Kanta ya ɗaure bisa yanayin da ta soma fuskanta. Sauyin da ta soma ji a tare da ita na saka ruɗani a zuciyarta matuƙa. Yawan faɗuwar gaba ga waɗansu irin mafarkai masu matuƙar tsoratarwa. Wannan dalili ne ya sanya rama sosai a tare da ita. Nan da nan ta fita hayyacinta. Wasu lokutan tana riskar kanta a fili fetal babu kowa cikin mafarkinta, wasu lokutan kuma tana hango Saubahn daga gefe yana miƙo mata hannu.
Yayin da za ta ga wata fuska a gefe tana yi mata dariya mai ɗaci. Tun tana jurewa har. . .