Skip to content
Part 2 of 6 in the Series Kushewar Badi by Kabiru Yusuf Fagge

4 OKTOBA

Ba wai tsari da yanayin kotun, mutanen da suka halarceta suka damu da su ba. Al’amuran da shari’ar da za a gabatar ke xauke da shi, suka sanya jama’a yin dafifi zuwa kotun. Hakan kuma yana nuni ne da cewar ko ma a ina za a gabatar da shari’ar to haqiqa mutanen za su halarta.

Kotun ta wadata da al’umma, ‘yan sa ido da ‘yan kallo, daman ba a rasa ‘yan jarida da ‘yan ba-ni-na-iya a irin wannan abu, don shaidawa tare da samun amsar tambaya guda xaya rak, wadda ta gagara samuwa a tare da duk wani mutum dake faxin jihar Kano da qasar Najeriya baki xaya.

Almustapha, Lajja, Albashir, Alhaji Hammad, Alhaji Zuhairu da sauran makusantansu babu wanda bai halarci zaman kotun ba. Kowanne vangare yana tare da lauyoyinsa da hujjoji gami da shaidu. Kowannensu yana da tabbacin nasara.

A lokacin da Alhaji Hammad ke ta xokin ayi-ayi a fara gabatar da shari’ar a vata lokacin da za a vata a mallaka masa matarsa, don hankalinsa ya kwanta, ya koma qasarsu da matarsa – Su kuma, su Almustapha, Lajja da Albashir suna jira ne a zauna a gabatar da shari’ar, a tabbatar musu da tavin hankalin Alhaji Hammad, kamar yadda suke zato – ko kuma a tona asirin da yake voye da shi, wanda yake son cutar da su, su ci gaba da harkokin gabansu.

Mai shari’a Mahdi Alyasa’u qwararre ne, fitacce, kuma sananne a vangaren gabatar da shari’a. Halayyarsa da ta kasance daban da sauran alqalai, waxanda ma sun fi shi qwarewa, shi ya jawo masa samun waxancan matsayi. Tsarinsa ne duk tsauri da girman shari’a baya yi mata zaman da ya wuce xaya ko biyu. A zama xaya yake qoqarin kammala shari’a – idan ta yi tsananin tsauri to sai ya yi zama biyu zuwa uku musamman idan da duk shaidun da ake buqata, amma ba ta haura haka yake yanke hukunci.

Yana yin shirye-shirye da tanade-tanade ga dukkan shari’ar dake gabansa. Yana da qwaqwa da bin diddigi a kan shari’a da al’amuran dake tattare da ita. Hakan yana taimaka masa ya gano gaskiyar al’amari, ya fahimci gaskiya, ko ya sunsuno qamshinta.
Haka nan Allah ya hore masa hikimomi da basira waxanda yake amfani da su yayin gabatar da shari’a. Wannan shi ya fi baiwa mutane mamaki. Kuma sukan bambanta shi da sauran alqalai. Sannan kuma yana da ji da kansa. Kuma yana da qoqarin kaucewa duk wani kuskure da zai ratsa cikin harkokinsa.
Mutane na ganin za a yi ta ta qare.

Barista Mahbub Ibrahim, qwararren lauya, shi ne lauyan Alhaji Hammad, shi ya fara karanto hujjojin vangarensu a game da qarar, bayan alqali ya ba su dama.

“Alhaji Hammad mutumin qasar Masar ne. Tun yana xan shekara goma sha tara da haihuwa suka fara soyayya da matarsa Lajjanatu, wadda a nan suka Hausantar da sunan nata suke kiranta Lajja. Sun yi tsantsar soyayya, daga bisani suka yi aure. Matsala ta shiga tsakaninsu a lokacin da auren nasu bai daxe ba. Matsalar da suka fuskanta kuwa ta sava da al’adun qasarsu, don haka sai wannan abu ya tilasta musu rabuwar dole, rabuwar da xaya daga cikinsu bai zaceta ba kuma rabuwar da suka yi tsananin baqin ciki da takaicinta, rabuwar da babu saki a tsakani. Lajjanatu ta bar qasar tasu (Masar) ta koma Saudiyya, saboda gaza jurewa baqin cikin da ta ke ciki. Haka shima Alhaji Hammad, saboda so da qaunar matarsa ya kasa jurewa, ya kuma qudiri niyyar fatali da abin da al’adarsu ta shimfixa, ya karkata ga ainihin kyakkyawar shimfixa, managarciya, wato shimfixar addinin Musulunci. Ya fito neman matarsa. Bai sameta a Saudiyya ba, amma ya samu labarin cewa baqin ciki da takaici sun hanata zama a can Saudiyyar, don haka ta biyo wata mata zuwa nan qasar Najeriya. Haka shima ya biyo bayanta.

