'Ta kashe shi.'
Kalmar ta ci gaba da amsa kuwa a kanta, yayin da gaɓɓan jikinta suka ci gabata da wata irin rawa kamar ana kaɗa mata gangi. Kamar suɓucewar tarwaɗa a hannun kuturu haka ta ji duk wata ƙwarin gwiwa na suɓucewa daga gareta. Wata juya ce take ɗibanta kamar ta sami karan mahaukaciya.
Sai dai kuma sannu a hankali wani ƙwarin gwiwa ya soma shigarta yayin da hannunta da Saubahn ya damƙa ya sanya ta jin sawaba. Hakan ya ba ta ƙarfin gwiwar ɗagowa. Yayanta Lawali ya sake haske idanunta da fitila. . .
Ya