Skip to content
Part 6 of 6 in the Series Kushewar Badi by Kabiru Yusuf Fagge

Babban abin da ya fi baiwa Alhaji Hammad mamaki shi ne da kotu ta neme shi, a madadin Almustapha, babban abokinsa Albashir ya daukaka qarar da aka shude shekara guda da kammalawa.

Kotun, wadda babba ce (high court) dake birnin tarayya Abuja, ta nemeshi a ranar Talata, shi da Lajja don ana tuhumarsa da qwacen matar da ba tashi ba. Alhaji Hammad ganin abin yake tamkar wasan yara, kwata-kwata bai zaci haka ba, tun da dai shi ya tabbatar har ga Allah Lajja matarsa ce. Koda yake ya san irin yadda ake tsilla-tsilla da shari’a a Najeriya, don haka ya sakankance akan hakan ne ya biyo baya.

Abin da ya fi bata masa rai shi ne da aka ce sai ya taho da matar tasa daga Masar din. A duniyar nan babu abin da ya fi tsana irin a ce ga wani abu da ya danganci takurawa zai shafi matarshi da danshi. Ya dauki son duniyar nan gaba daya ya dora kan matar ta shi da danshi, wanda ya sanyawa suna Yusuful Nabahani.
Wahalhalu, baqin ciki gami da takaicin da ya sha kuma yake kan sha daga wurin Lajjar abin har ba zai fadu ba. Ya azabtu, ya ga takaici kuma yana kan gani. Tun lokacin da mai shari’a Mahdi Alyasa’u ya qwace matar daga hannun Almustapha ya mallaka masa, ya tafi da ita qasarsu, shi da kansa bai yi zaton shi ko ita wani zai kawo wannan lokacin dauke da numfashi ba. Cikin ikon Allah, kuma da yake shi mai rayawa ne sai ga su a wannan lokacin har da da. A wurin Alhaji Hammad ya kira wannan lamari azimun, kuma ya saduda da cewa rayuwa ce.

Har a wannan lokaci ana cikin wannan hali. Haka ita ma Lajjar ba ta saduda ba. Shi kuma bai daina juriya da ci gaba da son ta ba, domin a ganinsa ko ba daxe ko ba jima zai shawo kanta a kan fushin da ta yi dashi, da azabtar dashi da take. Don haka duk wani abu da ya nemi shigar masa hanci ko kawo masa matsala a sha’anin rayuwarshi da matarshi a ganin Alhaji Hammad wannan abu ba shi da maraba da bala’i.

Ya qudurce cewar daga wannan lokaci zai bar duk wasu harkokinsa na Najeriya. Zai tattara yanasa-yanasa ya koma qasarsu. Kuma ya qudire da idan aka gama wannan shari’a wacce yake ganin babu ta inda za ta tabashi zai sa a jawa Almustapha kunne. Sai ma ya kulleshi don huce haushi.

Ranar Litinin da yamma suka sauka a Najeriya shi da Lajja da dansu Yusuful Nabahani a otel din Hilton dake Abuja. Tuni sun gama magana da lauyansa ta waya, tun yana can Masar.
Mai shari’a Uwais Lawal Uwais dan babban mai shari’a wato alqalin alqalai na Najeriya Muhammad Uwais shi ne da alhakin yin wannan shari’a.

Har lokacin da kotu ta dibar wa ganin Almustapha da Lajjanatu ya yi, ya wuce babu su, babu alamunsu. Abin kamar wasa. Albashir ya rikice, hankalinshi ya yi matuqar tashi. Gumi ya lullubeshi kamar ruwa alhalin ana yin sanyi.

Tabbaci suka nuna ba alamar zuwansu, don haka kotu ta kori qarar tare da neman Albashir sati mai zuwa don tuhuma.

Alhaji Hammad ma ya shigar da qara don tuhumar Albashir, domin ya kira abin rainin hankali da kuma neman tayar masa da kwance tsaye, gami da bata suna. Daman yana da niyyar hukuntashi da abokinshi, wannan ne ya jirkinta komawarsa Masar, yana son ya tabbatar da an jawa matasan kunne akan bata masa rai da tayar masa da hankali da suke yi.
Jirgin da ya dira daga Jidda da misalin qarfe daya na rana shi zai baiwa jirgin da zai tashi qarfe daya da rabi damar tashi zuwa qasashen da suka hadar Masar.

Alhaji Hammad, Lajja, da dansu suna cikin ayarin wadanda za su bi wannan jirgi don zuwa qasar Masar. Zaune suke a harabar filin jirgi na Malam Aminu Kano suna jira. Daga inda suke suna hango ko ina na illahirin filin jirgin. Ko’ina ka waiga mutane ne, kowanne da abin da yake yi da kuma abin da ya sanya a gaba.

