Skip to content
Part 3 of 6 in the Series Kushewar Badi by Kabiru Yusuf Fagge

Bayan Shekara Daya

“Lajja ta haihu!”

Tamkar ruftowar aradu, haka Almustapha ke jin kalaman idan suka maimaitu a cikin qwaqwalwarsa kamar yadda ya ji su tun a farko.

Tun bayan da kotu ta yanke hukunci, ta qwace masa mata, ta mallakawa Alhaji Hammad, sai ya zamo tamkar mai qarancin hankali, duk wasu abubuwa na hankali sun qaranta a gare shi. Duk ya susuce, ban da addu’a babu abin da ke tallafar rayuwar shi.
Kullum yana cikin tuna faruwar al’amarin. Idan ya tuno da maganganun alqali a lokacin da yake yanke hukunci, sai ya ji kamar bugun guduma ne a cikin qwaqwalwarsa. To kuma yanzu an zo masa da labarin haihuwar Lajjar da Alhaji Hammad xin.

A iya tsawon rayuwarsa ta aure da Lajja ko vari ba ta tava yi a gidansa ba, bare ta haihu, alhalin yana matuqar son haihuwar, musamman ma da ita a matsayinta na matar da ya fi qauna, ya fi so a rayuwarsa.

Yau gashi an wayi gari, bayan an yi masa fin qarfi an qwace ta a tsawon watanni goma sha xaya da ‘yan kwanaki kenan da suka wuce, yanzu ta haihu. Wannan abu, ya ruxa tunaninsa, yana nema ya haukata shi gaba xaya.

Bayan kammala shari’ar, cikin matsanancin hali na rashin lafiya wanda baqin ciki da takaici suka haifar ga Lajja, Alhaji Hammad xin ya tafi da ita can qasarsu Masar. A can ta sami sauqi, ta ci gaba da zama cikin tsantsar baqin ciki da takaici da uquba fiye ma da shi Almustaphan. Shi kuwa Alhaji Hammad sai banka mata addu’o’i da asirai yake yi, wai a tunaninsa zata daina fushin da ta yi dashi ta dawo ta so shi kamar da, ta daina qyamarsa da wulaqanta shi.

Duk da faruwar hakan da kuma kasancewar halin da Lajja ke ciki waxannan ba su hana Alhaji Hammad ci gaba da harkokin kasuwancin ba. Domin ya kafu, harkokin kasuwancinsa sun yi qarfi a qasar Najeriya, ta yadda ba zai tava barin qasar kwata-kwata ba kamar yadda da farko ya so yi. Sai dai kuma hankalinsa da tunaninsa ya kasa su kashi biyu, babban kaso yana ga matarsa da ya fi so a duniya.

Idan ya zo Najeriya yakan yi kwanaki biyu zuwa uku kafin ya koma. To shi ne ma ya kawo labarin haihuwar Lajjar da ranar da ta haihun ta hannun babban amininsa Alhaji Zuhairu.

Abin ya zamewa Almustapha garnaqaqi. Sai dai kuma hakan bai hana shi zurfafawa cikin tunani, nazari da kuma binciken yadda za a tabbatar da cewa Lajja fa matarsa ce, kawai zaluntarsa aka yi, aka qwace masa ita, aka raba shi da ita.

Ba shi da wata qwaqqwarar madogara da ta wuce binciken yadda za a gane kuskuren da aka yi yayin shari’ar aka yi masa qwace. Binciken kuwa yana yi ne ga asali da tarihin qasar Masar da kuma abin da ya shafi mutanenta, tarihin su, asalin su, yanayi da kuma al’adun su.

Ya yi la’akari ne tare da qoqarin bin wannan hanya ta dalilin wata lacca da ya saurara daga gurin wani malamin tarihi kuma masanin kimiyya da ilimin sanin abubuwan qasa (Geography). Wanda ya yi a kan qasar Masar xin da tarihinta a duniya da ire-iren abubuwan mamaki da take xauke da su, waxanda suka wanzu a zamunan baya da waxanda ke wanzuwa a wannan lokaci.
Idan ka xauke sallah da ragowar hukunce-hukuncen addini waxanda suka rataya a wuyansa babu abin da Almustapha yake yi face wannan aiki na bincike da nazarin abin da ya sanya a gaba. Ya fi qarfafa binciken nasa ga saqar sama (internet), littattafai, mujallu da jaridu. Sannan kuma yakan ziyarci wuraren masana tarihi da ilimin abubuwan qasar.

Wannan ita ce hanya xaya kacal da yake ganin za a gane cutar da aka yi masa. Bisa dubawa da nazari da ya yi, ya kuma hanga a qarshe ya gane cewa babu wata hanya face wannan, qasar Najeriya ta vaci da yawa.

A watanni takwas din da ya kwashe cikin wannan hali ya yi nasarar samo tarihin qasar Masar da wasu muhimman al’amura da suka faru a qasar. Tarihin fir’aunonin Masar xin da abubuwan da suka aiwatar a rayuwarsu. Sai kuma tarihin wani tsibiri da wata shahararriyar mata mai suna Lajjanatu uwar Lajjanatu kakar Lajjanatu da Lajjanatu ‘Island of Habilan and the women of her century’.

Mafi akasarin abubuwan ya samesu ne daga sarqar, sai kuma ‘encarta encyclopedia’ da wasu littattafai da suka haxar da ‘Behind the Mask of Tutenkamun, The Great Egypt, Who’s Who, Pharoah of Egypt, History and Culture of Egypt, sai kuma mujallar ‘National Geographic.’

