Skip to content
Part 6 of 8 in the Series Kudi Ko Rai by Mustapha Abbas

Ya fito daga cikin motar ya taka da ƙafafunsa zuwa bakin get ɗin ya ja ya rufe, sannan ya hau ya ƙarasa inda a ka tanada musamman don ajiye motoci. Gidan ya tsaru fiye da zaton mai tunani. A falo ya samu guri ya zauna, zuciyar sa cunkushe da tunane-tunane kala daban daban, bai sake damuwa ya san ko waye mutumin da ya kira shi a waya ba, hasalima ba ya tuna shi, abubuwan da suke damun zuciyarsa daban ne.

Ko ba a faɗa masa ba ya san dole akwai abinda Zinatu da Habib za su shirya masa a sakamakon bijirewa buƙatar su, son haka yanzu yana jin ya samu matsera daga dukkan wani sharrin su.

Har lokacin Sallar magariba yana zaune a falon gidan ba tare da ya samu sukunin zuciyarsa ba, ya miƙe ya shiga ɗaya daga cikin ɗakunan gidan, ya shiga toilet ya ɗauro alwala ya fito, a tsakar ɗakin ya shimfiɗa darduma ya gabatar da sallah. Ya ɗauki lokaci mai tsawo zaune a wajen, yunwa ya kamata ya ji amma sam ba ya jin ko da alamunta, damuwar da yake ciki ta ƙosar da shi, bai yi yunƙurin tashi ba har gabatowar sallar isha’i.

Bayan ya idar da sallar isha’ ne to wayarsa dake cikin aljihu ta yi ƙara. Ya duba fuskar wayar, dalilin kenan da ya sa shi jin wani sanyi a ransa, bai ɓata lokaci ba ya kara wayar a kunnen sa bayan ya shafe screen ɗin ya ɗaga, muryarta ta kwararo sallama cikin kunnuwansa.

Sai da ya da ya halarto nutsuwarsa gami da kashe murya kana ya amsa mata sallamar.
“Ka kyauta Suraj.” Yadda ta yi maganar ya tabbatar masa bai kyauta ɗin ba, irin abinda bahaushe ke kira GATSE, Suraj ya yi karfin halin cewa da ita, “Kamar ya ya Maryam? Ban fahimci inda maganar ki ta dosa ba.”

“Ai dama ba zaka fahimta ba, amma ko zan iya sanin dalilin da ya sa aikata min abinda ka aikata? kazo Zaria har ka koma baka nemi inda nake ba, wannan ba ɗabi’ar da na san ka da ita ba ce, a ina ka aro ta? Ko dai ba mamaki ka sauya tunani a kaina.”

Ya marairaice murya sosai, “Haba Maryam me ya sa ma za ki yi wannan tunanin? Ko kin san dalilin da ya hanani zuwa gare ki kuwa? Nasan da kin sani da baki faɗi haka ba.”

“Zan iya yarda da dalilinka ko wane iri ne, amma ba zan aminta da hujjar ka ta ƙin buga min waya lokaci mai tsawo har kusan tsayin sati guda, kuma sau biyar ina kiran ka ba ka ɗaga min waya ba, nasan daga baya dole zaka ga missed call ɗina ko?”

Ya sauke gwauron numfashi. “Maryam ki yi haƙuri, ki gafarce ni ina cikin wani hali da nake buƙatar taimako, ina so ki sani irin wannan lokacin da kika daɗe kina ankarar da ni zuwan sa tun a baya, lokacin da zai iya zuwa ya kasance tare da ni cike da nadama da da na sani, to fa ya zo yanzu haka ina tare da shi Maryam, ba ni da wata mafita.”

Daga can ɓangaren Maryam jikinta ya yi sanyi, cikin ƙanƙanin lokaci Suraj ya tura mata tsananin tausayinsa a cikin zuciyarta, ta sauke ajiyar zuciya, “A cikin kalaminka alamu sun nuna min cewa kana cikin wani mawuyacin hali, Me yake damunka please?

