Skip to content
Part 11 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

Kanta ya ɗaure bisa yanayin da ta soma fuskanta. Sauyin da ta soma ji a tare da ita na saka ruɗani a zuciyarta matuƙa. Yawan faɗuwar gaba ga waɗansu irin mafarkai masu matuƙar tsoratarwa. Wannan dalili ne ya sanya rama sosai a tare da ita. Nan da nan ta fita hayyacinta. Wasu lokutan tana riskar kanta a fili fetal babu kowa cikin mafarkinta, wasu lokutan kuma tana hango Saubahn daga gefe yana miƙo mata hannu.

Yayin da za ta ga wata fuska a gefe tana yi mata dariya mai ɗaci. Tun tana jurewa har ya zamana rauninta ya soma bayyana. Tasi kan zaunar da ita ya yi mata nasiha maimakon ta faɗa masa abin da ta ke ji sai dai ta fashe da kuka.

Tun yana lallashinta har ya koma faɗa. Sai dai ta kasa sanar masa ainihin abin da take ji, hasalima haƙuri ta koma bashi. Ganin babu sauƙi sai Allah ya sanya ya soma yi mata rubutu tana sha. A haka mahaifinta ya je ya dawo tsaraba kuwa sun sha ta ita da yaranta kamar ba gobe har hakan ya haifar da ƙaramin saɓani a gidan.

Maryam da Tasi sun zamo ababan alfahari da kuma kwatance cikin garin Malumfashi, sosai suke kulawa da junansu da kuma duk abin da ya shafi danginta. Cikin ikon Allah tun daga lokacin sai ubangiji ya ɗauke mata haihuwar kamar ɗaukewar ruwa. Suka rungumi yaran su sosai suke ba su tarbiya…

Tunaninta ne ya katse daidai lokacin da ta ji ana jijjigata. A firgice ta ɗago. Madu ne tsaye ya fi minti goma da shigowa amma tsabar ta lula a duniyar tunani ba ta san ya shigo ba.

“Don Allah mana Mammah! Ki bari mu ji da abu ɗaya kadda damuwa kar mana ke”
“Ba za ka gane ba Madui! Ba za ka gane ɗacin da nake ji ba. Ni na san na yi gangancin da ba zan iya gyarawa ba…”

Dare aka ce mahutar bawa amma ga Maryam sam ba haka bane, zuciyarta ta lula tunanin rayuwar da take ciki ita da ahalinta. A hankali ta mirgina ta sake juyawa. Idanunta ya sauka kan yaranta mata guda biyu.

Ba ta taɓa danasanin nagartar mahaifinsu ba irin yau, a tunaninta shi ɗin auransa zai zamo wata katanga mai ƙarfi da za ta gina shamaki tsakaninsa da yaranta, ashe kash ba haka bane.

Cigaban Labarinta

Tun bayan dawowar mahaifinta ‘yan uwanta maza suka soma takuwara mijinta kan dukiyar mahaifinsu. Ba huɗubar kowa ba ce sai ta Mama Sumaye. Tun suna tararsa a hanya har suka zuwa gida. Tun ba ta fahimci abin da yake faruwa ba har ta fahimta a wani zuwa da suka zo gida suka ƙare masa zagi.

Hakan ya baƙanta mata rai. Ta kanas ta shirya ta je ga mahaifinta tana kuka ta sanar da shi abin da yake faruwa, sai dai bayanin da ya yi mata ya yi matuƙar sanyaya gwiwarta.
“Ki yi haƙuri Maryama ba ni da wanda na yarda da shi kaf duniya a yanzu dai da zan ba wa amanar wannan dukiya. Idan ke kina ganin kin girma ko bayan raina za ki iya karɓar haƙƙinki ƙannanki fa? Wa zai tsaya musu. ‘Yan uwanki maha’inta ne ba sa ƙaunar Allah haka ma mahifiyar su. Su ne manya amma su ne suke neman makasat…”

“Amma Baba ba za ka iya zuwa alƙal…”

“To anamimmiya, da ma aike ki ke zuga shi yana zagar mini ‘ya’ya tare da aibata su.

