Na fara da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinƙai Allahu buwayi gagara Misali. Allah yanda Ka bani ikon fara rubutun littafin nan, Ka bani ikon kammala shi lafiya
GAISUWAR BAN GIRMA GARE KU
Princess Teema Star lady, Anty Surayya, Hafsat Boss Bature – ku na musamman ne a cikin zuciyata; ina ƙaunarku matuƙa. Mrs. BMB Anty Ummilolo, Mrs. BBK Anty Sadiya Kaoje, Mrs. Isham – kuma ina yin ku over. Sauran masoyana wanda ban faɗi sunayenku ba, ina miƙo gaisuwa lodi-lodi, gaisuwar ban girma a gare ku. Ina godiya sosai da shawarwari.
Iyayena, abin alfaharina, Allah ya ja min da ranku ya kara maku lafiya, amin.
*****
Littafin Kukan Zuci (Kaddara Ce Ko Son Zuciya), kagagge ne daga ni Fatima (Amyra), ban yi dan wani ko wata ba. Wanda ya ga ya yi daidai da rayuwarsa to arashun sani ne na yi saboda na kawo gyara a cikin al’umma ta hanyar fadakar dasu nishadantar dasu gami da Ilimantarwa.
GARGADI
Ban yarda wani ko wata ta juya min littafi ta ko wace sigar ba.
*****
Babi Na Daya
Kano
Unguwar Gadon Ƙaya
Zaune take ƙarƙashin bishiyar mangoro dake bakin wata makarantar gwamnati da botikin Masa (waina) a gabanta tayi tagumi tashiga duniyar tunani. Kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin damuwa. A shekaru bazata wuce 18 yrs ba.
Ƙafarta sanye take da silipas wari da wari wanda yasha ƙusa ba adadi se Hijabi wanda yazo mata har ƙasa baka ganin kayan dake jikin ta, baƙine Hijabin cotton me kyau wanda ta samesa tun last year (bara) da azumi lokacin da a kayi sadakar Hijabi a masallacin unguwarsu Allah yayi da rabonta ta samesa yaji jiki sosai Hijabin sedai kasancewar Hijabin mai quality ne yasa har yanzu be fara ƙurajeba amman yayi shara-shara tsabar shan wanki da rana.
Kalarta yellow color ce amman wahala da rana suka koɗar da ita suka maidata golden brown, kyakyawace tanada oval face ( wato Shape din kwai ) gata da manya manyan idanu farare kal se kwayar Ido brown me kama da baki me kyalli gashin gira kaman an zana ga gashin Ido shima kamar ta sanya eyelashes ga dogon hanci kaman karas har baka da dan karamin bakin ta wanda yake light pink color ga saje kwance a gefen fuskarta.
Duk da tana cikin damuwa hakan be hana bayyanuwar kyawunta ba. Ta yi nisa cikin tunani bata ankaraba taga students sun fara watsewa “Wayyo Allah na yanzu nafi awa da awanni ina jiran a tashe su ko zanyi ciniki a nan na baro kasuwa ba wanda ya siya nan ma haka Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji’un yanzu mezanje in cema Umma na shiga uku tun safe gashi yanzu kiran La’asar ake ban sayar da masa ko daya ba” Kallon sama tayi tace “Ya Allah ka kawo mun mafita” Jiki ba ƙwari ta miƙe tare da ɗaukan botikin masarta ta dora a kai ta kama hanyar komawa gida.
“Ƴammata ya kike” wani Dattijo ne dake zaune a ƙofar wani gida ne ya mata maganar “Lafiya lau baba” “Ƴammata akwai ta ɗari biyar da zumuɗinta tace “Eh akwai” “To zubamun kisamun manya manya” “Tohm” tace tare da tsugunnawa ta kirga masa ta ɗari biyar tasa a leda ta ɗan ɗago tace “a kai zan zuba maka ƙuli-ƙulin ko a leda daban?” “A’a mikon wainar ki zuba ƙulin a wata ledar bari in shiga gida in ɗauko maki kuɗin” “Tohm” tace kana ta mika masa ledar, amsar ledar yayi ya shige wani gate din gida.