A haka ya haxa littafi guda da ya sanya masa suna ‘Jan-Kundi’. Inda a ciki ya fi mayar da hankalinsa matuqa ga tarihin wannan shahararriyar mata, mai sunan matarsa.

Jan Kundi

Tsibirin Habilan da Matar Karni


Shekara Ta 878 (259 HijiraI)

Abubuwan da ya tattara ga samuwar Lajja.

Kamar yadda masana tarihi, rayuwar al’umma, halayya da kuma zamantakewar halittun duniya suka nuna tun daga bayyanar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW) zuwa shekara ta dari takwas da saba’in da takwas (878) (bayan Annabi Isa AS) wanda ya yi daidai da shekara ta dari biyu da hamsin da tara (259H) bayan hijirar Annabi Muhammadu (SAW) ban da addinin Musulunci a duniya babu wani addini ko yin bauta da ya fi yin tasiri a tsakanin wannan lokaci da ya wuce maguzanci.

Maguzanci yana nufin yadda al’ummar vangarorin duniya suka fi yawaita bautar iskoki, aljanu, maridai, duwatsu, bishiyoyi, rana da wasu abubuwa daga cikin namun daji da koguna da sauransu.

A wannan zamani, Allah da ya halicci duniya da abubuwan da ke cikinta ya halicci wani tsibiri don nuna wani iko nasa. Tsibirin da ke dauke da tarihin da ya kwashe zamaninnika ana zancensa, kuma ya vace a lokaci qanqani vat aka daina zancensa. Tsibirin da ke dauke da al’umma masu dauke da wani wakilci na Ubangiji, kebantattu. Tsibirin da yake qunshe da matar da ta zamo wata halitta ta daban a wani vangare a bainar halittun Ubangiji na doron duniyar Subhana.
Tsatsonta sun yawaita a duniya, dauke da abubuwa na musamman mamaki da al’ajabi. Iko kenan daga mahaliccin halittar. Tsibirin Habilan kenan.

Tarihi da hasashe na nuna tsibirin ya wanzu ne a qarni guda kuma ya kau a cikin wannan qarni. Amman hakan ba yana nufin shi ne zance mafi inganci ba. A vangaren rayuwa da al’amura kuwa mutanen tsibirin sun bambanta da na sauran al’ummar duniya.
Wani shahararren masani, Balaraben qasar Lebanon Malamin Fikira da Lugga mai suna Abu Baqir Al-Azwa ya tava gabatar da wani bincike (hasashe) a shekara ta 1960, inda ya nuna samuwa da wanzuwar tsibirin nan da mutanen kansa ta wani xan lokaci ne, kuma tsatso daga cikin al’ummar tsibirin nan za su watsu a duniya xauke da wani kevantaccen al’amari.

Dukkanin hasashen da wannan Balarabe ya rubuta sun faru ne tun kafin a haife shi, har aka haife shi, ya rayu ya yi rubutun, ya mutu, al’amarin na faruwa, gashi har ya riski gomiyar qarni, ya shiga shekara ta 2020, ya shafi Almustapha.

Malamin ya yi bayanin al’amarin kamar yadda ya faru, kuma tamkar a gabansa.
Dagulewar al’amuran sun fara durfafar tsibirin da mutanen kansa ne a lokacin da suka gota qarnin. Hakan kuwa ya faru ne daga ainihin iskar da suke bautawa wadda ke voye a cikin wani kogo qwaya xaya dake kan tsibirin.

Akwai barazanar da wata sarauniya dake yammacin duniya take yi musu na tarwatsasu ta raba su da wurin, a wannan lokacin, to amman hankulansu ba su tashi ba kamar yadda iskar da suke yi wa bauta ta tayar musu.

A cewar iskar wani ruhi daga cikin ruhinan al’ummar tsibirin na bijirewa daga bauta gareta, don haka fushi ya tabbata garesu.
A tsarin yadda suke gabatar da bautarsu shi ne duk shekara su kan je gindin dutsen su yi ta sujjada ga dutsen, tun daga safe har zuwa kusufin rana, sai kuma yanka dabbobin da suke yi. A qarshe kuma sai a baiwa iskar kyautar yarinyar da ta fi kowace kyau a cikin al’ummar tsibirin ta hanyar shigar da ita cikin tsibirin, sai kuma ta vace har abada.

Haka nan Sarkin tsibirin ne zai shiga tare da yarinyar. Idan ya fito sai ya sanar da al’ummar tsibirin dukkanin abubuwan da za su faru a shekarar da albishir-albishir da iskar ta yi musu. Idan kuwa bai fito ba, to hakan na nufin abin bautar tasu na buqatar sauyin sarki, don haka shima ya vace kenan har abada.

Shekaru uku sun kasance cikin fushin gunkin bautar tasu don haka suke fuskantar lamuran tashin hankali daki-daki.

A wannan lokaci sun yi cirko-cirko a bakin dutsen. Sarkinsu, Sarki Qaysu na gaba dukkaninsu sun yi sujjada sai wasu abubuwa suke yi na neman gafara ga Ubangijinsu. Tun safe suke a haka har zuwa zawalin rana, wannan ma nuni ne da cewar suna cikin fushin abin bautar.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kushewar Badi 2Kushewar Badi 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×