Skip to content
Part 4 of 6 in the Series Kushewar Badi by Kabiru Yusuf Fagge

Lajjanatu

A can cikin tsibiri, a gidan sarki, Lajjanatu na zaune riqe da wata sulken fata, wacce ke zane da rubutu irin na harshen Habashiyanci (yaren da suke yi). Tana mai miqa al’amuranta ga sarkin da dukkan al’ummar tsibirin ba su sani ba. Sarki buwayi, Ubangijin sammai da qassai, Allah (S.W.T.)
Samuwa da kasancewarta cikin wannan hali ya faro ne tun daga shekaru uku da suka wuce. Wata ranar Litinin da safe sun je kamun kifi (su) ita da sauran ‘ya’yan Sarki, ‘yan uwanta. Allah (SWT) ya bayyanar da haskensa gareta, ta yadda ta tsinci wannan sulken fatar. Sulken yana xauke ne da kaxaitakar zatin Ubangiji Allah, da wanzuwar Annabin gaskiya da addinin Musulunci.

Tarihi ya nuna sulken ya samo asali ne bayan wani yaqi da aka tafka tsakanin Musulmai da kafirai a xaruruwan shekaru da suka wuce daga wannan lokaci. A lokaci guda kuma ta tsinkayi ganin wata bishiya wadda ke sassarqafe ta rubuta kalmar shahada.
Tun daga wannan lokaci ta nutsu gami da tattara hankalinta gurin fahimtar wannan al’amari mai ban mamaki da al’ajabi, har kuwa sarkin sarakuna, makaxaici ya ganar da ita.

Ta nutsu wurin bauta ga Allah a voye, tun daga wancan lokaci har zuwa wannan lokaci da ta ji ba za ta iya dainawa ba, zuciyarta ma ta kai qololuwar ganin ta jawo hankulan mutanensu da kuma son kaiwa ga waxanda suka san wannan addini, kuma suke aiwatar da shi a cikin duniya.

Qaysu ya kutsa cikin kogon. Bai daxe da shiga ba, sai kuma gashi ya fito, dukkanin yanayinsa ya sauya, muryarsa wata iri ta koma.

“Tir! dinmu al’ummar tsibirin Hablan. Haqiqa banu ya tabbata ga ‘yata Lajjanatu, wacce ke bijirewa abin bauta mafi girma. Ya kai waziri Iklan dan Haman ina umartarka ka je ka kawo min ita yanzu nan.”

Sarki Qaysu yana rufe baki, Waziri Iklan ya tashi ya bazama. Ba tare da vata lokaci ba Waziri Iklan ya je ya kawo Lajjanatu. Sarki Qaysu ya kalli ‘yarsa, ya kuma umarceta da ta shiga kogon nan.

Lajjanatu ta kalli mahaifinta da biyayya, sannan ta kalli mutanen tsibirinsu da kuma halin da suke ciki. Sai ta fashe da kuka, zuciyarta ta tausaya garesu, yadda suke bauta ga wanin Allah, suke wahalar da kansu. Ta ce “Ya Babana babu shakka zan shiga inda ka umarceni da umarninka da izininka, amma ba domin umarnin kowa ba…”
Maganar Lajjatanatu ta razanasu gaba xaya.
Ta shiga xin. Lokaci madaidaici da bai wuce mintuna goma ba sai ga ta ta fito. Fitowarta daga cikin kogon ya firgita al’ummar nan matuqa. Sarki Qaysu ya kalleta sosai.

“Ya ‘yata haqiqa kina tattare da wani al’amari na musamman.”

Lajjanatu ta fashe da kuka, wannan ya faru ne saboda tunanin qarshen rayuwarsu a wannan tsibiri ya zo. Ba ta san inda rayuwa za ta cillasu ba, burinta kawai su riski hasken Musulunci a ko ina a faxin duniya.

“Haqiqa ya Abbana Allah (SWT) shi ne Ubangijin da ya halicci duniya, ya haliccemu, ya halicci wannan tsibiri da muka samu kanmu a ciki. Shi kaxai ne Ubangiji abin cancanta da a bautawa. Wanda ya samar da wannan tsibiri a wani xan wuri na duniyarsa mai faxi, ya halicci wannan tsibiri da wannan kogo da abin da ke cikinsa ake bauta masa, alhali shima abin halitta ne.

“Haka zalika shi ya albarkaci wannan tsibiri namu da ni’imomin arziqi da har wasu suke son rabamu da gurin don su mallaki ni’imomin da mu basu dame mu ba. Don haka abin la’akari anan shi ne duk duniyar nan ba zai zamo cewa akwai wata halitta da ke cikin wannan kogon da za ta zamo abar bautawa ba. Abin lura da misali shi ne yadda a yanzu na shiga kogon, na fito ba tare da wani abu ya sameni ba kamar yadda kowa ya yi tsammani, hakan na nuni ne da cewa na fito ne da ikon Ubangijin halittun duniya kaf, kuma mafificin abin bauta, madallan madogara. Shi ne Ubangijin da ya aiko ‘yan saqonsa (Annabawa) don isar da saqonsa ga mu bayinsa…”

Wata qara ce da ta bayyana ta katsewa Lajjanatu maganarta. Qarar ta firgita al’ummar dake gurin sosai, da yawansu sun yi zaton fushin abin bautarsu ne ya fara tabbata a garesu.

