Skip to content
Part 15 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

“Saubahn! Rayuwarmu ba kamar littafi ba ce, ba mu da ƙumajin buɗe shi mu zuba kalar rayuwar da muke so. Wani littafin na rayuwarmu kaurin bangonsa kaɗai ya isa karya duk wani lago na tunaninmu.

Wata rayuwar aiki tuƙuru ne ke mallakamana ita, wata rayuwar kuma sadaukarwa ce, a wani gurbin kuma tsanin rabo kan sa auratayya tsakanin kaza da muzuru. Sai dai kuma wata rayuwar zunzurutun ƙarfin alƙalamin ƙaddara ce. Ba komai ne yake zuwa yadda muke so ba, ba komai ne zai tafi tare da muradanmu.

Mu yi haƙuri idan lokacin kokawa ya zo akwai ranar da zamu dara. Idan ya zama dole mu koka, to mu koka tare da zuƙatanmu kaɗai, amma kuma mu raba farincikinmu tare da ahalin mu. Wannan kaɗai zai ba mu abin da tunaninmu bai mallakamana ba.

Da ace muna da iko da mun yi faɗa da alƙalamin ƙaddararmu iyakar iyawar mu domin tabbatar da rayuwarmu akan bigiren da muke muradinta. Amma kash ba zamu iya ba! Ba zamu iya ba Saubahn!”

Ta ƙarasa da wani irin raunin da yake bayyana tabon zuciyarta mai zurfi ne, daga lokacin ya sake shatawa alaƙar dake tsakinsu da Nuhu layi mafi girma.

“Mijin Mamma ina kwana.”

Shi ne kalmar farko da take haɗashi da shi a duk safiya, tun da ya gargaɗeshi da dangantashi da sunan mahaifinsa. A haka suka rayu, a haka suka ta shi har zuwa lokacin da Saubahn ya fahimci manufarsa ta son sace wannan takarda ta su ta gona. Ai kuwa ya ɗauketa ya nanniƙa mata ajiya tare da wannan kundi na mahaifinsu.

Kundin da kullum take ɓoyo kuma hana kowa karanta shi. Da hannunsa ya ɗauki takardar ya yi mata ɓoyon da ko ita Mamman ba ta san in da take ba. Wannan shi ne babban takaicin da ya asassa Nuhu raba tsakanin uwa da ɗa, yake kuma jin sai Saubanh ya bar kusa da ita sannan za su samu muradin su domin shi ɗin garwurta ne kuma ƙarfin gwiwarta.

A hankali ta saki ajiyar zuciya mai ƙarfi wanda ya yi daidai da kiran assalatu. A hankali ta motsa ta ɗauki buta ta ɗauro alwala. Raka’atul fijir ita ce abar da ta soma yi, duk sujjada goshinta ba ya ɗagowa ba tare da nemawa gudanin jininta kariyar mutum da aljan ba.

*****

“Lokaci fa ya yi Sumayye!”

“Ban fahimta ba Nuhu kamar ya lokaci ya yi?”

“Ina nufin lokaci ya yi da za mu yi yadda muke so da wacan gonar, domin a yanzu hankalinmu kwance za mu yi wadaƙa da koma mene ne nata.”

“Ni fa bana son munafurci ka fito mini sak a mutum kawai!”

“To uwar masifa da a aljan zan fito miki, ina tabbatar miki cewa na yi nasarar kaɗa ƙeyar wancan jan wuyan da muke tunanin zai bamu matsala wurin katantane duk wani abu na ta.”

ta gwalo, kamar an saka ɗan bududdugin kwaɗo a ruwan zafi,

“Da gaske Nuhu? Lallai kai an yi ƙwalon shege ne amma garin yaya hakan ta kasance?” Ba tare da jinkiri ba ya yi mata bayanin komai,

“Kan ganin kuma ya tafin ke nan?”

“Wannan shegen ɗan nata mai zuciya kamar kuturu ina tabbatar miki ba zai ko da waiwayeta ba.”