Wata ledar ta dauko ta zuba ƙuli-ƙulin aciki ta kulle ta cigaba da tsugunnuwar jiransa tana murna tace “Yau dai Allah ya rufan asiri Umma bazata daken ba kuma zanci abinci koba komai na sayar da rabi” ta faɗi hakan da murna a face nata, Almost 10mins tana tsugunne a wajen tana jiransa ya kawo mata kuɗi ta bashi ƙulin ta wuce gida amma shiru shiru bai fito ba.
“Ke me kike a nan” wani dan matashi daya zo wucewa ya a ganta a gun dan gun nada hatsari duk kangwayene masu gate kaman gida amman ba gida bane ansha yiwa yara fyade kuma ba’a daukar mataki sabida kangwayene na manyan mutane ne, ‘yan ta’addar gurbatattun mutanen ne ke zama a wajen, yar firgigit tayi ta ɗago dara daran idon ta ta kalli saurayin san nan tace “wani baba nake jira ya kawon kudina in bashi Ƙulin sa” “Ina yayi?” Saurayin ya tambaya yana ɗan zaro ido “Ya shiga gidan cen” tayi maganar tana nuna masa gidan da dattijon ya shige “Innalillahi ke cen ba gida bane kango ne, kawai gate yakeda Kuma da wata kofar fita ta baya aiko ya gudu dan ba dawowa zeyi ba Allah yasa bame yawa kikasa masa ba, ki tashi kawai ki tafi gida dan zaman ki anan be dace ba Allah ya saka maki” ya kai karshe maganar tareda barin wurin yana latsa waya.
“Nah shiga uku na lalace rabin masa ɗin nan na zuba masa ta Dari biyar yanzu ni mezanje in fadama umma Innalillahi yau kashina ya bushe kasheni umma zata yi” ta kai karshe maganar tare da sakin matsanan cin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Seda tayi kukanta mai isarta taga ba wata mafita seta Allah sannan ta miƙe ta dauki botikin ta ta kama hanyar gida tana Sharar kwalla tana karanto duk addu’ar da tazo bakinta.
Abuja
Gwarinpa
9:30am
Matashiyar budurwa ce kwance saman makeken gado dake shinfiɗe da bedsheet na alfarma, dake cikin Katafaren ɗaki mai matukar kyau da girma.
Kai ganin ɗakin nan kasan an kashe dukiya mai matuƙar yawa aciki kai kace dakin wata, komai na dakin Glass ne duk inda ka juya inuwa na binka, akwai komai na furnitures da ake buƙata kama daga kan makeken gado mai girman gaske, bedside drawer guda biyu ta gefe da gefen gadon saman ko wane beside a kwai lamp.
Ɗan nesa da gadon wani tampatsetsen dressing mirror ne mai shaƙe da su lotions kala kala dasu body sprays da perfumes masu ƙamshi da kyau da tsada sai kayan makeup da sauransu komai a kwai akan mirror ɗinnan babu ne kawai babu. Gefen dressing mirror wani Showglass ne transparent wanda yake cike da Al-Qur’an nai da sauran littattafan addini daban daban.
Daga yamma ta cikin ɗakin wasu tagwayen kofane a wajen ɗaya na toilet ɗaya na wani haɗaɗiyar baranda (balcony) mai kewaye da flowers kala kala, launin Ja kore yello sai kamshi flowers ɗin ke zubawa kamar an musu feshin turare, daga gefen barandar wasu haɗanɗun kujerune kewaye a wajen da wata haɗaɗiyar table a tsakiyar su da alama wajen shakatawar mamallakiyar ɗakin ne kusa da waƴannan dankara dankaran kujeru wani hadaɗen swimming pool ne ɗan ma dai da ci mai ɗuuke da ruwa sky blue ga wasu kyawawan fitillu a cikin sa dake juyawa suna bata haske kala biyu blue da fari.
Ɗakin gauraye yake da fitilu masu hasken gaske, haske ta ko ina fitilun bangon sama (POP) na tiles na bango da jikin furnitures.
