"Saubahn! Rayuwarmu ba kamar littafi ba ce, ba mu da ƙumajin buɗe shi mu zuba kalar rayuwar da muke so. Wani littafin na rayuwarmu kaurin bangonsa kaɗai ya isa karya duk wani lago na tunaninmu.
Wata rayuwar aiki tuƙuru ne ke mallakamana ita, wata rayuwar kuma sadaukarwa ce, a wani gurbin kuma tsanin rabo kan sa auratayya tsakanin kaza da muzuru. Sai dai kuma wata rayuwar zunzurutun ƙarfin alƙalamin ƙaddara ce. Ba komai ne yake zuwa yadda muke so ba, ba komai ne zai tafi tare da muradanmu.
Mu yi haƙuri idan lokacin kokawa ya. . .