Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Kukan Kurciya by Halima Zakariyya

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!”

Kalmar dana ambata kenan ina me saurin dafe bango saboda hajijiyar dake neman ɗibana ta watsar a ƙasa.

a lokaci ɗaya jina da ganina suka ɗauke na tsawon daƙiƙu, na ƙara rumtse idanuwana da tartsatsin wuta ke ambaliya a cikin su.

ƙafafuna suka min nauyi na kasa ko da motsa su balle na iya ɗaga su na nemi madafar tsayuwa, zuciyata ta matse, ƙirjina ya shiga bugawa tamkar ana buga mandiri, wucewar daƙiƙu biyar ina dafe da bango kafin na samu na dawo hayyacina, zuciyana da bakina ba su fasa maimaita kalmar innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ba.

“Nura!”. na kira sunan da wani irin amon sauti da ban san ina da shi ba. kuma tunda na ambaci sunan nasa sai na ƙara ƙafewa tamkar gunkin da aka sassaƙa, yawun bakina ya bushe.

a wannan lokacin da nake manne da bangon ƙofar gidan mu, a jikin rila, iska ce me sanyi take kaɗawa ta ko’ina, duk mutanen da suke wucewa jikinsu lulluɓe yake da rigunan sanyi suna ƙanƙame jikinsu saboda mashahurin sanyin da ake zubawa a garin, irin sanyin nan da haƙora ke caccakewa da juna, amma ni a lokacin wani uban gumi ne ke keto min na kata’i, wanda lokaci ɗaya ya jiƙa min jiki naji tamkar an watsa min ruwan zafi.

idanuwana da basa gani sosai acikin gangamin hazon da ake yi, na kanne su ina bin bayansa da kallo, ina kallon yanda yake takawa yana tafiya yana barin kusa da ni, cikin kaina ina ƙirga kowanne taku na tafiyarsa, yayinda zuciyata ke matsewa tana ƙara cunkushewa da sautin takun tafiyar tasa.

sai da ya isa bakin motarsa ya buɗe zai shiga, sannan na samu wani ɗan guntun kuzari a tare da ni, na sulale gwiwoyina suka zube a ƙasa, ƙarar sautin bugun simintin yay duka har cikin dodon kunnena.

“Nura! ka dakata Nura don Allah”.

bakina ya motsa da ƙyar wajen faɗin hakan, kuma furucin ya fito tattare da matsanancin sabon kukan da ya kufce min.

na dinƙa bin Nura da kallo ta cikin ruwan hawayen da ya taru a idona, kallonsa nake amma wani sabon mutum na daban nake gani a tare da shi, domin asalin Nura dana sani ba zai taɓa iya ruguza zuciyar mace ba, macen ma wacca ta aminta da shi, ta shaƙu da shi, tayi dukkan amanna da shi akan cewar shi ɗin nata ne, kuma ita ɗin tasa ce, macen da suka shafe shekaru biyar suna tsafatatacciyar soyayya, wannan macen da a kullum yake furta cewa kece uwar ƴaƴana, kece mafarkina, macen da baida wani buri da ya wuce yaga ya mallaketa, amma a yau ita yake kallo yake furta mata cewa babu ni babu ke, ME YA ZAMA SILA WANDA BAN SA NI BA?

“kiyi haƙuri Mujahida…”

furucin nasa ya yanke dukkan tunanina, ya kuma nemi yay raga-raga da zuciyata, nayi saurin ɗaga hannu na dakatar da shi daga maganar da yake yi.

“saura fa kwana ɗaya, Nura saura kwana ɗaya kacal fa, Nura me nayi maka a rayuwar nan?, wanne kuskure na aikata maka da ban cancanci ka yafe min ba?, Nura ka rasa lokacin da zaka ce ka fasa aure na sai a saura kwana ɗaya auren mu?, na shiga uku na lalace, me mutane za su ɗauke ni?, wanne kalar tunani za su yi akan hakan?, Nura me zance wa iyayena?”.