Wannan, wannan Khadija ba ta kyauta mana ba. Ga shi da ta bar gidan amma ta bar mana abin tsiya da wasali. Wallahi idan ba ki fita kin bar gidan nan ba yanzu zan yi miki ihun kwarto da kwartuwa sai na ga ƙarshen soyayya tsakaninki da uban naki…”

Ta faɗa tana warce hijabinta, hakan ta bayyana suturar dake jikinta shimi ce doguwa zuwa gwiwa sai zani da ta ɗora a sama. Saboda zafi ake ita kuma sam basa shiri da zafi shi ya sa ko da za ta taho kuma ta ga gida za ta zo ba ta wani damu da ta sauya ba. Wani tsoro ne ya ɗarsu a ranta. Ta tabbatar za ta aikata abin da ta faɗa don haka ta karɓi hijabinta tana mai barin ɗakin.

“Aniyar ki ta biki Sumaye, ni ki ke son tozartawa to ki je na sake ki saki ɗaya kin ga babu kare bin damo”

Wannan furucin na mahaifinta shi ya sanya ƙafafunta tsayuwa cak akan duga-dugansu. Wani abu mai kauri na yawo a ƙirjinta. Tabbas da ta san haka za ta faru da ba ta zo ba..

“Burinki ya cika Maryam mahaifinki ya sake ni, kamar yadda ya sake ni a dalilin mahaifiyarki, ƙoƙon ranku sai ya kwanta kun ƙarasa cire igiyar da ta ragemini. Sai dai ki tabbata kun yi kuskure. Kuskuren da za ki girbe shi ta hanyoyi mabambanta a rayuwarki. Wallahi sai kin yi nadama mara amfani. Sai kin yi kuka a lokacin da hawayenki zai ƙare.”

“Ƙarya ki ke Sumaye, baki isa ki yi mata abin da Allah bai mata ba.”

“Na nawa kuma Tukur ai na gama da rayuwarta tun da na kaɗa uwarta duniya, na kuma ɓarar da burinta na karatun zamani tare da gindaya mata rayuwa da mara asali cikin duniyarta.”

Kasa jin ƙarashen kalamanta ta yi, kawai ta kaɗa kai ta fita tana kuka kamar ranta zai fita.

“Umma ta gaida Assha, ko kin rabani da ubanki dai baki isa hanani zaman ‘ya’yana ba.”

A haka ta koma gida cike da ɓarin rai. Tun daga lokacin kuma ta ɗauki ɗamarar ganin ta raba Tasi da duk wata dukiya ta mahaifinta amma hakan ya gagara. Kwatsam ta sami labarin ya siyi wata gona mafi girma da mahaifinta yake da ita wanda hakan ya ɗaga hankulan ‘ƴan gidan su. Zanga-zanga guda suka yo suka ci mutunci har da duka ciki kuwa hadda rakiyar Nuhu ƙanin Mama Sumaye.

Tun lokacin da ta samu labarin ya siyi gonar hankalinta ya ƙi kwanciya, kuka ta tasa shi gaba tana yi kamar wadda aka yi wa albishir na mutuwa.

“Saboda Allah duk gonakin garin nan ka rasa gonar siya sai ta mahaifina. Ni ba siyan ne damuwata ba, yadda mutane za su kali abin da kuma yadda waɗancan marasa mutuncin za su juya lamarin shi ne damuwata.”

“Maryama ni ban ga abin damuwa anan ba, ina ce gona dai shi ya ɗagata ya siyar kuma ba dole aka yi masa ba, taki aka kawo na zamani yake so ya sara saboda manoman da za su nema nan gaba. Kuma yanzu ba shi da kuɗi a hannu shi ne ya yi mini tallarta gudun wani ya siya a waje…”

“Da ka bi ta shawarata gara kawai wani ya siya a wajen, don wannan tashin hankali kawai ka gayyato mana.

*****
Bugun da ake yi wa ƙofar gidan kamar za a karyata ya fi komai ba ta tsoro, sake kasa kunnuwa ta yi, tabbas wannan ba bugu bane na nutsuwa. Miƙewa ya yi zai fita, hannu ta saka ta riƙe rigarsa idanunta na zubar da ƙwala.

“Abu Saubahn ba za ka fita ba!”

“Ki yi haƙuri ko da ban buɗe ba, dole sai sun shigo saboda nan suka nufo. Ba ki ji yadda suke bugun bane kamar masu bayar da umarni? Bana son wani abu ya ratso ta kanku don haka ki yi haƙuri ko da hakan shi ne kuskure mafi girma da zan aikata miki”
“Ka haura ka gudu don Allah!”

“Idan na gudu ku fa Maryama? Hankalina ba zai taɓa kwanciya ba duk inda zan kasance.”

“Amma…”

“Amma me Oum Saubahn? Duk abin da Allah Ya hukunta shi ne zai faru.”