Daga saman kayin wan nan Katafare gadon wani haɗaɗen frame ne mai ɗauke da hoto mata 7 da namiji ɗaya sai wani babban mutun dake tsakiyar su wadda a kalla zai kai 43 to 45 years da alama mahaifin sune kyakkyawa ne dukkan su, san nan kuma kamannin su kusan ɗaya sai dai shi Baban nasu golden colour ne su kuma Yellow namijin ne ya dauko mahaifinsu a komai. Se wasu mata su biyu daya bazata wuce 30 to 35 yrs ba dayar kuma bazata wuce 35 to 40 yrs ba se kuma wata tsohuwa wacce ke mugun kama da mahaifinsu da’alama ita ta haifesa ( Family picture ne ) se wani hoto a gefen sa jarirai ne su uku da’alama ‘Yan uku ne dukkan su suna sanye da pink din Kaya wani hoton daga ɗan gefe shi ma jaririya daya a hannun baban da alama ranar suna ce, daga ɗan saman wayan nan hotonan wani katon hoto ne a wajen da alama cikin larabawa akayi hoton dan ba ƙasar nan bace wata matashiyace da bazata wuce 14 to 15 yrs ba sanye take cikin doguwar riga fara ta dora rigar graduation da hula se murmushi take dimples dinta ya lotsa da alama graduation dinta ne rike take da wani katon Medal ( gift ko ince Award).
Medal din school ne da tambarin school din ajiki kana gani kasan ba karamin kudin ne wannan medal din ba, glass ne me kauri Milk color da Star gold a tsakiya se a ciki akayi rubutu da golden colour kamar haka:
Award of Excellency
To
Aliya ( Mufeeda) Ishaq Bello
For being the most talented student this school has ever had.
Gefenta wani kyakkyawan dan saurayine sanye yake da kakin sojoji da hula baze wuce 19 to 20yrs ba, fuskarsa a ɗan sake amman ba murmurshi yake ba a jikin kakin an rubuta CPT Aliyu Haydar I.B.
Daga ta waje cikin nitsuwa a kayi knocking na kofar ɗakin, wani glass ne ya zuge ta kasa wata mata ce ta hauro ( Underground ) tashigo ɗauke da sallama a bakinta, kallo ɗaya zaka mata kasan mai aiki ce.
Sum sum matar ta ƙaraso bakin makeken gadonan ta tsugunna kamar mai tsoron wani abu ta bude baki a hankula ta furta “Mufy Mufyy Mufyyy” shiru ba alamun zata farka, hannu takai ta ɗan bubbugi gadon cike da tsoro. A hankali mufy ta fara mutsu mutsu alamun zata farka da sauri matar nan tayi baya, hannu takai ta tattare gashin daya rufe mata fuska tana yatsina fuska alamun bacci bai isheta ba, Ma Sha Allah Tabarakallahu Ahsanal Khaliqin.
Tsayawa zayyana maku kyauwan matashiyar nan bata lokacine duk da daga bacci ta tashi hakan bai hana bayyanuwar kyawunta ba tanada Oval face (wato shape din kwai) gatada pointed nose da manyan idanu ga sajen gefen fuska ya kwanta luf kai kace ‘yar larabawa ce, dan karamin bakinta light pink dashi kamar ta shafa lip balm.
Salatin Annabi tayi sannan ta bude wannan Idanun nata wanda rabinsu a lumshe shuke biji biji take ganin Luba wacce ke tsugunne nesa da gadon, ahankali ta bude bakinta tace “mene” cike da fargabar ta tashe ta Luba tace “da.. dama… daman kekika ce in 9:30 yayi baki tashi ba a tashe ki shine…..” Feed ta katseta da cewa “naji Abbo na nan?” Sauke ajiyar zuciya Luba tayi ganin batayi laifi ba ta bata amsa “a’a” “twin bro fa?” “Shima ya fita” “sisters fa?” “duk sunanan banda twins da auta sun tafi school yau zasu kammala exams” “oky you can leave” cikin sauri ta miƙe tana faɗin “a fito lafiya” ta kai karshen maganar tare da kama hanyar fita, har ta kai bakin benen feeda tace “Daada na ina?” tana lambu” shiru feeda tayi ba tare da ta sake magana ba ta mike ta shige toilet tana kwaɓe fuska.
