Skip to content
Part 13 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

‘Ta kashe shi.’

Kalmar ta ci gaba da amsa kuwa a kanta, yayin da gaɓɓan jikinta suka ci gabata da wata irin rawa kamar ana kaɗa mata gangi. Kamar suɓucewar tarwaɗa a hannun kuturu haka ta ji duk wata ƙwarin gwiwa na suɓucewa daga gareta. Wata juya ce take ɗibanta kamar ta sami karan mahaukaciya.

Sai dai kuma sannu a hankali wani ƙwarin gwiwa ya soma shigarta yayin da hannunta da Saubahn ya damƙa ya sanya ta jin sawaba. Hakan ya ba ta ƙarfin gwiwar ɗagowa. Yayanta Lawali ya sake haske idanunta da fitila, sai dai magana suke ƙasa-ƙasa hakan ya ɗaure kanta ya kuma ba ta tabbacin wani shiri ne kawai suka yi a kanta. Kuma suke son cimma shi a kusa ba don hakan ba da kwarmato za su yi har a iso a kamata da laifin da suke jefanta da shi.

Ɗaya bayan ɗaya suka fice daga ɗakin, shiru ya ratsa ta sake rarrafawa kusa da gawar mahaifinta, zuciyarta na matsewa da wani irin rauni ta ɗora kanta a bisa kafaɗunsa. Kuka take zuciyarta na faɗa mata yana jinta, ranta na ba ta kamar zai zai miƙe ya kama hannuwanta ya furta mata kalmar,

“Ki yi haƙuri Maryama.”

Saubahn ne ya ƙaraso tare da kama hannunta. Buta ya ciko da ruwa ya damƙa mata. Ta kuwa ji daɗin hakan domin alwala ta ɗauro ta tayar da sallah. Haka ta durfafi kaiwa ubangiji kukanta tare da nema mahaifinta gafara.

Yadda ta ga dare haka ta ga rana, sai mutuwar Tasi ta sake dawo mata sabuwa fil, haka ta kwana tana kuka tare da kaiwa ubangiji kukanta. Asubar fari batun rasuwar mahaifinta ya karaɗe ko’ina. Sai dai ga mamakinta babu labarin baƙin fentin da suka yi mata. Hakan ya sake ba ta tabbacin suna da gagarumin shiri a kanta.

Tun tana kasa kunne ta ji jiniyar motar ƴan sanda har ta haƙura. Kwanaki bakwai aka share makoki, kowa ya kama gabansa. Daga nan masu dogon buri suka soma tunanin yadda za su mallakin abin da mamacin ya bari.

*****

Ranar kwana goma tana zaune tana ninkin kayan su ita da Saubahn sai ga yayunta sun shigo, fuska a ɗaure suke dubanta ba ta kali ko guda cikin su ta cigaba da sabgarta, Saubhan dake gefanta Mama Sumaye ta bugawa tsawa tare da korarsa. Ƙi ƙam ya yi ya ƙi fita, sai da Maryam ta watsa masa harara.

Sai dai hakan bai sa ya bar ɗakin ba. Da idanu yake roƙonta kan ta ƙyale shi. Ba ta sake bi ta kansa ba, sai dai ba ta so su yi magana gabansa. Domin tana da yaƙinin ba alheri ne ya kawo su ba. . Su kuma hakan bai hana su isar da manufar su ba. Gaba ɗaya suka mayar da hankali kanta, Lawali ne ya soma magana kamar an cusa masa bread a bakinsa.

“Zaɓi ne guda biyu zamu baki, in ma ki zaɓi ɗaya ki samu masalaha in ma kuma ki ƙi zaɓa ki kasance a ɗaure ɗaurin rai da rai har abada.”

Ido ta ƙifta, busassun laɓɓanta da suke bayyanar da yunwa da tashin hankali suka motsa sai dai abin da ta furta sai ita sai zuciyarta.

“Ko ki ba mu takardar gonar Tasi’u ko kuma dolenki ki auri ƙanin mahaifiyarmu Nuhu!”

A razane ta ɗago kai tana duba su ɗaya bayan ɗaya. Wani abu take ji a ranta, wani abu da take jin idan har ta matsa ya wuce sai iya tafiya da ruhinta domin tsaf zai ya ga maƙoshinta. Tamkar sabuwar warkewar makanta haka ta dinga raba idanu tsakanin su. Sam ta manta da Saubahn na ɗakin sai da ta ji ya ɗauki moɗar kusa da ita ya jefi Lawali da ita.

