Bayan Shekara Daya
“Lajja ta haihu!”
Tamkar ruftowar aradu, haka Almustapha ke jin kalaman idan suka maimaitu a cikin qwaqwalwarsa kamar yadda ya ji su tun a farko.
Tun bayan da kotu ta yanke hukunci, ta qwace masa mata, ta mallakawa Alhaji Hammad, sai ya zamo tamkar mai qarancin hankali, duk wasu abubuwa na hankali sun qaranta a gare shi. Duk ya susuce, ban da addu’a babu abin da ke tallafar rayuwar shi.Kullum yana cikin tuna faruwar al'amarin. Idan ya tuno da maganganun alqali a lokacin da yake yanke hukunci, sai ya ji kamar bugun. . .