Lajjanatu
A can cikin tsibiri, a gidan sarki, Lajjanatu na zaune riqe da wata sulken fata, wacce ke zane da rubutu irin na harshen Habashiyanci (yaren da suke yi). Tana mai miqa al'amuranta ga sarkin da dukkan al'ummar tsibirin ba su sani ba. Sarki buwayi, Ubangijin sammai da qassai, Allah (S.W.T.)Samuwa da kasancewarta cikin wannan hali ya faro ne tun daga shekaru uku da suka wuce. Wata ranar Litinin da safe sun je kamun kifi (su) ita da sauran 'ya'yan Sarki, 'yan uwanta. Allah (SWT) ya bayyanar da haskensa gareta, ta yadda. . .