 'yan uwansa ɗalibai na lokacin, wannan dalilin ya sa baka raba shi da ƙawaye 'yammata a duk inda yake, abin ya hadu da halayyarsa ta shegen son matan tsiya. Yana shekararsa ta ƙarshe inda ya ke karatu a fannin magunguna.
Iyayensa ba masu kuɗi ba ne, sai dai suna da rufin asiri. . .