Kafin ta yi aune sun rufe shi da duka kamar sun sami sa’an su. Shi suke duka amma duk wani raunuka ita take jinsa a jikinta tun tana bashi kariya har ta rufu a kansa ya zamana ita suke duka sai da suka yi musu lilis.

“Wallahi aure babu fashi sai an ɗaura ko kin ki ko kin so.”

Gaba ɗaya suka yi waje suna huci, runtse idanu ta yi yayinda ƙwala ta dinga zarya akan kuncinta.

“Rayuwata ta gama zama turken jaki sha gwagwarmaya. Allah ka zamo gatana.”

Ta yi furucin kuka mai ƙarfi na ƙwace mata. Saubahn ne ya sanya hannu yana share mata.,

“Mammah kadda ki sarayar da ‘yanci da mutuntakarmu duk domin wancan. Kadda ki bayar da damar da nagartattu su ka gaza samunta sai wanda ya kasance watsatse. Bai kai matsayin da zai shiga gonar mahaifinu ba don girman Allah kadda ki ce wannan ma don mu ne Mammah.”

“Ba ni da zaɓi Saubahn, idan har hakan na nufin ‘yantuwarku da kuma cikar muradanku a shirye nake na miƙa wuya.”

“Mammah bai kamata ba.”

“Jin daɗi ba komai ba ne Saubahn matuƙar dai akwai ‘yantuwar ahali.”

“Mammah wata sadaukarwa kasada ce da rayuwa.”

“Na yarda da duk kasadar da za ta baku damar zama cikakkun ‘ya’yan da za su zamo masu tunƙaho da sadaukarwar mahaifiya.”

“Mamma…”

“Pls Saubahn ka bar ni.”

Daga wannan rana wani babin ya sake buɗewa cikin duniyarta. Babin da ta yi ƙoƙari matuƙa wurin saka naci ta daddana sandarta amma kuma ta rasa karsashin miƙar da ita. Babin da ya ba ta damar da ta zamo mata mabuɗin duk wani ƙalubale na rayuwarta.

Tsanin azaba da rabon haihuwar Humaira da Hafsat da kuma yanke ƙauna tare da tabbatar da kariya ga yaranta shi ne dalilin da ya tilast mata auren Nuhu. Auren da ba ta san ranar da aka ɗaura shi ba saboda tana kwance cikin tsanin ciwon da ta shafe sati uku tana yin sa. Saubahn ne ke jinyarta hatta da kaiwa banɗaki.

Sai wayar gari ta yi ta ganta matsayin mata, matsayin da ta kasa yi masa rabaya na bambantuwa tsakaninta da baiwa. Ta rayu tsakanin rayuwa da mutuwa, domin numfashi kaɗai ke iya bambanta ruhinta da na matace amma zuciyarta ta gama tabbatar da zama ita ɗin mataciya ce. Domin gangar jikinta ta mutu murus da makauniyar biyaya wa burukan Nuhu.

Abu mafi baƙin ciki shi ne tabbatar da ita a gidan mahaifinta kuma ɗakin da aka ba ta tabbacin nan mahaifiyarta ta rayu shi ne Mama Sumaye ta zaɓa mata bigiren da za ta zauna. Sai a lokacin ta sake tabbatar da rashin gata, sai a lokacin ta yi kukan rashin dangin mahaifi ga yaranta ta kuma tabbatar haka za su rayu har zuwa abin da ubangiji ya hukunta.

A wannan tsakanin aka raba musu gadon. Yayin da nata kason ya saraya a hannunsa da sunan shi ɗin jagoranta ne. Tana ji tana gani duk wani abu da aka bata wanda ta ɗorawa burin ya samo silar komawar yaranta makaranta ya ɓalɓalce a hannunsa wurin caca.

Shekarunta biyu cikin bautuwa ita da yaranta da suka koma ƴan ƙwadago wurin bautawa duk wata gonakin da suke mallakinta amma kuma suka koma na Nuhu. Su za su noma amma kuma shi zai siyar ya yi caca da kuɗin.

A haka rantsattsen rabo ya ƙaddara mata samuwar cikin tagwayenta biyu. Takaicinta na ƙaruwa bisa bautar da ƙimarsu. Bautuwar da ko da sun yi ta ba ta isa ba su ƙimar cin ƙwayar gero ba daga ɗan abinda ya ajiye mata. Shi ma sai ya yi niyya.