Tsayuwar jirgin da sanya masa matattakala duk ya faru ne akan idanun ayarin Alhaji Hammad su bakwai shi Lajja, Yusuful Nabahani da kuma ‘yan rakiyarsu mutane huxu.

Mutanen cikin jirgin suka fara fitowa.
A tsakanin mutum na tamanin da kuma na tamanin da xaya daga masu fitowa daga jirgin ne al’amarin ya faru. Duk da cewa mutum na tamanin da biyu Balarabe ne kuma tafiyarsu xaya da na tamanin, da tamanin da xayan hakan bai sa an damu da shi ba.

Almustapha ne na tamanin xin, Lajjanatu tamanin da xaya sai kuma Saif Ali na tamanin da biyu.

A vangaren su Alhaji Hammad wanda hankalinsa ke xauke da tabbacin gamsuwa da irin hukuncin da kotu ta yankewa Albashir, bai zata ba bare tsammani, sai gani ya yi Lajja ta jefa masa Yusuful Nabahani ta zabga da gudu zuwa wurin da jirgin nan yake. Shima bin ta ya yi cikin rashin zato xin da tsammani, amma riqe yake da xan qam-qam.

Lajja tana kaiwa bakin matattakalar jirgin Almustapha na gama sauka qarshen matattakalar, a ximauce cike da matuqar gigicewa suka dubi juna.

Alhaji Hammad ma ya qaraso wurin cikin haki. Hankalinsa ya kasu biyu, a bayan Almustapha da Lajja matarsa ya gani Lajjanatu.

Hankulan tarin mutanen dake harabar filin jirgin ya yo garesu.

Kamannin Lajja da Lajjanatu ba za su rarrabu ba, kuma babu mai iya rarrabewa, sai ‘yan tsirarun mutanen da ba su fi huxu ba in ka haxar har su.

Yanzu Alhaji Hammad ya yi matuqar gane kurensa. Ximuwa da tsananin qauna da son matarsa da yake yi haxi da matuqar kama da suka yi da junansu, ya sanyashi tafka kuskure. Kuskure xaya da ba zai tava gyarawa ba a babin rayuwarsa.

Gavovin jikinsa suka yi sanyi, nadama da baqin ciki da takaici suka yi damqar a zuciyarshi, ya rasa abin da ke mishi daxi. Ya kalli Lajja, ya kalli Lajjanatu, kana ya dubi xansa qwaya xaya a rayuwarsa Yusuful Nabahani. Hawaye mai tsananin raxaxi ya rinqa malala a kan kumatunsa.

Mene ne matsayin Yusuful Nabahani, xan da Alhaji Hammad ya haifa da matar da ba tashi ba cikin rashin sani? Kuma a wane matsayi auren Almustapha da Lajja yake?

Waxannan sune tambayoyin da suke gina kansu a zuciyar duk wanda ya san da al’amarin, ko ya sami labari. Amsoshin tambayoyin suna da rikitarwa da sanya shakku.

*****
‘Bisa amincewar Lajja da tsananin qaunarta ga mijinta an mayarwa da Almustapha matarsa Lajja. Xan da ta haifa da Alhaji Hammad kuwa da zarar an yaye shi zata kaiwa ubansa. Auren dake tsakanin Lajjanatu da Alhaji Hammad kuwa ya zamo warwararre kuma babu shi….’

Kamar a cikin qoqon dake gina tunane-tunanen al’amuran yau da kullum na duniya Alhaji Hammad ya rinqa jin maganar mai shari’a. Idan alqali yana magana a can baya a wani lokaci daga cikin lokutan rayuwarsa Alhaji Hammad yana nutsuwa ne, ya girmama kalaman, ya fahimcesu, amma a wannan ranar ya rasa nutsuwarsa a kalaman farko, ya dabarbance ya ximauce, ya gigice.

‘Ruhina da raina sun karkata ga ainihin wanda suke so. Na rantse da maqagin numfashina idan ban zamo mata a wurin Almustapha ba rayuwata taqaitacciya ce. Jinina da hantata sun ji qamshin magwajinsu, idanuna sun ga ainihin haskensu mai alfarma.’ Cewar Lajjanatu.

Shiru ya wadata.

Almustapha ya kalleta, kana ya kalli matarsa Lajja, duk ta rame ta sauya masa a yadda ya santa, mai walwala, mai fara’a, mai qamshi, mai fararen idanu, mai xauke da sirri yayin da aka kalli fuskarta. Xauke a hannunta Yusuful Nabahani ne, xan da ba nasa ba, zuciyarsa na raya masa kamar nasa ne, halittar da ya daxe yana so da wadda ta haifi halittar, amma bai samu ba. Wannan iko ne na Allah, nufinsa ne, tsarinsa ne. Hawaye masu zafi suka shiga saukowa daga idonsa.

