Skip to content
Part 5 of 8 in the Series Kudi Ko Rai by Mustapha Abbas

Jami’ar Bayero Kano

Anwar matashi ɗan kimanin shekaru talatin, fari ne tas, yana da kyau dai dai nasa, ba a nan kaɗai ya tsaya ba, yana da matuƙar farin jini musamman wajen yammata, hakan ya sa shi yin fice sosai a cikin ‘yan uwansa ɗalibai na lokacin, wannan dalilin ya sa baka raba shi da ƙawaye ‘yammata a duk inda yake, abin ya hadu da halayyarsa ta shegen son matan tsiya. Yana shekararsa ta ƙarshe inda ya ke karatu a fannin magunguna.

Iyayensa ba masu kuɗi ba ne, sai dai suna da rufin asiri bakin gwargwado. Ƙoƙari gami da jajircewarsu a kan karatun nasa ya sa shi kai wa har matakin da yake kai yanzu.
Anwar na ɗaya daga cikin burikan Zinatu na rayuwa, tamkar dai mafi yawa daga cikin ‘yammatamsa ita ma ta haɗu da shi ne a makaranta, tun a wancan lokacin da yake shekara ta biyu ita kuma tana ta uku, inda suka ƙulla soyayya mai tarin yawa, har da alƙawarin aure.

Rugujewar alƙawarin ta samo asali ne, lokacin da Zinatu ta kammala karatunta, sai ƙanin mahaifinta, da yake riƙon ta ya takure shi a kan lallai sai ya turo magabatansa an yi maganar aure, kasancewar ya gaji da nauyin su da yake a kan shi ita da ƙaninta, a lokacin babu abin da ya ke ci masa tuwo a ƙwarya irin kuɗaɗen da yake kashewa a kan su a ko wace safiya a matsayin kuɗin makaranta, wanda ko kuɗin cefanen iyalinsa matuƙar ya yi awo sai haka.

Anwar ba shi da wata sana’a ƙwaƙƙwara da zai dogara da ita ta mayar da shi mai aure, ko da ya fuskanci matsin Malam Sa’adu ya yi yawa sai ya fara neman janyewa daga neman ɗiyarsa, duk kuwa da tsananin son da suke wa juna, lamarin da ya matuƙar ɗaga hankalin Zinatu, ta shiga wani hali mai wuyar a fassara.

Daga ƙarshe dole tana ji tana gani ta rasa shi. A dai dai lokacin wani mutum ya nemi aurenta gurin shi wan mahaifin nata, ya yi farin ciki matuƙa, don shi dai ba shi da burin da ya wuce rabuwa da ita. A take ita kuma ta ce duniya babu wanda ta tsana kamar wannan mutumi, don haka ba za ta aure shi ba. Yin duniya Zinatu ta ce sam ba ta yi, sanadin haka Malam Sa’adu ya ce sai dai ta bar masa gidansa.

Zinatu ta zaɓi barin gidan, inda shima ƙaninta Habib ya ce bai ga ta zama ba ya bi ta duk da cewa ba su da inda ya fi nan ɗin, kazalika ba su da wanda ya fi Malam Sa’adun
A wannan lokaci suka riƙa watangaririya a gari, sanadiyyar faɗawar Zinatun ɗan ƙaramin karuwanci, a ɓangare guda suka fara sheƙe ayar su da masoyinta Anwar.
Habib ya yi iyakar bakin ƙoƙarin ganin ya raba ta da karuwancin ta hanyar zagewa kan neman abinda za su ci, ba sana’ar da bai yi ba a lokacin, basu da taƙamaiman wajen kwana, su tashi can su faɗi can, a haka Allah ya haɗa Habib da wani bawan Allah, ya ɗauke shi matsayin mai wanke masa mota parmanent yana biyan sa, wannan mutum ba kowa ba ne face Alhaji Ahmad, wanda daga baya ya fahimci halin da suke ciki shi da ‘yar uwarsa, gida kyauta ya ba su suke zama tare da alkhairan shi masu yawa a gare su.

A wannan lokacin ne rayuwa ta warware musu suka samu yadda suke so fiye da yadda suke ma a baya. Alhaji Ahmad da kansa ya nuna son auren Zinatu tare da shawara da goyon bayan ɗansa dari bisa ɗari.

Anwar ya tayar da hankalinsa, ganin abar sonsa za tayi aure ta bar shi, so Shu’umi sai ta ji kamar kar ta yi auren, sai dai babu ta yadda za ta bijirewa mutumin da suke rawa da bazarsa, amma fa tana matuƙar son Anwar ɗinta wanda har yau har kwanan gobe suna son juna, ya yi ya yi su riƙa kasancewa tare a wasu lokutan, musamman da yake tana da damar fita a duk lokacin da ta so, ta ƙi amincewa don tana matuƙar jin maganar ɗan uwanta Habib da ɗaukar shawarwarinsa.

*****
Ko da suka dawo gida ma ba su sami Suraj ba, kamar yadda suka fita ba tare da sanin taƙamaiman inda yake ba. Dama dai a cikin ‘yan kwanaki da faruwar lamarin sam ya janye jiki daga al’amuransu, Zinatu ce ta tabbatar wa Habib ba ya gidan, don ta ji lokacin da ya fita da mota da safe, ga shi kuma har yanzu bai dawo ba, to ina ya ta fi?
Abin al’ajabi dai-dai lokacin da Habib ya tura ƙofar ɗakin Suraj ɗin ga mamakinsa sai ya ga ta buɗe, hakan ya janyo hankalin Zinatu dake zaune kan kujera.