Wajen ɓoye suna Saubahn ne ya dage aka sakaya musu suna amma ba haka ya so ba. Domin shi ya sanya sunan ne domin ya samu mafakar cin mutuncinta. Ya kira sunan domin baƙanta ranta, domin Hafsat sunan ɗiyar Mama Sumaye ne da ba sa jituwa. Khadija kuma sunan mahaifiyarta.

Sai dai ko kaɗan hakan bai wani dameta ba hasalima sai ta ba wa banza ajiyarsa. Wasu lokutan tana kwatanta ɗabi’ar Nuhu da jahilci irin na mutanen farko. Sai dai kasantuwarsa uba ga yaranta biyu na neman doke duk wani mugun kwatankwaci da za ta bayar a kansa. Har mamakinsa ya daina kamata.

Ita kam ta ƙarar da haihuwa. Haihuwar da aka yi ta a tsiyace, domin ko asibiti ba ta samu an leƙa da ita ba. Yaran da ko albarkacin hakikar haihuwa ba su samu ba. Abin da har gobe Mama Sumaye take goranta mata shi.

Haihuwar da take gani kamar wata sabuwar ƙaddara ce cikin rayuwarta domin a dalilin jinkirinta wurin haihuwa ne ta gamu da cutar da ta sake dagula duk wank lissafin rayuwarta wato yoyon fitsari. Kwananta huɗu tana naƙuda mai tsanani sai ana biyar ta haihu da ƙyar da taimakon Baba Yelwa.

Duk wannan baƙar izayar da ta sha bai sa tausayinta a zuciyar Mama Sumaye ba hasalima ganinta suke a matsayin mai raki da nuna son jiki. A haka har ta yi sati biyu da haihuwa. Saubahn ne ye zuwa daji ya samo itacen da take wanka da shi. Shi ne yake gudanar da duk wata sana’a da take gudanarwa ya ɗorawa su Ahmad a haka ake ɗan samun abin kaiwa bakin salati.

Satinta biyu da haihuwa, kwatsam ta riski kanta cikin wannan muguwr cuta. Da fari sam bata fahimci yanayin da take ciki ba, a tsamaninta tunda haihuwar ta soma yi mata nisa ko haka sauran mata suke fuskanta da fari ta soma ne da yawan fitsari akai akai. Kasancewar ana yanayin damuna sai ta ɗauka har da yanayin.

Sai dai kuma sannu a hankali ya kasance idan tana jin fitsarin kafin ta tashi matuƙar ta yi wani ƙwaƙwaran motsi sai dai ta ji ya zubo ko da kuwa nishi ne. Ko kuma tari da dariya mai ƙarfi. Tun abin ba ya damunta har ya soma damunta, duk tsaftar Maryam sai ya zama ta soma fuskantar barazanar zaurin hitsari.

Nuhu shi ne mutum na farko da ya soma goranta mata a gaban Saubahn, ranar ne karo na biyu da Saubahn ya yi ƙoƙarin dukan Nuhu tana nuna masa ɓacin ranta. Tijara ya fito sosai ya yi mata a tsakar gida su Mama Sumaye na sake zuga shi.

“Da ma Nuhu ban da kai wa zai zauna da ita, tsabar ƙazanta ta koya tun da ta haihu kamar kanta aka soma haihuwar ‘yan biyu.”

“Aikuwa Sumaye kin san ba zan ɗauki wannan iskancin ba, da ma gab nake da kai kuɗin auren Sabira tunda na kusa kammala ginina.”

“Yo da ma Nuhu mace ba ta komai sai zarni ƙila fitsari take yi.”

“Ba ta fitsari amma kuma tana kashi a leda.”

Saubahn ya mayarwa da Mama Sumaye magana. Saboda ɗabi’arta ce ai kuwa matan gidan suka kwashe da dariya. Ta kuwa shaƙa iya shaƙa. Ta jawo shi ta soma kima tana bambamin faɗa. Marym kuwa sai abin ma ya ba ta dariya, wai Nuhu ne yake mata barazana da zai ƙara aure mutumin da da shi da babu duk ɗaya ne cikin duniyarta. Kai tsaye za ta iya kiran aurensa da auren manufa.

Tsiran kwana biyu tsakani yaro ya zo siyan ƙuli, Maryam na tashi za ta ba shi sai ga lema a kwance. Sam ba ta san yadda abin ya soma ba. Ba ta ankara ba Mama Sumaye ta rangaɗa shewa,

“Ku ta ya ni gani uwar miji ta zama kaza, babba da fitsarin zaune a ranar Allah!”