na faɗa ina dukan kaina ajikin garu, sai na tsinci maganar Nura na cewa da ni,”a yanda kika mayar da kanki a haka zasu kalli maganar lalacewar aurenki, banda niyyar tozarta ki a rayuwa, ada ina sonki sai dai yanzu kin fita a raina, domin ba zan iya zaɓawa ƴaƴana uwa irinki ba, haka nima ban cancanci auren mace irinki ba, ki koma cikin gida, ki zauna ki natsu kiyi nazari, anan zaki fahimci dalilin da yasa na fasa auren ki, na barki lafiya”.

yana gama faɗar hakan ya ɗaga ƙafafunsa ya shiga cikin mota, kafin daga bisani ya figi motar ya baɗe ƙofar gidanmu da ƙura, ban ɗauke idona daga bin bayan motar da kallo ba har sai da ta ɓacewa ganina.

tabbas ayau na gasgata cewa babu tashin hankalin da ya wuci a tsaida ranar aurenka kuma a fasa, nafi ƙarfin mintuna goma yashe a ƙasa a wajen, har sai da ƙanina Mujtafa yazo ya sameni ya ɗago ni da kansa, ya kama hannuna muka shiga ɗan ƙaramin gate ɗin gidanmu, ba don yana riƙe da hannuna ba tabbas da ban iya shiga gidan ba domin kuwa kwata-kwata bana ganin abunda ke gabana.

muna saka ƙafafun mu acikin ƙofar da zata sadaka da cikin gidanmu, naji wata sabuwar hajijiya ta ɗebe ni tayi walagigi da ni ta yarfar a ƙasa, nayi saurin kai hannu zan toshe kunnuwana saboda na dakatar da abinda nake ji daga bakin Umma na, amma inaaa furucin da Babanmu yayi shi ya tsayar da ni.

“abunda kika gani ajiki shi nake nufi, kije na sake ki saki biyu Bilki, idan kin sami wani mijin kiyi aure domin ni ba zan iya zama da lalatacciya kuma watsatstsiyar mace irinki ba, wallahi summa tallahi nayi dana sanin auren ki, domin sam ba kece macen da addini yace mu zaɓa ba wajen aure, ki kwashe komai naki ki bar min gida cikin ƙasa da mintuna biyar.”

sai naji kuma Ummana na cewa, “yanzu Baban Mujahida ka rasa a lokacin da zaka sake ni sai a saura kwana ɗaya auren ƴata?, me nayi maka Habibu?, wannan kalar tozarcin fa har ina?, kasan kuwa irin furucin da kake min?, Habibu ni matarka da muka shafe sama da shekaru 20 tare zaka datse igiyar aurenmu a saura kwana ɗaya mu aurar da ƴar mu?, wannan ranar fa ita muka daɗe muna jira Habibu, me yasa?”.

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un

na ƙara nanata kalmar acikin kaina, domin nasan ita ɗaya ce zata yi maganin duk wata musiba dake afkuwa acikin gidan mu daga daren jiya zuwa yau.

Mujtafa ya durƙuso kusa da ni yana ɗago ni yake faɗin,”Yaya wai meke faruwa da ke ne?, ba ki da lafiya?”

ya faɗa yana ɗaga ni zaune, na miƙe da ƙyar muka shiga cikin gidan, na sami Umma tsaye a gaban Baba tana hawaye sosai, Baba kuma na gefe yana hucin bala’i, kallo ɗaya nayi masa na hangi tsananin ɓacin rai da tashin hankali wanda ban taɓa ganinsa aciki ba iyakar tsayin rayuwata.

“Me ke faruwa?”
zuciyata ta tambaya, kafin kuma na sami amsa sai na bi ƴan taron biki da kallo, kowa yay curko-curko a tsakargida ana kallon Baba da Umma kamar an sami tv, sai dai kana kallon fuskar kowa girgije yake da lamarin da ke faruwa na sakin auren.

lokaci ɗaya gidan ya koma tamkar anyi mutuwa, tsakar gidan yay tsit sai kukana da shashsheƙar kukan Ummana da ke tashi. sallamar Kakar mu Iya muka jiyo, kallon mu duk ya koma gare ta da abunda ta shigo tana faɗa.