Sannu a hankali tamkar mai jin tsoron ƙofar Habib ya ƙarasa tura ta, ta buɗe gaba ɗaya, kamar ko wane lokaci makeken hoton ne ya fara yi wa idanunsa maraba, har kullum yana ji a ran sa matuƙar da gaske ne kyakkyawar budurwar ita ce matar da Suraj zai aura shakka babu ya gama dacewa da kyakkyawar mace irin wacce ko wane ɗa namiji zai yi mafarkin mallaka a rayuwar sa.

Babu wata alama da ta nuna masa akwai mutum cikin ɗakin, hakan ya ba shi damar sa kai ciki gaba ɗaya, duk da cewa ba wannan ba ne karo na farko da ya fara shiga ɗakin hakan bai hana shi kalle kalle tamkar bai taɓa ganin ‘yan komatsan da ke ciki ba, bai tsaya nan ba, sai gashi yana bincike-bincike tamkar yana neman wani muhimmin abu a cikin dakin.

Zinatu tana nan zaune kamar an kafe ta, har zuwa lokacin da Habib din ya fito, ta kafe shi da ido, “Ba ya ciki ko?”

Ya numfasa, “Ba ya ciki, ko ina ya tafi kuma?”

“Ya tafi Zaria.” Zinatu ta faɗa kai tsaye.

Ya dube ta sosai, “Kina so ki ce min ya je wajen Hajiya Sabuwa mahaifiyarsa?”

“Ƙwarai kuwa, kuma ba zai dawo ba ba tare da ya bankada mata sirrin mu ba, lallai Suraj da gaske yake.” Zuciyarta ta fara bugawa, “Habib da zafi-zafi a ke dukan ƙarfe.” Abinda ta faɗa kenan, kawai kuma sai ta jawo jakarta dake gefenta, wayarta ta ɗauko ta fara laluben lamba.

*****
Babu abinda ya fi ba shi takaici irin yadda ya ɓata lokaci yana jan hankalin mahaifiyarsa wajen ganar da ita illar abinda ta sa shi ya aikata, ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita hanyar ba mai ɓullewa ba ce, komai nisan jifa ƙasa zai faɗo, dole akwai ranar nadama tana nan tafe gare su. Duk abinda suka shuka shi za su girba khairan ko sharran.

A kan hanyar sa ta komawa kano, a karo na farko kawai zuciyarsa ta cika da ɓacin rai gami da tsanar munanan halayen mahaifiyarsa, saboda tsananin ɓacin rai ko Maryam bai nema ba ya kamo hanyar kano cike da saƙe saƙe a zuciyarsa.

Misalin ƙarfe biyar na yammaci ya shigo garin kano, a wannan lokacin ne kuma wayar sa dake gefe a kujerar zaman banza ta yi ƙara, ya kai hannu ya ɗauka yana dubawa lambar babu suna don haka ba zai shaida ko waye ba, ya kara ta a kunne yayin da yake murza sitiyarin da hannunsa guda ɗaya cikin ƙwarewa da sanin makamar iya tuƙi, kafin ya yi magana aka riga shi daga cikin wayar, “Ina magana da Suraj ko?

“Eh shine, wa ke magana?” Ya faɗa don ko alama bai shaida muryar ko waye ba.
Daga can ɓangaren mai maganar ya sake cewa da shi, “Ka da ka nemi sanin ko ni waye, domin hakan ba zai maka amfanin komai ba a yanzu, kar ka sake ka yi gangancin komawa gidan Alhaji Ahmad, domin kana taka ƙafa ƙofar gidan sai dai wani ba kai ba, zaka zama GAWA, ka yi ƙoƙari ka kuɓutar da rayuwarka, sun yi shiri sosai domin su ga sun ɓadda ka.”

Saura ƙiris sitiyarin motar ya ƙwace daga hannunsa, ya samu guri ya yi parking yana riƙe da wayar a kunnensa har yanzu, da ƙyar ya iya sake buɗe baki ya yi magana, “Wane ne kai ɗin don Allah?”

“Ba ka ji abinda na ce maka da farko ba, kawai ka yi ƙoƙari ka bi umarnina, idan kana da wani wajen ka je ka fake ɗan samari.” Daga haka dai ba a sake magana ba, yana iya jin lokacin da aka datse wayar Ƙiit! Suraj ya yi kasaƙe yana duban fuskar wayar tasa tsayin wani lokaci.

Sai da ya dai-dai ta nutsuwarsa kana ya ja motar ya fara tafiya. Waje ɗaya yake dashi inda zai je ya fake kamar yadda mutumin da bai san ko waye ba ya ba shi shawara mai tafe da umarni.

Kai tsaye ya karya kwanar da za ta sada shi da sabon gidan da Alhaji ya ginawa Mashkur a unguwar zoo road wanda a ka bashi makullin tun tuni don ya riƙa kulawa da baiwa fulawoyi da sauran shuke-shuke ruwa. Lokacin da ya iso ƙofar get ɗin gidan, bayan ya yi parking da motar sai ya fito ya ƙarasa ya sa ‘ya ‘yan makullai ya buɗe murdeden kwaɗon haɗi da jarmlock ya cire su ya riƙe a hannunsa, ya tura get ɗin ya bude shi baki ɗaya, kana ya dawo ya shige cikin motar ya tashe ta ya sa kai cikin harabar gidan.

Dai-dai lokacin wani baburin a dai-dai ta sahu dake can gefe da gidan ya fara tafiya a hankali a ƙoƙarinsa na barin wajen.

Da ace ya kula da baburin A dai-dai ta sahun da ke bin sa a baya tun daga Unguwa uku, har ƙofar gidan, da a ce kuma ya san abinda zai biyo bayan shigar sa gidan shakka babu da ya ƙaryata mutumin da ya kira shi a waya ɗazu dazun nan.

<< Kudi Ko Rai 4Kudi Ko Rai 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×