Kwanci tashi da taimakon Allah sai ga shi ya ganta a wannan lokaci.

“Don haka ya mai shari’a wannan da ragowar shaidu haxi da hujjoji, musamman idan mai shari’a ya buqata, su suka tabbatar mana wannan mata, mallakar Alhaji Hammad ce halak malak, akasi ne kawai ya gifta, ta bar shi, kuma ta bar shi ba don ya kamata ta bar shi xin ba.”

Barista Mahbub ya yi gaisuwa ga mai shari’a, kana ya zauna.

Lauya Idris Hashim mai kare waxanda ake qara, Lauyan Almustapha ya miqe, ya zayyano tarihi, bayanai da al’amura, tun daga haihuwar Lajja, rayuwarta tana qarama, girmanta, karatunta, soyayyarta, aikinta, rayuwar aurenta da zamantakewarta da maigidanta Almustapha. Kana ya zauna.
Bayan nazartar bayanan da lauyoyin suka kawo a taqaice, tare da yin xan taqaitaccen rubutun da ya lamishe aqalla mintuna uku, kana mai shari’a ya dubi Barista Idris Hashim.

“Bayan saurare da jin bayanan da duk ku ka gabatar, kotu kuma za ta saurari hujjoji, musamman daga gareka.”

Barista Idris Hashim ya sake miqewa.
” Allah ya taimaki mai shari’a, bayanaina suna xauke da bayyanannun hujjoji. Sannan ita kanta Lajjar shaida ce akan hakan. Sai kuma mahaifiyarta, sannan akwai uziri na rasuwar mahaifinta tun tana qarama, akwai mutane guda uku da suka san rayuwar mahaifanta da rayuwarta, saboda a gabansu aka haifeta, a gabansu ta rayu, kana kuma akwai takardu waxanda suka haxar da takardar haihuwarta, takardun karatunta, da kuma katin shaidar zamowarta cikakkiyar haifaffiyar qasar nan.” Ya xan tsahirta, kana ya ci gaba.

“Allah ya taimaki mai shari’a, a bisa waxannan hujjoji da shaidu ina gani waxannan mutane masu qara, sun zo wa da kotu wani ruxani ne, wanda a zahiri babu abin da suke ikirari, zan so mai shari’a ya yi watsi da wannan qara (shari’a).” Bayan ya miqawa alqali kwafin takardun, kana ya zauna.

Alqali ya baiwa Barista Mahbub dama, ya miqe.

“Allah ya taimaki mai shari’a, kafin in ce wani abu zan fara amfani da wannan dama in ja hankalin kotu da ta duba waxannan maganganu da Barista Idris ya yi ta gargaxe shi domin nan gaba ya daina kafa hujja da abubuwan da sam ba hujja ba ne, kuma ta ladabtar da shaidun togiyar da yake tunanin shaidu ne, musamman idan ya gabatar dasu. Mun riga mun sani cewa idan har ita Lajjanatu ta zama shaida, to wannan zai iya zama abin da muke da tabbacin faruwarsa kenan, domin a bisa la’akari da tsabar baqin cikin da take ciki gami da yanayin al’adar garinsu hakan sassauqa ne.

“Sannan kuma wasu mutane da kuma wasu takardu da yake magana ai wannan tuni ya zama tsohon yayi a vangaren shaidu, an riga an san an qware wajen yin jabu. To amma idan har kotu ta bashi dama to ya gabatar da su ni kuma zan nuna na jabu ne.” Barista Mahbub ya yi shiru yana kallon mai shari’a.
Mai shari’a ya baiwa Barista Idris damar gabatar da shaidun nasa.

Barista Idris ya gabatar da Lajja a matsayin shaida ta farko. Lajja ta fita zuwa xan mumbarin shaida, mai gaskiya ko marar gaskiya, ta tsaya, ta yi rantsuwar faxar gaskiya.

Barista Mahbub ya dubi Lajja.
“Baiwar Allah ki sani ke Musulma ce, kuma kin san bayan wannan shari’a akwai wata wadda za a yi a gaban Ubangiji Allah. Muna son ki yi qoqari don kaxaitar zatin Ubangijin da ki ka rantse ki ka yi imani dashi, ki faxawa kotu gaskiya don kar ki wahalar da shari’a. Shin kin tava yin aure kafin ki auri Almustapha?”

