4 OKTOBA
Ba wai tsari da yanayin kotun, mutanen da suka halarceta suka damu da su ba. Al'amuran da shari'ar da za a gabatar ke xauke da shi, suka sanya jama'a yin dafifi zuwa kotun. Hakan kuma yana nuni ne da cewar ko ma a ina za a gabatar da shari'ar to haqiqa mutanen za su halarta.
Kotun ta wadata da al'umma, 'yan sa ido da 'yan kallo, daman ba a rasa 'yan jarida da 'yan ba-ni-na-iya a irin wannan abu, don shaidawa tare da samun amsar tambaya guda xaya rak, wadda. . .