Matarshi, ta haihu da wani mijin na daban wanda ba nata ba. Ga xan yana gani tana shayarwa! A vangare guda kuma ga Lajjanatu! Shi take so! Take so da aure!

Allah ya sanya masa nutsuwa ta xan lokaci, ya ba shi damar nazarin al’amarin, ya haska masa haske a ruhinsa. Hanya mafi kyau kuma marar sauqi ita ce Lajjanatu ta haqura, ta koma gidan mijinta, ta raini xan da matarshi ta haifarwa mijin nata. Dukkanin wannan nazari da ya yi a cikin kalaman da Lajjanatun ta yi suna nuna ko kaxan kuma ko alama ba zai yiwu a.

‘Ina! Ai sam!’
Ko shi zai iya haqura da matarsa Lajja ya bar wa Alhaji Hammad? Ko ita Lajja za ta iya ci gaba da zama da Alhaji Hammad a matsayin mata da miji har abada.

Ko kaxan ba zai yiwu ba.

Qwaqwalwarshi kamar za ta zagwanye.

Wata shari’ar! Ba shakka sai a lahira
A cikin waxanda suka halarci shari’ar har da alqali Mahdi Alyasa’u. Dukkanin abubuwan da suka faru sun faru ne tamkar a cikin qwaqwalwarsa. Bayan kammala shari’ar bai koma gidansa na Kaduna ba, sai gawarsa da aka gani a masaukinsa dake otel xin Oondo Motel ya harbe kanshi.

Duk a tarihin rayuwarsa kaf wannan ce shari’a xaya da ya sami kuskure, ta dama masa lissafi, ta dagula masa al’amura, ta lalata tsarinsa da tarihinsa, ta sauya masa alqibla.

Allah ne kawai mabuwayi! Gwani akan komai.
Almustapha ya dubi Lajjanatu daga bisani ya dubi Lajja, da Yusuful Nabahani, ya fashe da kuka. Hakan ya zame masa kamar numfashi. Tun da suka baro Abuja abin nasa ya qara tsamari. Albashir da Saif Ali ne ke ta qoqarin rarrashinsa.

Lajja ma a halin da ta kasance kenan, har ma ta so ta fi shi. Ga baqin ciki da takaici ga tsananin tausayin ta da ta ke ji.

‘Lajjanatu ki yi haquri, ki duba, ki ga halin da muke ciki. Ki tausaya mana, ki ceto rayukanmu. Ki koma ga mijinki. Haqiqa tsananin son ki da qaunarki suna tattare da zuciyata. Ba yadda zan yi ne, mafita xaya tal ita ce ki jure, ki koma ga maigidanki, ku yafi juna, ki taimakeshi ki taimakemu.’

Muryarsa na xauke da tsantsar sakankancewa ga abin da ya faxa.

Lajjanatun ta kalleshi. Kamanninta sun sauya. Hakan ne ke faruwa a duk loakcin da Almustapha ya yi mata nuni da ta haqura da son da take yi masa wai ta koma ga Alhaji Hammad. Ranta yana matuqar vaci da hakan.
‘Almustapha na riga na san al’amarin da ya faru ya ritsa da kai al’amari ne mara daxin ji, mai tsananin da ke tattare da tausayi, takaici, damuwa da mamaki, amma yana da kyau ka san cewa dukkanin waxannan abubuwa sun faru a gareni, kuma za su ci gaba da faruwa gareni musamman idan abin da ka faxa ka ga shi ne mafita, shi zai fitar da ku daga halin da kuke ciki ni kuma ya qara jefani zai…’

Ya katseta.

‘Ki sani Lajjanatu kin ganni, kin kamu da sona a lokacin da ni kuma nake matuqar son matata, nake cikin mawuyacin hali. Wanda ya sa matata ta haihu da mijinki. Yana da kyau ki lura, ki san cewa idan har ba ki koma ga mijinki ba xan da suka haifa da matata zai cutu, idan ya cutu matata za ta cutu, idan ta cutu ni kuma zan cutu, don haka kin ga soyayyarki gareni ba ta da wani amfani. Zata zame min cutuwa, za ta haifar min da tsananin baqin ciki, za ta cutar da duk wanda ke qaunata, ta zamo marar amfani gareni da shi.’

Ya fashe da kuka.

Na gama
Mu hadu a
Launin So
Rayayye
Dansanda…abokin kowa

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kushewar Badi 5

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×