Fice wa luba tayi ranta tana yaba hali irin na feeda duk cikin ƴan uwanta itace ta daban mai son ƴan uwanta ga biyayya da kyautata wa bata da girman kai ko kadan ga Ilimi both addini dana zamani sabanin ƴan uwanta hakan yasa mahaifinsu ke ji da ita duk da ba itace auta ba ba kuma ‘yar fari ba.
Amma idan ran Feeda ya baci ran mutum in yayi dubu seya baci sejiki ya gayama mutum da akwai ranarda Hajiya Babba ta taba kwada mata mari akan ta mari Dan kanwarta Dan ya rike mata hannu aiko ranar jikinsu ya gaya musu dan bade musu Ido tayi ta ringa masu ruwan kunama taki sakinsu ga Haydar wanda takejin maganarsa bayanan Abbo ma haka haka kunamu suka dunga illatasu suna ihu amman ba mai cetarsu su twins da auta sun roka har su hakura yayyunta suna makaranta Daada ma lokacin taje garinsu Seda ta masu likis sannan ta ta batar da kunamun kana ta sakar masu idanu taki taba inda kunamun suka cijesu tace sunema ma kansu magani. Aiko sunfi sati suna Jinya.
Khamilarh
Gudu gudu sauri sauri take tafiya da botiki a hannunta da’alama daga gurin markaɗe take Dan duk botikin a ɓace yake da kullin gasara. Bazata wuce 18 yrs ba.
Matashiyar kyakyawace ajin farko duk da wuya da azaba da take sha be hana kyanta fitowa ba tanada oval face ( wato shape din kwai ) da manyan idanu farare kal da kwayar Ido brown me kama da baki me kyalli ga gashin gira kaman an zana ga gashin Idon Shima hanci har baka kaman karas Ma Sha Allah se dan karamin bakinta light pink ga saje kwance a gefen fuskarta tana tafe tana ‘yan wake wakenta wanda hakan yasa wushiryarta bayyana ga dimples dinta na lotsawa.
Sanye take da farin Hijabi wanda wuya da datti da wahala suka maidashi brown color ( ruwan kasa ) dai dai gwiwarta yake see wani koɗaɗɗen zani daure a kugunta kasan zanin duk ya ciccinye yayi laushi tsabar wuya.
“Milarh! Milarh!!” A ka kirata daga bayan ta, Juyowa tayi don ganin me kiranta “La Humaira kece” ta faɗa tana ɗan murmushi “dole ki tambaya ai tukunnama meya hanaki zuwa Islamia jiya?” Nan take ta ɗan kwaɓe fuska tace “Wallahi Inna ce ta amsa kudin Islamiyyar daren ta bama Safina ta sayo fura” “Ina Baba yake ta amsar maki kudi?” “Ke bayanan lokacin” “Muguwa in ta Isa ta amsa kudin lokacin da baba yake nan mana, ina kuɗin da muke tarawa idan ya Habeeb ya bamu Da kuɗin kwalaye da ƙarafunan da muke sayarwa?” Tayi tambayar dai dai lokacin da ta kariso dab da milarh ɗin, Ɗan jinjina kai milarh tayi kafin tace “Suna nan” milarh ta bata amsa “To meya hanaki dauka ki taho Islamiyar?” Zaro ido waje milarh tayi kafin tace “So kike taga na fito da kudi tace ina mata sata, ko tace bin maza nake na samu kuɗin? Kina tunanin in ta ganni da kudi bazata am she su ba?” “A’a milarh amman dai….” “Amman dai base kince komai ba ya wuce In Sha Allah anjima Zango Islamiyyar Allah yasa ba’a maku dori ba” “Eh ba ayi ba Allah ya so ki jiya malam habu bai zo ba muraji’a kawai mukayi” ɗan murmushi milarh ta saki kafin tace “Allah na gode maka, ina zaki haka?” “Gidan ku mana ya Habeeb ne yace inzo inji dalilin daya hanaki zuwa makaranta” Humaira ta bata amsa “Tohm muje mu karasa gida kafin Inna tace na tsaya Iskanci” cewar milarh “Wallahi ba inda zani dabadan ya Habeeb ya matsaba da ba abunda ze kaini gidanku wannan matar me idon mujiya duk abunda take maki In Sha Allah akan ‘ya’yanta ze kare…..” Bata kai karshen maganar ba milarh ta tari mumfashin ta da cewa “Ya Isa tunda bazaki ba anjima inna samu sarari zanzo inyi Karatun DUK KARFIN IZZATA” hararar wasa Humaira ta mata kafin tace “Tohm shikenan kinma tunamun banyi karatun update na jiya ba bari in tafi” girgiza kai milarh tayi tace “In kin ga dama in kin gama karatun ki goge yadda kikamun rannan na haddace number din sister Amyra message kawai zan mata ta turon daga inda na tsaya” “Bazan ma goge ba ai ranar batan rai kikai shiyasa” cewar Humaira “kyaji dashi” Tasss Humaira ta daka mata duka a baya ta ruga a guje tace “Ladan kin zuwa makaranta” kwafa milarh tayi tace “Zan kama kine ni wanda zan maki ma seyafi wanda kikamun” ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi hanyar gida ita ma Humaira ta wuce ta koma in da ta fito.