“Salamu alaikum, yo ai barin tsayuwar tsakar gida zaku yi mu shige cikin uwar ɗaka. yau dai wannan ahali bamu tashi cikin sa’a ba.”

ganin yanda duk take a ruɗe Baba yace,”lafiya Iya?”

“ina kuwa lafiya Habibu, ina zaune an kira ni ance ka saki matarka, kafin in kira ka inji ba’asi sai ga Sabitu ya kira ni yana faɗa min baƙin labarin cewa wai wannan yaro Nura yace a tsayar da shirye-shiryen aure ya fasa…ke Bilki maza buɗe ɗakin ki mu shiga ciki maganar ai bata tsaye bace”.

sai kuma ta juyo tana kallona tace,”ja’irar yarinya, albasa dai bata yi halin ruwa ba wallahi, to dan ubanki kuka ai baki fara shi ba, tashi ki wuce muje ciki ko in sanar da ubanki dalili ya fara tamole da ke tun yanzu, ya ƙarasa da ke cikin ɗakin da kutufo”.

ina kallo Umma da Baba suka shiga parlo jiki duk a saɓule kamar waɗanda aka yiwa mutuwa, sannan babban Yayan su Baba da muke kira Baba Musa shima ya shigo da sallama ya wuce parlo, Baba Sadisu kuma ya mara masa baya shima wanda yake ƙanen Babana ne, ni dai har lokacin na kasa motsi, dalili kawai nake nema, dalilai guda biyu, dalilin da yasa Nura ya fasa aurena da kuma dalilin da yasa Baba ya saki Ummana.

na miƙe tsaye da ƙyar ina rangaji na bi bayan Iya, ina saka ƙafata cikin parlon gabana yay wani mugun duka, Baba Musa ya yarfa min wani mugun kallo da ya haddasawa ƴaƴan cikina hautsinawa, ya sakar min wata muguwar tsawa da ta amsa a duka gidan mu, babu shiri na rumtse idanuwa saboda tsananin tsorata.

“tsaya daga nan bakin ƙofa kar ki ƙaraso mana nan.”
Baba Sadisu ya faɗa yana jifana da kallon banza.

na zube ƙafafuna a ƙasan wajen, sabbin hawaye suka shiga sintiri saman fuskana, naji na ƙara tsanar kaina, sakamakon kallon tsanar da naga dukka iyayen nawa su na yi min.

“Kai Musa ai sai ka yiwa Habibun bayani ko, daga nan ku nemo bakin zaren abun da zaku faɗawa jama’a idan suka ji batun fasa auren da za’a ɗaura gobe”. cewar Iya.

muryar Babana kamar zai fito da kukan zucin da yake yace,”Yaya Musa ka faɗa min me yake faruwa?, zancen fasa auren nan ya ɗaga min hankali, tashin hankalin da nake ciki tun daren jiya ya ninku, yanzu haka ji nake kamar zuciyata zata buga.”

“to Habibu matsayin mu na musulmai dole muyi haƙuri mu karɓi ƙaddara hannu biyu, don haka wannan abu da ya faru sai dai mu roƙi ubangiji ya bamu ikon yin tawakkalli. ina zaune a cikin gida Hajara na mun batu akan sauran kayan ɗakin yarinyar nan da ba’a siya ba, sai ga kiran Alhaji Lukman wato shi mahaifin Nura kenan, bamu wani jima muna gaisawa da shi ba yace min ai Nura yazo ya same su yanzu ya sanar musu cewa a tsaida maganar aure shi kam ya fasa, suka titsiye shi da tambaya yace kawai auren ne ya fita akansa, to dai haka su kai ta kai ruwa rana har ya fito ya faɗa musu dalili cewa shi ba zai auri Ƴar Maɗigo ba, Mujahida Ƴar Maɗigo ce, a daren jiya ƙawarta Halisa ta zayya ne musu komai, to kaji dalili, wannan ƴa dai ta jefa mu a bala’i”.

Baba Sadisu ya ɗora da cewa,”and ya ƙara faɗar cewa Mujahida na ɗauke da cutar zamani….”

ina kallo Babana ya wani zabura ya miƙe tsaye tare da faɗin,”wacca iriyar cutar zamani?”