Wata guɗa ta saki mai ƙarfi, hakan ya yi daidai da shigowar Barira tana sharɓar Kuka kamar ranta zai fita,

“Wallahi Inna na gaji Allah sai Sabitu ya sake ni, dukan yau daban na gobe..”

“Ai kiwa ba ki isa ba domin ba ni da wurin tsarmaki a wannan ɗan kututtirin gidan uban.”

“To wallahi sai dai a yi uwar watsi, a raba a bani gadona ni ma..”

Duka ta kai mata ta yi tsalle gefe ɗaya tana ƙunƙuni kamar tana magana da sa’arta.

“Allah wadaran na ka ya lalace…”

Nuhu ya faɗa yana turo hula gaba,

“Kai dakata ai ko dame-dame kurna ta fi magarya, ina abin yake? An faɗa maka bamu san komai ba ne? Tsohuwa ma takaicin wani ne ya kasheta…”

“Kan uwa…ki Sumaye ga ta nan a zaune, Barira ni za ki faɗawa magana ina ƙanin uwarki to bara na yi miki tonon sililin tunda shi ki ke muradi…”

Da hanzari Mama Sumaye ta dakatar da shi tana furwa, matan gidan kuwa sun yii kasaƙe, kowa ta ba za na zomonta suna naɗar komai , ƙwafa ya yi tare da shurar takalminsa ya fice.

*****

“Samira wai me ya sa ki ke son takurwa rayuwata ne. Wannan fa zaɓin ba nawa bane zaɓin Aliyu ne. Shi ya zaɓa mini rayuwar da kansa kuma ya tabbatar da ni a kanta ba tare da hango kuskuren sa ba. Kuma haka yake son rayuwarmu ta kasance. Mene ne laifina don na samawa kaina mafitar da ta dace da rayuwata?”

“Ƙwarai mafita ki ka samu Alawiyyah amma kuma mafita a hanya mara ɓulewa, kadda ki manta ke matar aure ce kuma musulunci ya ba ki darajar da bai bawa wanɗancan watsattsun matan da suke birgeki ba. Rayuwar su ba irin taki ba ce, matsayinku ya bambanta kin fi su gata domin kina kewaye da martabar aure..”

“Samira ba za ki gane ba, ba za ki fahimci gubar da take cikin rayuwar aure ba, saboda ke har yanzu ba ki yi ba don haka ki ƙyale ni!”

“Alawiyyah gori za ki yi mini saboda na faɗa miki gaskiya.”

“To auren ki ka yi ne Samira?”

“Tabbas ban yi aure ba, amma kuma ina godewa ubangiji da ban makance da son zuciya irin taki ba. Ki sani aure abu ne mai ƙima sa daraja. Kuma duk wanda ya ci amanar aure sai ya ga ƙarshansa domin amanar ubangijinka ka ci. Na bar ki lafiya”
Da idanu ta raka ƙawartata, tun ranar da ta ganta da Mas’ud a wurin shopping shi ke nan ta takura mata har sai da ta bayyana mata asalin rayuwar da take yi, ta shiga tashin hankali matuƙa saboda ƙawarta ce tare suka taso tun suna ƙanana sai dai ita ubangiji bai bata miji da wuri ba. Sauyawar alawiyyah ya yi matuƙar tayar mata da hankali. Amma kuma ta fahimci ta yi nisa ba ta jin kira.

*****

wanan Mamma biyar a asibiti aka sallameta zuwa lokacin ta murmure babu laifi. Sai dai fuskar nan ta yi fayau da ita. Ga shi kuma jikinta babu ƙwari sosai hakan ya sa duk wata hanyar neman kuɗi ta ɓangarenta ta tsaya sai abin da suka ɗan samu suka kawo. Suna kulawa da ita yadda ya kamata sai dai hakan bai hanata tunanin ina Saubahn yake ba.
Safiyar Asabar ne Nuhu ya dawo, tun dawowarsa babu wanda ya kula da lamarinsa bare ya dame su, ita kanta sannu da zuwa ce kawai ta haɗa su. Sai dai yanayin yadda ta riski walwala da ƙafafa a fuskarsa ya faɗar mata da gaba tare da karya duk wani kuzari nasa. Ta sa ni shi ɗin ungulu ne ba ya jewar banza, musamman a yanayin da suke ciki.