Khalilarh
Wani dan gidane na masu rufin asiri dan ba za’a kirashi dana talakawa ba da akwai yar kofa ta katako a gidan, ba fenti gidan se siminti da gidan yasha ta ko ina yazama ash colour ( Ruwan toka ) cikin gidan Khalilarh tashige da sallama dauke a bakinta.
Matsakaicin tsakar gidane me dan fadi se wasu kofofi guda biyu da’alama dakunane wanda windows dinsu keta cikin tsakar gidan se bayi acen gefe wanda buhu ne ƙofar sa se wata rijiya, da kuma wajen girki inda yake kewaye da langa langa samansa a bude, cikin gun duk toka se itace wanda suka fara zama gawayi se tukwane da tandar masa ( kaskon soya waina) da kwando wanda yake dauke da kwanuka da sauran su.
Ba kowa a tsakar gidan ko ina kaca kace ga uban wanke wanke dake tare gefe guda, hamdala Khalilarh tayi tare da a jiye bokin masar a gefe tace “Allah ya so ni su Umma basa nan dana yaba ma Aya zakinta” bakin rijiya dake tsakar gidan ta karasa taje ta janyo ruwa tayi alwala tazo kan tabarmar dake shinfide a gefen window ta tada Sallah a nitse tayi Azahar da La’asar.
Bayan ta idar ne ta mike ta cire Hijabin ta ɗora a kan window dake bude ta linka tabarmar biyu ta shige cikin wajen girkin ta dauko ashana ta hada murhu ta ɗora dumamen tuwon ta da bata cinye jiya ba. Wani botiki ta bude “Alhamdulillahi kullin ya tashi bari inyi sauri kamun su dawo in fita da kayan suyar” ta fadi tana rufe boktikin ficewa tayi daga gun girkin ta dauki tsintsiya ta share tsakar gidan tas san nan tazo ta zauna taci tuwonta sharp sharp ta cinye ta mike da sauri sauri tayi wanke wanke tukwane uku wanda suka kama ga maiko ba’a jiƙa suba suta jiƙa ta mike ta kwasa kayan ta kai su mazaunan su.
Hijabi ta saka ta fara dibar itace da sauri ta kai kofar gida ta hura wuta da kyar ta kama sabida iskar da’akeyi da alama ruwa za’ayi tanda (kaskon suya) ta dauko tazo ta dora akan wuta san nan ta koma cikin gida baking powder da sugar da gishiri ta dauko tazo ta auna ta zuba acikin kullin ta ɗauki muciya ta juya san nan ta ɗauki ludayi tasa a cikin kullun ta dauka tayi waje, taje ta ajiye kusa da murhun suyar nata san nan ta koma cikin gida ta ɗauko mai da botikin masar data tafi talla da shi ta ɗauka da kujerar tsugunne ta dawo kofar gida ta zauna ta fara suyar wainar ba jimawa aka fara kiraye kirayen Sallah Mangrib, ana idar da Sallah aka fara layin siyan Masa biyu hamsin.