“cutar ƙanjamau”. ai ban san lokacin dana miƙe a gigice ba ina girgiza kaina ina faɗin,”a’a Baba wallahi ƙarya yake yi, ni ban taɓa aikata zina ba na rantse da Allah, sharri Nura yake yi min Baba wallahi ƙarya yake.”

Baba Musa yay min wani mugun kallo murya a kumbure yace,”idan shi Nura da mu mun miki ƙarya ai shi likitan da kike zuwa wajensa ba zai yi miki ba ko?”

ban sami zarafin yin magana ba naji Baba Sadisu na magana a waya yana cewa,”Dr Bismillah”. kuma kafin ƙiftawar ido sai gani nayi an ɗaga labule an shigo, allon ƙirjina ya girgiza fiye da zato saboda ganin Dr Bashir, har ya nemi kujera ya zauna ban iya ɗauke idona akansa ba.

sai da ya zauna tukunna laɓɓana suka tale wajen furta,”Dr karka min sharri, kaji tsoron Allah ka faɗa musu gaskiyar cutar da take damuna, ni ban taɓa aikata zina da wani ɗa namiji ba taya zan kamu da cutar ƙanjamau?”

Dr Bashir ya numfasa sannan yace,”kwanakin baya ƴarku tazo asibiti kan matsalar ɗoyin farji da take fama da shi, da kuma ciwon sanyin mara da a turance muke kira (gonorrhea), wanda hakan ke samuwa ta dalilin aikata masturbation. to bayan nan a shekaranjiya sun je asibitinmu domin ayi musu gwajin genotype ita da Nura, to ta dalilin wannan ɗiban jinin aka gano tana ɗauke da cutar ƙanjamau.”

“ƙarya kake yi ni ban taɓa kusantar ɗa namiji ba, wallahi banda ƙanjamau.”

“Mujahida ki nutsu, ni ba likitan da za’a haɗa baki da shi ba ne a cuci wani, maganar gaskiya kina ɗauke da cutar ƙanjamau, abunda ba’a san da shi ba mostly shi ne, A wani bincike da aka gabatar, ya tabbatar da za’a iya ɗaukar cutar ƙanjamau ta hanyar maɗigo, idan aka yi da wadda ta-ke ɗauke da ita, kamar yadda za’a iya samun ciki ta hanyar maɗigo, idan mace ta yi da wadda ba ta daɗe da saduwa da ɗa namiji ba, kamar yanda likitoci suka tabbatar da maɗigo da istimna’i su na iya jawo rashin haihuwa, kamar dai ke da istimna’i ya janyo miki cutar ɗoyin farji da kuma sanyin mara”.

furucinsa na istimna’i take anan zuciyata ta tariyo min abunda ya faru a daren jiya.

sai na ɗaga kai na kalli Baba, muka haɗa ido da shi yay saurin yin ƙasa da idonsa, wanda hakan ya shaida min ganina ne baya ƙaunar yi, ban san lokacin dana dire gwiwoyina a ƙasa ba na sake fashewa da kuka me taɓa zuciyar duk wani me imani, cikin wani irin ƙaraji na furta.

“Allah ya isa, Allah ya isa tsakanina da ke Ummu Auwal, wallahi ba zan taɓa yafe miki ba, duk kece silar halin da na shiga, Allah ya isa da izinin ubangiji ba zaki gama da duniya lafiya ba, insha’Allahu ba zaki yi tozali da manzon…”.

ban sami damar ƙarasa maganata ba naji Baba ya doka min wata razananniyar tsawar data kaɗa ƴaƴan cikina, tsawar da tasa na ɗago a furgice ina kallon Ummana wacca tasa hannu ta rufe bakinta idanuwanta a warwaje, Baba kuma ya saki baki ya rasa abun yi, zan kuma buɗe baki nayi magana Baba ya kuma buga min tsawar data fi ta ɗazu, tsawar da ta lula da ni duniyar tunanin daren jiya, tunanin abun da ya afku, daren da ya zama mafi muni a tarihin rayuwata, daren da bana fatan in maimaita irinsa ko a mafarki, a daren jiya daren da nake kira da baƙin dare, mahaifina ya shigo ɗakinmu ya same ni cikin wani mummunan yanayi.

tunanin wannan daren yasa nayi saurin runtse ido ina jin wani ɗaci da ƙullutun baƙin ciki a ƙirjina, ina me bala’in danasani da nadamar karantun littafin batsa a rayuwata, tare da la’antar duk wani marubucin littafin batsa da duk wanda ke dasa hannu akan yaɗa shi a media, domin da ba’a yaɗa shi ba da bai iso garemu ba har ya lalata rayuwamu.