Kafin faruwar qarar wasu daga cikin al’ummar tsibirin sun fara nutsuwa da maganar Lajjanatu, kuma ta ratsa zukatansu matuqa.

Qarar da suka ji, qarar jirgin ruwan wakilan sarauniyar yammacin duniya ce, wadda ta yanke shawarar kawo jirgi don kwashe su, yadda ita kuma za ta kwashi arziqin yadda take so.

Qalilan sun amince da shiga jirgin ruwan, wasu don bin umarnin sarauniya, wasu kuma saboda tasirin da maganar Lajjanatu ta yi musu. Akwai kuma waxanda ba su bi ko xaya daga ciki ba, sun zavi zamansu a tsibiri ko da za su halaka.

Jirgin ya sanya gabansa yamma don nufar yammacin duniya, vangaren da sarauniya ta buqaci a kai su.

Duka-duka ba su yi tafiyar murabba’i metan da rabi ba suka ji wata mummunar qara, ninki ga wadda suka ji a xazu, hankulansu suka yi vangaren da qarar ta taso. Vangaren tsibirinsu kenan, hankulansu suka tashi, razana da fargaba ta mamayi yawancinsu.
Wani irin tsaumiye (vulcano) ya tashi a saitin dutsen bautarsu, kana a hankali suka ga tsibirin na zagwanyewa. Mutanen da suka rage a cikin tsibirin suka rinqa afkawa cikin ruwa don tsira da rayukansu. A qarshe wata guguwa mai tsananin duhu wadda basu san ta inda ta taho ba ko ta faro ba, ta turniqe dukkanin illahirin tsibirin, a lokacin da ta lafa sai wurin ya zamo sai ruwa, tamkar ba a tava yin wani abu tsibiri a gurin ba.

Hankalin Lajjanatu da sauran mutanen dake cikin jirgin ruwan ya tashi. Lajjanatu ta xaga hannu sama tana kuka tare da addu’a ga Allah, mahaliccin gangar jiki da ruhi.
Kallon mutanen dake cikin jirgin ruwan ya koma gareta cike da mamaki. Mutanen tsibiri suna mamakin wannan sabon addini da Lajjanatu ke yi, su kuwa Turawa, ma’aikatan jirgin da wakilan sarauniya mamakin samuwar addinin Musulunci, wanda suka daxe da saninsa a wannan tsibiri suke yi.
Thomsop Barry, shi ne shugaban wakilan sarauniya, ya fi kowa mamakin wannan al’amari, sai dai mamakin nasa ya sha bamban, kasancewar ya tava yin bincike mai yawa akan addinin Musulunci da Kiristanci da sauran addinan duniya, da tarihe-tarihensu.

Idan bai manta ba a cikin bincikensa ya tava cin karo da wani hasashe da wani Barumiye ya yi tun a zamanin Annabi Isa (AS) cewar za a yi wata mata mai tattare da abubuwan mamaki, tsatsonta za a samu masu yiwa Musulunci hidima, tsatsonta za su watsu a duniya da yawansu suna xauke da tarin abubuwan mamaki savanin ire-iren waxanda mutane suka sani. Za su rinqa zuwar wa da mutane da sauyi a dukkanin al’amuransu na rayuwa.

Tsatsonta za su hayayyafa, su samar da al’umma masu matuqar kamanni da junansu. Za su watsu a duniya, za su rinqa bayyana a zamunna daban-daban.

Thomsop ya qarfafa tare da kyautata zatonsa da cewa wannan mata da yake gani a gabansa ita ce Lajjanatu, bugu da qari ga shi idan ya kalleta sai ya ji gabansa na faxuwa.

A tarihin da ya karanta musamman wanda ya shafi watsuwar addinin Musulunci a duniya da durfafarsa nahiyar Afrika yana da alaqa da samuwar wannan mata wadda aka samar da bayan samuwarta tun kafin ta samu xin.
Musulunci ya fara shigowa nahiyar Afrika ne a lokacin da Annabi (SAW) da sahabbansa suke fuskantar matsawar kafiran Makka. A lokacin da azabar ta tsananta a cikin shekara ta biyar da fara kira, sai Annabi (SAW) ya baiwa sahabbansa damar yin hijira zuwa Habasha (Ethiopia) wadda ke cikin nahiyar Afirikan. A lokacin sarki Najjashi (Negus) shi ne sarkin Habashar, Kirista ne, amma ya karvesu hannu bibbiyu, ya karramasu, kuma ya yarje musu zama a qasarsa, musamman ma da ya ji cewa sun yi imani da Annabi Isa (AS) Manzon Allah ne kuma bawansa ne, don haka ya amince da basu mafaka.