“Maryam akwai matsala, duk da bai kamata ki ji abinda zai fito daga bakina ba ya zama tilas in faɗa miki kasancewar ki mafi kusanci a da ni.” Suraj bai ɓata lokaci ba ya kwashe duk abinda ya faru ya faɗa mata, sannan ya ci gaba da cewa, “Ba komai ba ne ya fi ɗaga min hankali irin halin da bawan Allah nan ya ke ciki, wallahi duk lokacin da na tuna cewa da sa hannuna a ka yi masa wannan abun sai in ji duk na tsani kai na, sannan wani abin takaici Umma ma irin tunaninta kenan.”

Maryam ta kai rabin sa’a ba ta ce uffan ba, yayin da ɓangarensa shima ya yi shiru yana jiran abinda zai fito bakinta, yana cike da fargabar irin hukuncin da za ta yanke masa sannan yana ta ƙoƙarin hana gamsar da kansa cewa bai kamata ta san abinda ya faru ba, sai babu yadda za a yi ya samu sukuni matuƙar bai fada mata ba, don a sa’i guda ya ji a jikinsa tamkar ita kaɗai za ta iya bashi mafita game da halin da yake ciki.

Ta numfasa a hankali, “Haba Suraj me ya kai ka biye wa son zuciya da wa shaiɗan har ya samu nasarar kitsa maka aikata irin wannan mugun aiki?”

“Ki fahimce ni Maryam, tabbas na aikata kuskure, amma yanzu na gane illar abinda na yi, na san wannan ba aiki ba ne mai kyau sai dai ita ƙaddara ce idan ta zo wa bawa babu yadda zai iya kauce mata.”

“Haka ne, shikenan ka gode wa Allah da ya ganar da kai, yanzu kana ina?”
Suraj ya faɗa mata yadda su ka yi da mutumin nan ta waya. Maryam ta ɗan yi shiru jim kaɗan sannan ta ce, “Ka san wani abu?” Ya ce, “Sai kin faɗa.”

“Wallahi shi kansa mutumin da ya kira ka a waya ya sanar da kai hakan a matsayin shawarar kuɓuta ba abin yarda ba ne, idan haka ne me ye dalilin sa na ƙin bayyana maka ko shi waye? A ina ya san ka har ya samu lambarka? Bugu da ƙari ya san sun shirya maka wani abu, tunda a cikin labarin ka faɗa min babu wanda ya san abinda ku ke shiryawa daga kai, Zinatu, Habib, Boka, sai Umma da ka faɗa wa ɗazu ɗazun nan, a kwai buƙatar ka yi tunani da bincike kafin ka yarda da mutumin, yanzu ka yi ƙoƙari ka bar gidan nan, don tunanina yana ba ni an haɗa baki da shi ne domin a cuce ka.”

Lokaci guda gabansa ya yi wata mummunar faɗuwa! zumbur ya miƙe tsaye yana ƙarewa ɗakin kallo, sai yanzu tunanin cewa akwai safayar makullin gidan a hannun Habib ya faɗo ransa, tabbas za su iya riga shi shigowa su barbaɗa duk abinda suka ga dama.

Motsin da ya jiyo a bayan tagar ɗakin ne ya ƙara jefa tsoro a cikin zuciyarsa, da sauri ya ƙarasa jikin tagar ya ɗaga labule don ya leƙa, sai ya ji kamar takun mutum ya bar gurin da sauri, sakin labulen ya yi ya fita zuwa falo da hanzarinsa, har yanzu yana riƙe da wayar a kunnensa, yana kuma ci gaba da sauraren Maryam.

Ga tarin mamakinsa sai ya ga ƙofar falon a buɗe wayam, hakan ya san ya masa tsananin tsoro gami da shakkar ci gaba da tafiya a tsakar falon don ba ya ko tantama ba shi kaɗai ba ne a cikin gidan. Tunani da numfashin sa suka tsaya cak sa’ar da idanunsa suka ga gabjejen mutumin ya fito daga ɗakin da ke kusa da wanda ya shiga, hannunsa riƙe da kakkaifar wuka tsirararta.

Zuciyar Suraj ta tsinke, lokaci guda yawun bakinsa ya ƙafe ƙaf, me yiyuwa da za a tsaga jikinsa zai yi wahala a riski jini, wayar tana jikin kunnensa, yana kuma iya sauraren ragowar jawaban Maryam da suka ƙunshi nasiha da jan kunne, har zuwa lokacin da ta saurara tana tsumayen abinda zai fito bakinsa.