A DAREN JIYA

kwance nake a ɗakin mu, kan ƙaramin gadonmu wanda muke kwanciya ni da ƙanwata Amira, na rufa da ƙaton bargonmu me ɗan banzan ɗumi, yayinda nake riƙe da wayata a hannu ina karatun littafin hausa me suna *YANAYI* na marubuciya *UMMU AUWAL*, ina masifar son littafan marubuciyar saboda babu abinda ta iya rubutawa sai zalƙar iskanci.

shauƙin karatun littafin yasa gaba ɗaya na mance a inda nake, domin kuwa ina cikin wani irin yanayi ne mara daɗin fasaltuwa, ƙafafuna buɗe suke na saka hannuna guda cikin wandona, idanuwana a wani irin lumshe saboda jin daɗin abinda nake aikatawa kaina becox i want to be satisfied, irin satisfied ɗin da marubuciyar ke faɗa, kai har wani karkarwa nake yi saboda ji nake ina ma ace akwai wani ɗa namiji ko mace ƴar’uwata da za su iya sauke min buƙatata a halin da nake ciki, sai dai ko babu komai Ummu Auwal ta taimake ni da take fayyace komai wajen koyar da mu yanda zaka yi sex da sauran su, don ni dai na gode mata domin ba don ta sanadin karantun littafanta ba da ban san yanda zanyi wajen ragewa kaina sha’awar dake bala’in addabata ba kusan ko da yaushe.

ba komai nake yi ba illa kwatanta abunda nake karantawa a littafin, labarin da aka rubuta shi da tsantsar batsa ta bala’i, fayyace komai na yanda ake sex, masturbation, lesbian, kai wasu irin kalami ma masu hawa kan mutum da tayar da zuciya saboda ƙyanƙyami, irin kalaman da sai in har baka karanta ba amma sai ka tsinci kanka acikin hali na matsananciyar sha’awa, idan azumi kake ibadarka zata karye tabbas, kalamai ne da har nake mamaki da ganin ƙoƙarin marubuciyar wajen fitsarar iya rubuta su.

a lokacin na cije leɓe sosai ina ƙara cigaba da aikata duk abunda na karanta, saboda sosai yanda ake koyar da lesbian sex da masturbation a labarin ke rikita ni.
cikin wasu ƙalilan ɗin mintuna na gama fita a hayyacina, domin kuwa har Baba yazo ya yaye bargon da nake lulluɓe da shi ban sani ba, sai a sanda naji an sheƙo min ruwan sanyi tukunna nayi furgigit na dawo kyakykyawar duniyar dana bari.

sai dai sam har lokacin na kasa cire yatsana daga ƙasana, haka ma na kasa ɗauke hannu daga saman breast ena waɗanda nake wasa da su. a karo na biyu da aka ƙara sheƙo min ruwan sanyi tare da jin saukar bulala a jikina, babu shiri na dawo hayyacina gaba ɗaya, nayi azamar miƙewa zaune ina haki tare da zare idanuwa kamar mujiya, ganin Baba tsaye akaina nayi saurin miƙa hannu na janyo bargo tare da rufe jikina, domin kuwa tsirara nake haihuwar uwata da ubana.

