"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!"
Kalmar dana ambata kenan ina me saurin dafe bango saboda hajijiyar dake neman ɗibana ta watsar a ƙasa.
a lokaci ɗaya jina da ganina suka ɗauke na tsawon daƙiƙu, na ƙara rumtse idanuwana da tartsatsin wuta ke ambaliya a cikin su.
ƙafafuna suka min nauyi na kasa ko da motsa su balle na iya ɗaga su na nemi madafar tsayuwa, zuciyata ta matse, ƙirjina ya shiga bugawa tamkar ana buga mandiri, wucewar daƙiƙu biyar ina dafe da bango kafin na samu na dawo hayyacina, zuciyana da bakina ba su fasa. . .
Gaskiya malama Halima wannan littafi naki ya taɓo wani batu mai matuƙar muhimmanci. Allah ya ƙara basira da hazaƙa.
#haimanraees