Rungumeta ya yi tsam a ƙirjinsa, yana jin kamar hakan shi ne abu na ƙarshe a duniyarsu. Wani irin rauni ne yake mammayarsa, tabbas yasan a yau komai zai iya faruwa domin da ma sun sha gargaɗinsa. Yana ɓoye mata ne saboda ba ya son ɗaga mata hankali.

Gaba ɗaya rauni ya bayyana akan fuskarta, zuciyarta ta yi wani irin dokawa a hankali kuma ta shiga tsittsinkewa, kafin ta yi wani yunƙuri burum! Aka doke ƙofar gidan gaba ɗaya ƙofar ta faɗi ƙasa.

Sun ji sautin gaba ɗayan su, don haka ya yi azamar fita, da sassarfa ta biyo bayansa sai dai ba ta ƙarasa fitowa tsakar gidan ba sautin muryarsa ya dira akan kunnuwanta, sautin da har gobe ba za ta manta da shi ba a rayuwarta.

“la’iallah illalah…..!”

“Mun gama da shi”

Sautuka biyu suka yi mata dirar mikiya, ba don cikin tashin hankali take ba tabbas za ta iya gane muryar. Muryar wani nata, wani wanda take da kusanci da shi sai dai kash!

Tashin hankalin da take ciki ya tafi da duk wata guntuwar nutsuwarta.

Da gudu ta ƙarasa fitowa sai dai jinin da yake fita ta wuyansa sakammakon yankan rago da aka yi masa shi ne ya yi wa fuskarta tsartuwa, dai dai lokacin yaran suka fito waje suka yi cirko-cirko. Saubahn da ya fi su hankalina ya ƙaraso kusa da ita. Ganin yadda baban su yake numfashi ne ya saka shi fashewa da kuka.

Ido ya ƙurawa masu ɗaure da ƙyalaye a fuskokinsu ya yi, wani abu na cin zuciyarsa duk da kasancewarsa ƙaramin yaro. Wato kujera ce a kusa da shi da hasken farin wata ya haskata. Ɗaukarta ya yi ya wurgawa babban cikinsu. Take wani ya ɗauke shi da marin da ya sanya ya faɗi a wurin sumame. Madu da Abdallah sai suka koma gefe suna kyarma.

“Dakata boss, kadda ku taɓasu ba a ba mu damar taɓa kowa ba, mu yi hanzarin barin wurin kafin mutane su farga.”

Ras! Gabanta ya faɗi, sautin muryar ne ya cigaba da yi mata amsa kuwa a ranta. Da idanu take rakasu, ɗaya bayan ɗaya suke fita daga gidan, kowane taku na su na ba ta tabbacin shi kw nan komai ya ƙare.

Yayin da zciyarta ke wata irin dokawa, jin ta take kamar ba mutum ba kamar kuma ba a duniyar take ba. Ta kasa wani ƙwaƙwaran motsi bare ta fahimci a wane yanayi take. Ita ba mai hankali ba ita ba mahaukaciya ba.

Ta cikin farin wata ta ƙurawa Tasi ido, har zuwa lokacin da sauran numfashi a tare da shi, kokawa yake da fitarsa, kamar wadda aka tsikara ta yi kansa yayin da wani irin kuka ya ke ce mata, to wai ma wa za ta kira a wannan talatainin daren? Da rarrafe ta ƙarasa inda yake, kansa ta ɗauka ta ɗora kan cinyarta. A hankali hawaye yake zuba a idanunta.

“Shi ke nan komai ya ƙare!”

Ta furta da wata irin marainiyar murya, muryarta ta sarke yayin da ta cigaba da ƙoƙarin laƙanamasa kalma shahada a bakinsa. Cikin ikon Allah ya soma maimaitawa. A haka har ransa ya ƙarasa fita.

Da murmushi ɗauke a fuskarsa, idanunsa na kallon sama, wani tuƙuƙi ya dinga taso mata a ƙahon zuciya. Idanunta ya sauka akan su Madu da suka rungume juna suna kuka da kyarma. Yayin da ta sake kallon Saubahn a kwance da bai da maraba da matace. Wani duhu ne mai girma ya gilma ta tsakanin zinariyar idanunta.

Kalmar hasbunallah kawai take kira, ba za ta iya cewa ga wasu turaku da suka riƙeta ba, bata iya tantance a yanayin da take ciki ba har zuwa lokacin da ta ɗaga kai ta ga mutane zagaye da ita ba ga kuma yaranta na kuka kamar ran su zai fita.

‘Ya tabbata ba mafarki na yi ba.’