ƙarfe ɗaya na dare a lokacin amma haka Baba ya zage dukkan ƙarfinsa yana min dukan mutuwa, kuka nake ina ihu ina kiran mutane akan azo a cece ni.
a lokacin kuma Umma ta faɗo ɗakin a rikice, babu yacca bata yi ba akan Baba ya daina dukana amma inaaa yayi nisan da baya jin kira, kai dukan da ta kai har sai da ya koma haɗawa da Umma saboda tsananin fusata, jikina duk ya farfashe, da ƙyar dai ya dawo hayyacinsa ya fuskanci Umma yana cewa da ita,”abunda ƴar nan zata saka mana da shi kenan?, ɗauki wayarta ki duba Bilki”.

furucin nasa yasa Umma kallona, sannan ta kai hannu ta ɗauko wayata, a lokacin wata azababbiyar kunya suka lulluɓe ni naji kamar in tsaga ƙasar wajen in rufe kaina, domin tabbas abun kunya ne ace iyayena sun ci karo da irin baɗalar da nake karantawa a matsayina na ƴar musulmai, kai ko mara addini ban jin zai iya karanta rubutun, wallahi har gwara ma da Allah yasa iyayena ne ba wani ba, don tabbas duk wanda yaga batsar dake cikin labarin nan sai ya daina ganin mutumcina har gaban abada, babu kuma mutumin kirkin da zai so yay mu’amala da ni, kai da gani kasan wacca tayi rubutun ba me tarbiya ba ce, kazalika da wuya idan daga gidan tarbiya ta fito, duk wata kalma da ke jikin rubutun haramtacciya ce a addinin muslim da christan.

da farko nayi zaton kwarton namiji ne me rubutun ba mace ba, don dai duk wata mace ta gari data san zata yi aure ta zama uwa, ba zata iya zaman rubuta abunda tasan ba zata taɓa iya barin wani sashi na jikinta ya karanta ba.

kallo ɗaya Ummana tayi min a sanda ta karanta point ɗin da nake, sai naga ƙwayar idonta ta sauya kala, tsananin tashin hankali ya bayyana a tare da ita, tamkar zata yi kuka, cikin sanyin jiki ta saki hannuna ta miƙe tsaye, a hankali ta shiga furta kalmar innalillahi, ta juya ga barin kallona tana kallon gefe na daban tace da ni.

“tarbiyar da muka yi miki kenan Mujahida?, dama abunda kike aikatawa kenan a bayan idon mu?, Mujahida yaushe gangar sheɗan tayi miki daɗin da har kika bi ayarinsa?, dama ta wannan hanyar kike amfani da wayar?, mun siya miki domin karatu ashe ke iskanci kike yi da ita, Mujahida tunaninki wannan ba saɓon Allah ba ne?, ko mantawa kika yi akwai Allah yana kallonki yana kallon duk abunda kika aikata a fili ko a ɓoye?, kin cuce ni Mujahida domin ba tarbiyar dana miki kenan ba”.

sai ta runtse idonta sosai, da alama zuciyarta nayi mata zafi kamar wuta.
gani nayi tayi dirshen a gefen gado, kuma lokaci ɗaya ta fara zubar da hawaye, sai naji zuciya ta matse ta ƙara ƙuntata fiye da da, naji duk na tsani kaina da ma duniyar, yau rana ta farko kenan da zance naga hawayen mahaifiyata, haƙika ba zan taɓa yafewa kaina ba.

naja gwiwoyina na ƙarasa gaban iyayen nawa na shiga basu haƙuri ina kuka sosai, amma cikin su babu wanda ya ƙara saurarata suka bar ɗakin jiki a sanyaye, a wannan dare ko bacci banyi ba sai salloli da nayi ta jerowa akan ubangiji ya yafe min ya kuma sanyaya zuciyar mahaifana, kamar yanda Ummana da Abbana basu sami yin bacci ba a wannan daren, domin kuwa ina jiyo sautin muryarsu.

maganar Baba ta katse tunanina lokaci ɗaya, na ware ido ina kallonsa kunnuwana na son tantance zantukansa.

