Ya fito daga cikin motar ya taka da ƙafafunsa zuwa bakin get ɗin ya ja ya rufe, sannan ya hau ya ƙarasa inda a ka tanada musamman don ajiye motoci. Gidan ya tsaru fiye da zaton mai tunani. A falo ya samu guri ya zauna, zuciyar sa cunkushe da tunane-tunane kala daban daban, bai sake damuwa ya san ko waye mutumin da ya kira shi a waya ba, hasalima ba ya tuna shi, abubuwan da suke damun zuciyarsa daban ne.
Ko ba a faɗa masa ba ya san dole akwai abinda Zinatu da Habib za su shirya masa. . .