Wani matashin ne yazo a mashin da gilashi a idonsa ya saka face mask kuma ga duhu baka ganin fuskarsa yazo ya sayi ta Dubu daya ya bata Dubu biyu taki amsa seda yace mata kudin tsohonnan ne daya sayi masa tace ai 500 yace to sadaka ya bata sauran amsa tayi tamasa godiya ya buga mashin na shi ya tafi. Haka tayi ta ciniki yau Kamin Isha’i kullin ya kare gashi su inna basu dawo ba farinciki kaman ta zuba ruwa a kasa tasha. Haka ta tattara kayanta takoma cikin gida Ana kiraye kirayen Sallar Isha’i.
Alwala tayi tayi Sallah mangrib da Isha’i san nan ta yi wanke wanke.
Kan tabarma ta koma danyin lissafi 5000 ta ware daban tace “kullin botiki” Ta sake cire 1000 tace “masar talla” sauran chanjin ta kirga 950 “Allah na gode Maka” ta fadi, tare da mikewa ta nufi daki da 950 din. Jim kadan ta dawo kan tabarmar ta hade kudin wuri guda “Alhamdulillahi kuɗin sun cika yau darabon inyi bacci kai amman Allah yayi ma bawan Allah dinda ya bani Dubu daya Albarka yanzu da ban amsa ba yaya zanyi?” Haka tayi ta surutanta har ta fara Hamma, Kulle kuɗin tayi a gefen zanin ta ta dukunkune a gefe guda tare da kwanciya saman tabarman nan take bacci yayi awon gaba da ita.
Tana kwance a tsakar gida tana sharar baccin ta har ɗaurin data ma kuɗin ya kwance. Wani matashi ne ya shigo gidan da sallama ƙasa ƙasa yazo diban ruwa be kula da ita ba ya nufi rijiya yaja ruwa ya cika botiki ya dauko ze fita karaf idanunsa suka sauka akan kuɗin nata da suka kwance, dire botikin yayi cikin sanɗa ya karaso gunta ya dau kuɗin ya koma ya dauki botikin da sauri ya fice daga gidan.
Mufeeda
Almost 40mins ta dauka kafin ta fito daga toilet da bathrobe sanye a jikin ta, ƴar dogowa ce ba laifi ba kuma gajera ba, gashin kanta a jike kwance har gadon Bayan ta da’alama wanke kan tayi ga manya manyan Idon farare kal se kwayar Ido brown me kama da baƙi me kyalli ga dogon hanci har baka se dan karamin bakinta light pink kaman ta shafa lip balm.
Gaba mirror ta karasa wani botton ta danna wata kujera ta fito ta ƙarƙashin mirror zama tayi cikin nitsuwa ta fara shafa lotions dinta masu kamshi da kyau da tsada, bayan ta kammala shafa lotions ɗin ta feshe jikinta da body sprays Kala Kala ta Kara da humra nan da nan dakin ya dau kamshi.
Dryer ta dauko a drawer din mirror ta kunna ta busar da gashin kanta ta shafa mayuka san nan ta ɗaure gashin da baƙin ribon, batayi makeup ba lip gloss kawai ta shafa bayan ta kammala komai ta tashi ta shiga dressing room Jim kaɗan ta fito sanyeda wando Palazzo baƙi da white top se black boyfriend jacket da dan ƙaramin mayafi ta dora akanta ta danyi rolling dinsa.
Gadon da ta tashi ta Kaɗe ta gyra ta dau wani machine na shara ta share dakin tare da yin mopping tas ta dau air fresheners ta fesa Kala Kala kana ta chanja takalmi tasa wani flat shoe baki ta dau wayarta *Samsung Galaxy S22+* ya fice ta kofar underground dinnan.
Khamilarh
Gidane wanda ke daukeda mata hudu amma Allah yayi wa matar ta uku rasuwa wajen haihuwa yaran na zuwa duniya Allah ya mata rasuwa ( ƴan biyu ne yaran mace dana miji) Yara takwas maza uku mata biyar ɗakuna Bakwai se matsakaicin tsakar gida da toilet guda daya se dan karamin Kitchen.