*****

“Maryam tsautsayi fa ya faɗa kan gonarki tana cikin gonakin da gwamnati ta karɓe, sun bayar da tabbacin ta shiga kan hanyar sabon titin da ake shirin yi a cikin gari”
Kamar saukar aradu haka ta ji saukar maganarsa a kunnuwanta, hakan ya sa duk wata gaɓa tata ta saki,

“Ban fahimta ba Nuhu, har tsawon wane lokaci hakan ya kasance amma aka kasa sanar da ni?”

Ƙureta ya yi da idanu, karon farko da ya ji tana yi masa magana cike da ƙarfin gwiwa, wannan ya ba shi tabbacin Maryam ɗin baya ta dawo ko kuma tana dab da bayana.

“Ban sani ba uwata, sai kin shaƙe ni tukuna!”

“Ba uwarka ba ce, don abin Allah wadai ne uwa ta haifi anamimin mutum irin ka, ni zan je har garin Malumfashin zan ji in da aka haihu a ragaya, ko da gwamnati ce ta amshe ai tana bayar da diya!”

Muryar Abdallah ta ratso tsakaninsu, duk suka juya a furgice musamman Mamma. Sam ba ta muradin abin da zai gindaya faɗi na faɗa tsakanin mijinta da ‘ya’yanta. Muryarta har rawa take yi, yayin da duk wata gaɓa tata take motsawa,

“Wa ya saka da kai Abdallah, me ya sa ba kwa jin magana ne…?”

“Da ma ya ya marasa asali za su ji magana, tsintaciyar magge tana magge ne?”

“Nuhu ya ishe ka!”

Abdallah ya faɗa da wata irin murya buɗaɗɗiya,

“Ko da kasantuwar mu marasa asali ta gefe guda, ai bai sarayar da mutuntaka da kuma ƙimarmu ba. Kuma nagartar mahaifiyarmu ta danne nagartar masu tunƙaho da na su asalin..”

Tas! Ta ɗauke shi da marin da ƙarfinsa ya jawo hankalin ‘yan uwansa, Madu da Afnan da Humaiyrah ne suka fito, tsaye suka yi cirko-cirko.

“Ko me za ki yi mini Mamma, wallahi ba zan bari ba, ba zan bari a sake haƙa wasu ramukan a zuƙatan ahalina ba. A baya kam na ɗauka amma ban da yanzu. Tun daga yarinta muke cin takaicin wannan mijin naki. Wallahi wallahi ruwa da iska babu abin da zai hanani zuwa malumfashi. Na ga uban da yake da iko akan sarayar da abin da yake malakin ki ne.”

Idanu ta zuba masa, ƙarfin halin Abdallah na tsorata ta matuƙa, tabbas ta fi shi baƙin ciki tana da buri mai girma akan wannan gonar. Hasalima ita ce wani turke da takewa kallon za ta ɗaura igiyoyin rayuwarsu a jikinta sai dai bi sa dukkan alamu idan ba ta yi da gaske ba wannan shi ne zai zamo muradinta na ƙarshe.

“Nuhu idan ba ka saketa ba sai na luma maka wannan wuƙar.”

Abdallah Ya furta yana saita shi da wuƙar dake hannunsa, ba abin sa yake yi sai huci, kuka ne ya taho mata, shi ke nan Nuhu ya yi nasarar ɓata mata rayuwar yaranta da ma abin da take gudu ke nan ya kai su maƙurar da za su bijirewa ko wace tsawatarwarta kuma bisa dukan alamu an zo gaɓar.

Tana tsoron ya gindaya gaba tsakanin yaranta, ko ba bu komai Afnan da Humaiyrah jininsa ne, kuma dole na sa jinin na gudana a tare da su. Dole akwai ranar da za su ji babu daɗi na abin da yayunsu suke akan mahaifin su.

“Ka bari Yaya Abdallah!”