Takaici ya ishi Lajja. Hawaye ya cika fuskarta,. Amma cikin wannan hali ta yi qoqari ta shaida wa kotu ita ba ta san wata qasar Masar ba in ban da a labarai daga bakunan jama’a, haka nan kuma bata tava zuwa ba. Ba ta tava yin aure ba face mijinta Almustapha da ta aura – shi kaxai a duniya, kuma shi ne mijinta kaxai a yanzu da nan gaba. Ba su tava yin husumar da har za ta yi fushi da shi ta yi yaji, ko ya saketa ba. Ba su tava rabuwa ba. Ba ta san wani xa namiji a rayuwarta ba, face Almustapha!

Barista Mahbub ya yi murmushi. “Bai kamata ki fara da kuka tun yanzu ba. Saboda yanzu aka fara tambayoyin!”

Faxin hakan ya qara ba ta haushi.
Ya ci gaba. “Kin tava zuwa Saudiyya?”
Gabanta ya faxi! Kuskure! Koda yake ko kaxan Lajja ba ta xauki wannan a matsayin kuskure ba, musamman game da wannan shari’a. Ba shakka idan ba ta manta ba a lokacin da tana ‘yar shekaru goma zuwa goma sha biyar. Ta manta shekarun! Sun je Umra ita da mahaifiyarta. Kuskuren da take ganin ta yi kuma har ya sanya gabanta faxuwa shi ne ta yadda bata tava gayawa kowa faruwar wannan tafiya ba, hatta Almustapha ma bai tava sanin ta je Saudiyya ba. Illa iyaka dai waxanda aka yi tafiyar a lokacin suna nan, suka kuma san da tafiyar to sun sani, amma bayan haka duk wanda ya san ta bai san zuwanta Saudiyya ba, sai dai idan wani ne ya faxa masa, amma ba ita ba ko mahaifiyarta wadda suka yi tafiyar tare.
Kuma hakan ta faru ne ta dalilin hanata faxawa kowa da mahaifiyarta ta yi. Ba ta kuma san dalili ba.

Cikin kotun ya yi tsit!
Almustapha da Lajja suka haxa idanu. Wani yanayi ta gani a cikin idanunsa, hakan ya tsoratata matuqa.

“Na….tava!” A taqaice ta faxa, a liqe a cikin muryarta akwai alamun rawa.

“A wane lokaci? Ku nawa ku ka je? Kuma ku nawa ku ka dawo?” Ya jeranta mata tambayoyi uku a lokaci guda.

“Ba zan iya tuna lokacin ba. Amma dai mu biyu ne. Ni da mahaifiyata, muka je, kuma mu biyun muka dawo.”

Shiru na daqiqa bakwai.

Barista Mahbub ya miqa mata wata takarda. Takardar ta haihuwa ce, wadda ke xauke da hoto da kuma sunanta, sai dai akasin yadda ta san sunan; Takardar ta Masar ce, mallakar haihuwar can ce, an rubuta sunan kamar haka: Lajjanatu Ums-Khairy.

“Kin san wannan?” Ya tambayeta.
Ba wai takardar da aka nuna ta sani ko tambayar da ya yi mata ne suka bata mamakin da ya yi hanzarin bayyana a fuskarta ba. Hotonta da ta gani tana jaririya kamar yadda ta san ire-irensu kuma take da kalar shi. Shi ya fi ba ta mamaki kuma ya xaga mata hankali, haka siddan ta ji jikinta na rawa, wanda kuma ya sanyata dole ta jefar da takardar daga hannunta, a tunaninta takardar tana da nasaba da sanya jikinta yin vari.

Barista Mahbub ya kalli Lajja a taqaice, a lokacin da ya mayar da kallon nasa ga takardar, ya xauketa, ya dubeta a taqaice kamar mai yin nazarin wani abu a tattare da ita, daga bisani kuma ya miqawa alqali takardar. Ya juya ga Lajja.

“Mene ne asali da kuma tarihin wannan suna naki? Domin sam bai yi kama da sunan Hausawa ba, kuma ba su da wata dangantaka.”

Kafin Lajja ta yi magana Barista Idris ya miqe gami da katsar hanzarinta.

“Allah ya taimaki mai shari’a wannan ba ta cikin irin tambayar da ya kamata a yi.”
“Bar shi ya gama.” Cewar alqali.

Barista Mahbub ya yi murmushi. “Malama Lajjanatu muna sauraronki.”

Lajja ta girgiza kai. “Ba daidai ka ke faxar sunana ba. Sunana Lajja. Kuma game da tambayarka; mahaifina wanda Allah ya yiwa rasuwa tun wani lokaci can baya da ya shuxe shi ya raxa min wannan suna kamar yadda yake a al’adar duk wani Musulmi.”