Da sallama dauke a bakinta ta shigo gidan Uwar gida ( Larai ) wacce suke Kira da inna itace zaune akan tabarma wacce da ita da babu duk kusan daya tana kulla goro da gyada a leda da alama sana’ar ta kenan. Mai bin Uwar gida ( Lami ( ƴar uwar mai gidan) wacce suke kira da Umma tana gindin murhu da’alama ita ke girki se Amaryar (Maryam) wacce suke kira da Inna Mairo tana surfen gero a turmi. Ba wacce ta amsa mata sallama a cikin su se inna Mairo daman su tasan ba amsa mata zasuyi ba inda sabo ta saba. Gun Ummi ta karasa ta duka ta ajje markade tace “Ummi na dawo…” bata bari ta karasa maganarba ji kake tass ta kwashe ta da mari, A fusace Inna ta karaso gun ta tace “haba Larai mene haka me ta maki wannan wane irin zalunci ne wallahi duk abunda kuke ma baiwar Allah dinnan se Allah ya saka mata haba kuma fa kunada ƴayannan ya zakuji in akama naku haka? Itama tana da nata iyayen fa Kaddarace ta faɗa kanta Allah ya hadata da malam ya kawota nan gidan” tsaki Ummi taja sannan tace Mairo ki fita a sabgata ki dena shiga gonata akan wannan marar asalin tsintacciyar zaki na gayamun magana sa’ar kice ni? Ko ko matsayin mu daya?” Inna ta amshe da cewa “Kin min dai na so duka kika laka dama shegiya aikin banza ke kuma Mairo me hadinki da ita da kike shish shige mata? Da kike maganar tanada iyaye suna ina wayasan ta wace hanyar suka haife ta ma…” haka Inna da Ummi sukayi ta masifa da fada da zagi ta inda suke shiga ba tanan take fita ba Inna Mairo ta kama Milarh ta kaita dakin su tace tayi hakuri In Sha Allah Jin daɗinta na gaba ta fice ta koma surfenta tashi Ummi tayi ta je kofar dakin tace “wallahi kika Kara minti daya baki fito kinmun tata ba sena lahira ya fiki Jin dadi” jiki ba kwari da sauri sauri ta fito ta shiga dan wani karamin dakin girki wanda ajjiyar kwanuka kawai suke dan ƙanƙantar gun bazeyi girki ba Jim kadan ta dawo da tsumman tace kullin da tukunya ta fara tatar kulli gasara.
Tana cikin tatar kulli Baba ya shigo gidan dauke da sallama a bakinsa da leda a hannunsa amsa masa sukai Mairo ta shiga daki ta dauko tabarma mai dan dama dama ta shimfida masa zama yayi sannan ya kalli khamilarh dake tata ba hawaye a fuskarta amman KUKAN ZUCI take da ka ganta kasan tana cikin damuwa Allah kadai yasan meke damun ta.
“Milarh Albishirinki” tayi nisa cikin tunani batama lura da shigowar baba ba balle maganar dayake mata “Khamilarh lafiya tunanin me kike kin manta Alkawarin da kikai mun?” Firgita ta dawo daga duniyar tunani tace “A’a Baba” “to tunanin mekike?”
Duniyar da kai tayi tace “ba komai” “Ajje tatar nan ki biyoni ki rakani wani gu” “to Baba” “Malam bangane ta ajje aikina ta raka ka wani gu ba, to ba inda zata in me raka ka kake nema ka nema a cikin ƴaƴan ka amman ba Shegiya tsintacciya ba” Ummi ta fada Inna ta amshe da cewa “kai ko kunya bazakaji ba duk yawan ƴaƴan da Allah ya baka ka rasa dawo zaka fita se Shegiya tsintacciya? Ita dai Mairo da ta zuba musu Ido tana jiran hukuncin da malam ze dauka dan tafi kowa sanin yafison Khamilarh akan kowa dan amanace a wajen shi bude bakinsa yayi yace Ni Malam Garba Bello Malami na.
*****
Toh masu karatu sai mun haɗu a babi na biyu. Ku suburbudo mun comments yadda zan ji dadin sako maku long pages in sha Allahu.
Just Amyra
Masha Allah, wannan littafin yayi muna godiya Allah ya ƙara basira da zakin hannu. Next pls Allah yasa malam ya ce ya sake su
Kukan zuci
Masha Allah