“Shi yasa a kullum aka ce ka shuka alkhairi sai ka girbi alkhairi. Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:”Kunya alheri ce gaba ɗayanta.”, A wata riwaya kuma; “Kunya ba ta kawo komai sai alheri.” Buhari ne ya rawaito…to yanzu Bilki WA GARI YA WA YA?, tunaninki za ki yiwa Allah wayo?, ki yaɗa fasadi sannan ace ruwa tasha, ai inaaa dole kiga sakamako, kin zauna kinyi asarar lokacinki kin rubuta batsa kin yaɗawa duniya, ƴarki da kika haifa da cikinki taci karo da shi ta karanta, wanda har ta dalilin hakan take aikata istimna’i da maɗigo saboda koyarwar da kika yi, ga shi hakan ya janyo mata kamuwa da cututtuka da fasuwar aurenta, ke kina zaton Allah ya isan iyayen yara zata bar irin ku ne?, ko zaton ki su waɗanda suke karantawar basa bin ku da Allah ya isa?, idan fa mutum yay maka Allah ya isa direct take tafiya wurin ubangiji, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Bilki ta dalilin rubutunki fa tarbiyar ƴarki ta wargatse, tarbiyar da kika gina sama da shekaru ashirin da ɗaya an kawo lokacin da kin rusheta da kanki, ya za kiyi da sauran hakkin iyaye da suma ƴaƴansu suka faɗa irin wannan halin a dalilin karatun littafinki?, me zaki ce da ubangiji a sanda ya tsare ki da tambayar amanar da ya baki?, kaico! kaico da aurenki Bilki, wallahi Allah ɗaya ba zai taɓa barin irinku ba, dole hannayenku za suyi bayanin abinda suka rubuta a ranar lahira, ranar da komai ya ƙare muku, ranar da baku da wata madafa ta tuba, kaicon ki Bilki, kije kawai na ƙarashe sakin gaba ɗaya domin bana buƙatarki cikin rayuwarmu.”

“Kamar ya kenan Habibu?, wacca iriyar magana kake yi?, da wacca Bilkin kake ne?” kowa ya jefowa Baba tambayar a sanda ya nufasa yana dafe kansa da hannu biyu.

banda ni dana kasa ɗauke ido akan Ummana ina ta kallonta kamar yaune na fara ganinta, gaba ɗaya zallar mamaki da al’ajabi sun baibaye ni, da yaushe ta haifi ɗa me suna Auwal har ta zama Ummu Auwal?, ta ya akai Baba ya san itace marubuciyar littafan batsa a media wacca sunanta ya shahara a fannin rubuta iskanci, na shiga ukuna, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.

Kan Baba a ƙasa kamar zai yi kuka yace,”na gano hakan ne a safiyar yau lokacin da message ya shigo wayarta daga wajen fans nata akan cewa Ummu Auwal ina buƙatar novel ɗinki Yanayi, ki tura min details na account. dama tun a daren jiya na ɗau alwashin duk inda marubuciyar take sai na nemota an kaita hisba, idan sun kasa kuma mu garzaya ga kotu, ita ma idan ta kasa sai na bita da Allah ya isa ko hakan ya hanata sukuni da kwanciyar hankali tunda har ta zama silar gurɓacewar tarbiyar yarinyana”.

Baba na cikin magana ban san lokacin da na buɗe bakina ba ina girgiza kai nace,”Baba don Allah kace min ba Ummana ba ce, Ummana ba zata iya rubuta abunda Ummu Auwal ke rubutawa ba, Baba ita fa waccan Ummu Auwal ɗin media tayi mata tambarin ƴar iska, kusan kullum sai an zageta an tsine mata fa a groups ɗin da nake ciki, kuma wallahi ko mu da muke tunzura su zaginsu da tsine musu muke yi a bayan idon su, na shiga uku ni Mujahida, Baba Ummana fa ba ƴar iska bace, Ummana da na sani kullum nasiha take yi min akan zama mace ta gari, mace me kunya, kullum haka take cewa in ƙauracewa ganina da jina daga zina, domin haramunne, to ta ya kuma ita zata zama ita ce me yaɗa baɗalar da tarbiyar wasu zata lalace?, taya zata bi hanyar da ta san haramun ce?, Baba ba zan taɓa yarda Ummana ce ke rubuta irin wannan batsar ba da ake ji tamkar ana kallo ba, don Allah Baba ka taimaka min zuciyata zata harba, hasbunallahu wani’imal wakil,  innalillahi…”

Share and comment.*

1 thought on “Kukan Kurciya 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.