Babban abin da ya fi baiwa Alhaji Hammad mamaki shi ne da kotu ta neme shi, a madadin Almustapha, babban abokinsa Albashir ya daukaka qarar da aka shude shekara guda da kammalawa.
Kotun, wadda babba ce (high court) dake birnin tarayya Abuja, ta nemeshi a ranar Talata, shi da Lajja don ana tuhumarsa da qwacen matar da ba tashi ba. Alhaji Hammad ganin abin yake tamkar wasan yara, kwata-kwata bai zaci haka ba, tun da dai shi ya tabbatar har ga Allah Lajja matarsa ce. Koda yake ya san irin yadda ake tsilla-tsilla da shari'a a Najeriya. . .