Ta furta a ƙasan zuciyarta, sai lokacin ta ji wani irin kuka ya kuɓce mata,

“sai haƙuri Maryam amma cuta kam an cutar dake.”

Muryar Yelwa maƙociyar su ta ankarar da ita abin da ta kamaci kokawa nan gaba ba yanzu ba. Domin yanzu ta sani kuka take mara tushe tunda akwai masu ba ta haƙuri. Kafin ka ce kwabo mutuwar Tasi ta zagaye ƙauyen.

Haka aka yi masa sutura aka sada shi da makwancinsa na gaskiya. Har aka kai shi jini bai daina zuba daga wuyansa ba. Wannan labari ya ƙara ruruta zuciyarta. Saubahn kuwa babu abin da yake sai haɗiyar zuciya.

Lokacin da labarin mutuwar ya riski mahaifinta take ya yanke jiki ya faɗi, daga sannan ya haɗu da ciwon shanyewar ɓarin jiki.

Haka aka gama zama na kwana bakwai, wanda kafin a kammala duk wata takarda ta Tasi wadda take nuna mallakin wata kaddara ce ta mahaifin su yayunta maza sun karɓeta har ma da wasu cikin nasa takardun, da sunan ta mahaifin su ce. Wanda suka tsira kawai wanda suke ɗauke da sunan Saubahn ne.

Sai dai babu abin da ya ɗaga hankalin su face takardar wannan gona da ta kasance mafi girma a wurin mahaifin su, lokacin da suka yi nufin karɓeta ne suka samu tabbacin Tasi ya siyeta da kuɗinsa. Kuma sunan Saubahn ne akan takardun. Wanda mahifin su ya yi barazanar tsine musu a kanta. Kuma yarjejeniya har gaban maigari kan cewar mallakin Saubahn ɗin ce da sunansa ke jiki.

Hakan ya ɗugunzuma hankalinsu matuƙa ya kuma karya duk wani shiri na su. Sun kuma ɗauki ɗamar karɓarta bakin rai bakin fama. Da wannan suka ƙulaci Maryam da ƴaƴanta wadda babu abin da ta tsira da shi sai wannan kundi da kullum yake mata gargaɗi a kansa sai marayun ‘ya’yanta. Kundin da tashin hankali sam bai bada damar tunanin buɗe shi ba bare abin da ya ƙunsa.

*****

A hankali ciwo ya cigaba da cin mahaifinta, matansa da yaransa gaba ɗaya babu wanda yake kula da shi. Tun tana zuwa ta gyarashi idan ya yi bahaya da sauran buƙatu har ya kasance ta tattara kayanta ta koma gidan na su gaba ɗaya. Tana tunanin saka haya a gidan domim su dinga samun na abinci sai labari ta ji yayanta Hamisu ya bige kwaɗon ya saka sabuwar amaryarsa Karime a ciki. Ranar dambe shi da Saubahn kamar sa’ansa haka ya yi masa laga-laga tare da targaɗe a ƙafa.

Haka aka kawo mata shi kamar matace magashiyan. Tana kuka ta kai shi aka gyara masa, lokacin da ta dawo ne ta samu matan gidan su na tsegumin Saubahn ɗin ya cika taurin rai idan aka taɓa ta.

“Ai wannan yaron idan ku ka bari ya ƙara wayau sai dai ku zama abokan gabzawa, domin zuciyarsa har ta fi ta uwarsa tauri. Ka ga fa yadda duk girman Hamisu da ya maka masa wani dutse a goshi sai da ya saka shi kuka.”

Ƙawar Sumaye Lantana ta furta tana kama haɓa,

“Ni kuwa idan ni ce ita wallahi soja zan tura shi.”

Jumala ta yi karaf ta saka baki,

“To ai sai ki ba ta shawara.”

Sumaye ta faɗa a tunzure ita dai wucewa ta yi ta ba su wuri. Tana riƙe da Saubahn da yake ɗingishi har suka shiga ɗaki. Haka ta shafe sati tana jinyarsa.

Komawarta gida bai haifar da komai ba, domin abinci ma sai ya soma gagararta.Rayuwar tala da ta tsana tun ƙuruciyarta ita ce rayuwar da yaranta suka durfafa ka’in da na’in. Wata rana sai sun je talla sun dawo sannan su samu abin da za su kai bakin salati. Tana ji tana gani ta haƙura da karatun su, saboda kafin su siyar su dawo an ci rabin karatu ko kuma an ma tashi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Wasu 10Kuskuren Wasu 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×