Duk sai ta muzanta musamman da ya kasance yaron da aka aiko ya yi tsaye yana kallonta. Ƙwalla ta ahare ta miƙa masa ya tafi. Ko minti uku bai yi da tafiya ba sai ga shi ya dawo da kai a fashe yana ihu.

“Lafiya me aka yi masa?

Mammahn ta tambaya a ruɗe, gabanta na faɗuwa. Take yara suka hau yi mata bayani.

“Madu ne ya fasa masa kai saboda ya ce mamansu na fitsarin zaune…”

Kafin yaron ya dire Saubahn da ya shigo ya ɗauke shi da mari. Nan fa rigima ta sake ɓarkewa saboda yaron na wajen Sadi ne ɗan gidan Mama Sumaye. Da ƙyar aka raba faɗan. Sai dai ga Maryam sai abin ya zamo mata bin terere da yamaɗiɗi. Nan da nan batu ya ba za ƙauyen sai ya kasance kayanta ma an soma daina siya. Hakan ya sanya rayuwa ta yi musu ƙunci fiye da ba ya.

An yi bakan babu jimawa ranar wata littinin tana zaune tana sauraren rediyo. Rediyon da Abdallah ya samota a kayan gwangwan Madu kuma ya gyarata suke ɗan saka batira suna saurara lokaci zuwa lokaci. Wani lokacin ƙuma idan ba sa’ar gaske ba bata kamawa saboda dama ba wata rediyon a zo a gani ba ce.

Khadija da suke kira da Afnan na bayanta a goye yayin da Humaiyrah da suke kira da Afra tana hannun Ahamd Saubahn kuma yana wanki Abdallah na ta ya shi. Wani shiri ne ya ɗauki hankalinta sosai da sosai, ba ta san lokacin da suka fara ba amma dai ta tsinkayi muryar wata mata na bayani dala-dala. Fahimtar kamar shirin ita ya shafa ya sanya ta ɗauki rediyon ta shige ɗaki ta kasa kunne. Muryar mai gabatar da shirin ce ta cigaba da bayani yadda ya kamata:-

“Cutar yayon fitsari cuta ce da ke haifar da fitar fitsari ba tare da tsayawa ba, lamarin da ke sa masu cutar shiga halin damuwa.

Binciken da aka gudanar a fannin kiwon lafiya ya nuna cewa a mafi yawan lokuta cutar yoyon fitsari tana samuwa ne a dalilin doguwar nakuda da yin tiyata ga mata da kuma wasu abubuwa da suka shafi al’ada.

Mata da yawa sun rasa ransu sanadiyyar cutar, kuma yayin da wasu suka warke daga cutar, wasu da dama suna zaune ne a cikin rashin tabbas sakamakon an yi musu aiki amma ba su warke ba.

Binciken masana ya gano cewa bayan ita kanta wannan lalura da matan da suka kamu suke fama da ita, a gefe guda wasu daga cikinsu suna kamuwa da matsalar ɗaukewar jinin al’ada wanda hakan ke sanya fargaba a zukatansu, lura da cewa idan mace ba ta jinin al’ada babu batun daukar ciki gare ta. Dokta Abdallah babban likita ne da ke kula da ɓangaren masu cutar yoyon fitsari , ya ce,

“Cutar yoyon fitsari cuta ce da ke samun mata a dalilin buɗewar mafitsara lamarin da ke sa fitsari ya riƙa zuba ba tare da saninta ba. Haka kuma cuta ce da za a iya yin riga-kafinta ta hanyar kula da mai juna biyu tun daga lokacin ɗaukar ciki har zuwa haihuwarta. A cewar Doktan matan da ke fama da cutar yoyon fitsari sun kasu kashi-kashi gwargwadon girman hudar da suka samu a jikinsu.

Ana samun matan da hudar da suka samu ba ta da yawa, wannan za ki ga da zarar an yi musu aiki suke warkewa. Yayin da wasu kuma sai sun ɗauki lokaci wasu kuma saboda girman da hudar ta yi, to sai an yi aiki a matakai daban-daban. Akwai kuma waɗanda saboda yadda ciwon ya same su sai an yi musu dashen gaban nasu ma gaba daya sannan a zo a yi aikin yoyon fitsarin.

Akwai kuma waɗanda sai dai su yi haƙuri da halin da suka samu kansu a ciki, domin an yi aikin sai dai irin waɗannan kaɗan ne a cikin dubbai. Doktan ya ƙara da cewa idan har masu

<< Kuskuren Wasu 12Kuskuren Wasu 14 >>

1 thought on “Kuskuren Wasu 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×