Hakan ya vatawa kafiran Makka rai, suka aiko da wakilai gurin Sarki Najjashi domin su koma da sahabban nan, amma ya qi yarda, ya fatattakesu. Don haka sahabban suka ci gaba da zamansu a qasar, har ma daga baya wasu suka qara zuwa, yawansu ya kai tamanin da uku. Sun zauna a nahiyar Afirika har Annabi (SAW) ya yi hijira daga Makkah ya koma Madina, sannan suka yi sallama da Sarki Najjashi, suma suka tafi Madina. Ga dukkan alamu wannan ce dama ta farko da Musulunci ya fara samuwa a Afirika. Koda yake Thomsop ya san a lokacin bai yaxu ba saboda yana da rauni sosai.

Haka nan bayan da fiyayyen halitta Annabi (SAW) ya kafa daular Musulunci a Madina, sai kuma qasar Masar (Egypt) wacce ita ma babbar qasa ce a Afirika, tana qarqashin mulkin Rumawa ne a lokacin. Rumawan kuwa sun mayar da ‘yan asalin qasar (wato Kibxawa) kamar bayi. Sarkin Rum ya naxa Almaqaqis (Cyprus) ya zama gwamnansa.
Annabi (SAW) ya fara aikewa da wasiqu zuwa ga sarakunan duniya yana kiransu zuwa ga addinin Musulunci wannan ya faru ne a cikin shekara ta bakwai (Hijiriyya) a cikin sarakunan da ya aikawa har da na Afirika guda biyu, sarkin Habasha da gwamnan Masar.

Al’amarin dai ya ci gaba da faruwa salo-salo har bayan wafatin Annabi (SAW) zuwa kalifancin Sayyadina Abubakar zuwa ga gwarazan Musulunci irin su Zubayr Bin Qays Abalam, Hassan Bin Numan Alghassari, Musa Bn Nusayi Bn Abdulrahman bn Zaid Allakhmi da sauransu. Haka dai abubuwan suka ci gaba da faruwa, amma duk ba wannan ne suka fi daga hankalin Thomsop ba, musamman ma da yake sun riga sun faru, face siffanta da Lajjanatu ta yi da matar da yake tabbacin ita ce, dari bisa dari. Wannan abu ya fi tayar masa da hankali fiye da komai.

A taqaice dai ita ce matar da zuri’arta zata zamo mai yaqi wajen kawar da tsubbace-tsubbace da maguzanci. Zuri’arta zata bambanta da sauran al’ummar duniya ta vangare da dama. Zuri’a masu kamanceceniya da juna.

A lokaci guda ga afkuwar zagwanyewar tsibirin Hablan, wanda hakan ke xauke da abubuwa guda biyu; Na farko dai zagwanyewar tsibirin ta watsa musu shiri da burinsu na amfana da abin da yake qarqashin tsibirin, abu na biyu kuwa faruwar hakan ya qara tabbatar da zarginsa na cewar Lajjanatu da yanzu yake gani a gabansa ita ce matar da yake tsammani.

Don haka ya yi hanzarin sauya shawara. Maimakon su kai su Lajjanatu inda ke tattare da ni’imomi, kusa da tarin al’umma masu ci gaba, gara su barsu a nan nahiyar Afirika, mai tarin dazuzzuka su watsar da su cikin sahara da dazuzzuka. Domin hakan zai kawowa abin da za ta watsa xin nakasu.
A take ya bada umarnin a juya jirgin zuwa tsibirin Nasser dake kusa da Masar, daf da saharar iyakar qasar Libiya.

Jirgin ya doshi tsibirin Nasser gadan-gadan to a lokacin ne kuma wata baqar guguwa ta tokare sararin samaniya. Lamarin ya dagule musu, tuni daman babu wani abin yi ko dabara face saduda.

Wannan ma wata alama ce ta gaba wadda ta tabbatarwa da Thomsop zarginsa.

Guguwar ta kifar da jirgin. Mutane bakwai ne kawai suka tsira, waxanda suka haxar da Lajjanatu, Iklan da kuma Thomsop.

Tarihi ya ci gaba da wanzuwa, kuma ya nuna Lajjanatu ta rayu a Masar cikin baqar wahala da muni. Ta hayayyafa, tana cikin waxanda suka tone kabarin Fir’auna Tutankhamun, wanda ya shafe shekaru dubu xari uku da mutuwa a binne.

Alama ta qarshe kuma maqasudiya da Thomsop ya gani ita ce da shi kansa ya Musulunta ta sanadiyyar Lajjanatu kuma ya aureta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kushewar Badi 3Kushewar Badi 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×