Ya juya ga mahaifiyar Lajja, tamkar bai damu da amsar da Lajja ta gama ba shi ba.

“Malama Mariyatu, ke mahaifiyar Lajja ce?”
Tambayar ta ba ta mamaki, kuma ta zo mata a matsayin rainin hankali. A cikin idonta take ganin Barista Mahbub a matsayin mai rainawa mutane wayo, mara tarbiyya. Ta jure don ta ba shi amsa kasancewar a kotu suke.
“Qwarai kuwa, ni mahaifiyarta ce.”

“Mene ne zai iya ba mu tabbaci?”

Takaicinta ya qaru, “Allah shi ne shaida.”

Ya kawar da kallonsa gareta. “Me ku ka je yi Saudiyya ke da Lajjanatu?”

“Ban je Saudiyya da wata mai suna Lajjanatu ba.” Ta ba shi amsa daidai da tambayar rainin wayo da ya yi mata a ganinta.
“Ma’ana Lajjar da ku ke faxa mata.”

“Umra muka je.”

“Ku nawa kuka dawo?”

“Biyu.”

Ga yadda take bayar da amsa duk mahalarta kotun sun fahimci a kufule ta ke.

“Wane ne ya sa mata wannan sunan?”

“Ni ce.”

“Saboda me?”

“Sha’awa.”

“Mene ne tarihi da asalin sunan? Kuma daga ina aka samo shi?”

Shiru, babu amsa. Kotun ma kowa ya yi tsit!
Barista Mahbub ya dubi alqali. “Allah ya taimaki mai shari’a ba na buqatar wasu shaidu a gaba, domin bisa waxannan tambayoyi da na yiwa shaidun Barista Idris da amsoshin da aka samu daga garesu sun isa baiwa kotu damar ci gaba da nata aikin. Don haka idan kotu ta ba ni dama zan gabatar da nawa shaidun.”

Kotu ta ba shi dama.

Mahaifan Lajjanatu Usm-Khairy da Khulsum, Barista Mahbub ya fara gabatarwa. Misirawa ne, ba sa jin harshen Hausa ko kaxan, daga Larabci sai yaren gado wanda suke kira barba (Berbar) suke ji.

A lokacin da aka shigo da su kotun, da yawan mutane kusan dukan jama’ar kotun sun yi musu maraba da ido, to suma kuwa baza idanunsu suka yi, suna kallon al’ummar kotun xai xai. Ganinsu ya kai ga Lajja kusan a tare tamkar maganaxisu. Ximuwa da tsananin mamaki ne ya janye zukatan su Usm-Khairy da Khulsum zuwa gareta.
Khulsum ta zabura don isa ga ‘yar ta. Shi kuwa Usm-Khairy kalmar shahada ya shiga yi gami da hailala, yana faxin.

“Shukurulaka ya Allah! Aina Lajjanatu! Aina! Aina La…”

Duk da sun fuskanci nutsuwa a cikin kotun, hakan bai hane su ci gaba da nuna mamakinsu a bayyane ba tare da yin godiya ga Allah da ya nuna musu ‘yar su. Har dai sai da alqali ya yi musu magana cikin harshen Larabci, kana suka nutsu.

Shari’ar ta koma da harshen Larabci, ana fassarawa waxanda ba sa ji. Usm-Khairy ya gayawa kotu tabbacin ‘yarsa ce, sannan ya bayyana taqaitaccen tarihinsu da al’amarin da ya faru a baya wanda ya haddasa rabuwar Lajjanatu da mijinta Alhaji Hammad da kuma barinta qasarsu. Duk dai bayanan nasa kamar maimaici ne ga bayanan da Barista Mahbub ya karanto a madadin Alhaji Hammad.

Bayan sauraron qarashen bayanai da nazari, alqali ya yanke hukunci.

“A bisa hujjoji da bayanai, tare da qwararan shaidu…kotu ta yanke hukuncin Almustapha ya saki Lajjanatu, kotu ta mayarwa da Alhaji Hammad matarsa.”

Ba dukkanin mahalarta kotun ba ne suka ji hukuncin da alqali ya yanke ba. Almustapha da Lajja kuwa suma suka yi. Surutu da hayaniyar mahalarta kotun ce ta hana fahimta da jin duk wasu abubuwa da suka biyo baya.

Wani mahalarcin taron ya kalli wanda ke zaune a kusa dashi. “Ba adalci a wannan shari’ar fa.”

Xayan ya dubeshi. “Me ya sa ka ce haka?”
“Kai me ka fahimta?”

“An yi adalci mana.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kushewar Badi 1Kushewar Badi 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×