Sai dai hankalinsa sam ba ya tare da ita, yana kan gabjejen mutumin da ke tunkaro shi gadan gadan fuskarsa rufe da baƙin ƙyalle, ba girman mutumin ke bashi tsoro ba face kakkaifar wuƙar da ke hannun sa.

Maryam ta gaji da saurare ta fara faɗin, “Hello! hello! Suraj.” Cikin ɗaga sauti, ya kasa cewa da ita komai har zuwa sa ar da baƙin mutumin ya ƙaraso daf da shi, ya miƙa masa murɗaɗɗen hannunsa. Suraj ya san abinda hakan yake nufi, cikin rawar jiki ya cire wayar daga kunnensa ya miƙa masa ba tare da ya yanke kiran Maryam ba. Ya karɓa shima ya kara ta jikin kunnensa har kawo wannan lokacin Maryam tana ta faɗin hello! hello! Suraj kana iya saurare na? Lafiya kake kuwa?”

Maimakon ta ji amsa sai ta ji ya saki wata irin ƙara mai razanarwa! Ta ƙwala kiran sunansa da ƙarfi, “Suraj!” Dai dai nan ta ji an katse wayar. A karo na biyu Maryam ta sake yunƙurin kira, sai ta ji ma an kashe wayar gaba ɗaya. Tabbas akwai mummunan abun da ke faruwa. Zuciyar ta ta fara lugude, ta rasa abin yi, sai kai gwauro take tana kai mari a tsakar ɗakinta, tana duba fuskar wayarta tamkar mai son yin tozali da abinda ke faruwa a ciki.

Ta fito tsakar gidan su, in da mahaifiyarta ta ke kwance a cikin rumfa kan tabarma tana hutawa, bata tsaya ba ta fara ƙoƙarin ficewa daga gidan.

“Ina za ki je kuma?” Ta ji muryarta, daɓa ta san ba barci take ba, idonta biyu.

“Mama yanzu zan dawo recharge card zan siyo.” Mahaifiyar ta ta ba ta sake cewa da ita komai ba ta mayar da kanta saman filon ta sake kwanciya.

Lokacin da Maryam ta iso bakin titi akwai wadatattun ababen hawa, ba ta ɓata lokaci ba ta samu adai-daita sahu ta hau, duk da cewa, yawancin lokuta a ƙafa take zuwa gidan su Suraj kasancewar ba wata tazara ke da akwai tsakaninsu ba, ta yi hakan ne don ta yi saurin zuwa ta dawo, kasancewar dare ya fara kawo kai.

Hajiya Sabuwa tana kwance a cikin ɗaki ba ta jima ba da ta rufe gidanta, sai ta ji ana buga ƙofa, ba ta motsa ba sai da ta ji an sake buga ƙofar a karo na biyu, ta tashi zaune daga kwancen da take. Aka ci gaba da bugun ƙofar, ala tilas ta sauko daga kan gado ta fito tsakar gida har zuwa soro.

Lokacin da ta bude ƙofar ta ga Maryam ne mamaki da saƙe-saƙen abubuwa da dama suka ziyarci zuciyarta.

“Kamar Maryam na ke gani lafiya kuwa?”
“Muje daga ciki Umma.” Maryam ta faɗa.
Hajiya Sabuwa ratse gefe ta bata hanya Maryam ta shige sannan ita ma ta rufa mata baya, a tsakar gida, daga tsaitsaye ta kwashe duk abin da ya faru ta sanar da ita.

Hajiya Sabuwa ta saki salati tare da ɗora hannu a ka, “Na shiga uku na lalace, shikenan sun kashe min ɗa ni Sabuwa ina zan sa kaina?”

Kururuwar da take ya sa Maryam karaya ita ma sai ta fara zubar da hawaye, “Umma yanzu meye abin yi?” Ta tambaye ta. Sai da ta share hawaye da haɓar zaninta kana cikin kuka ta ce, “Abinyi Maryam yanzu zan tafi kano, da sauran lokaci, zan samu mota, ki koma gida kar dare ya yi.” Ta shige ɗaki ta bar Maryam nan tsaye tana wassafa lamarin, idan har ya tabbata cewa sun kashe Suraj ina abin yi kenan?
Tare suka fito daga gidan, Maryam ta koma gida, yayin da Hajiya Sabuwa ta kama hanyar kano a daren.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kudi Ko Rai 5Kudi Ko Rai 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×