Muryar Humaiyrah ta ratso kunnuwansu cikin furwa da nuna neman alfarma. Jikinsa ya yi sanyi, ya hangi wani abu mai kaifi a ƙwayar idanun ƙanwar tasa. Lalai akwain ƙalubale mai girma a gabansu.

“Duk lalacewara mahaifin mu ne yaya Abdallah, mu kan mu ba ma jin daɗin abin da yake yi domin ku ɗin ko ba ku kasance ‘yan uwa garemu ba kun bamu dukkan wata soyyaya bare kuma jini ya tsaga ina mai baka haƙuri a madadinsa.”

Da wannan damar Nuhu ya samu ya suɓuce, da gudu ya ƙarasa barin gidan a zuciyarsa yana mai tsinewa Maryam da yaranta. Sai yanzu yake danasanin ƙin bin shawarar yayarsa tun farko da ba a zo wannan gaɓar ba. Amma yanzu ma yana jin kamar ba su makara ba duk ta wani irin tsoro na mamayarsa.

Sautin kukan Mamma ne ya sanya su juyawa gareta gaba ɗaya, a surƙushe take riƙe da ƙirjinta, muryarta na rawa sosai,

“Ba ni da zaɓi bisa kalar ƙaddarar rayuwata. Amma ina neman sassauci mafi alkhairi daga ubangijina. Shi ne mafi cancanta da yi mini kowa ce sadaukarwa. Nasan yana jina kuma zai isar mini cikin gaggawa. Allah ga mi gareka ga haulata ka gaggauta zama mai kariya wa duk wani motsinmu.”

Madu ne ya dubeta cike da rauni yana share ƙwala,

“Mamma! Idan ƙunci ya shigo rayuwar mu sai mu yi gaggawar binne shi, hakan ba zai sa mu yi tsamanin komai ya ƙare ba. Ko da ba za mu daina jin maƙaƙinsa a maƙoshinmu ba. Mukan kai matuƙa wajen ɓoye damuwarmu da nemo farincikin da za mu raba tare da masoyanmu.

Ba don ba ma son sanar da su damuwoyin mu ba, sai don gudar musu damuwar da ta yi nauyi ga ƙirazan su ko da ba su furta mana ba. Da yawa sukan tambaye mu,

“Anya kun taɓa shiga cikin damuwar rayuwar nan? Anya kun san mene ne matsala ma?”

Ba su sani ba wasu lokutan da muke walwala akwai kwantaccen hawaye a idanuwanmu, sai dai mukan rubuta shi a littafi mu goge domin kada ya kasance a ajiye. Kadd kuma ya bayyana har ya taɓa alƙarmu da su.

Duk runtsi ka da mu bari damuwar duniya ta rungume farincikinmu, ka da mu ɗauka mu kaɗai ne a cikin ƙuncin rayuwa, ka da mumayar da matsalolinmu abin hira ga kowa, domin zai iya yi wuwa wanda muke tattaunawa da shi ya ninka mu wajen shiga matsalar rayuwa. Ita rayuwa mallakar ƙaddara ce, ita kuma ƙaddara ba a iya guje mata, domin shiryayiyar furofa ganda ce.

A dalilin gujewa ƙaddara akan riskarta. Kamar dai yadda ki ka yi domin gobanmu sai ga shi mun riski kanmu a bahagon yanayi.

Lokacin da ɗaruruwan dalilai suka bamu damar kokawa, imaninmu zai bamu duban dalilan yin dariya. A lokacin da muke zagaye cikin ƙalubalan maƙiya, kamun kai zai ba mu tabbacin a kan daidai muke. Allah ya amintar da mu a cikin abubuwa na alkhairi, ya ba mu ikon mallakar zuciyarmu a lokacin da jarrabawoyin rayuwa suka kutso kan mu.”

“Amin”

‘Yan uwansa suka asma yayin da Mamman ke jin ya tafi da kaso casa’in na nauyin da ƙirjinta ya yi mata. Shi ya sa take matuƙar ƙaunar Madu matuƙar zai ganta cikin wani yanayi sai ya san kalaman da zai faɗa mata masu kwantar da zuciya. Madu daban ne cikin yaranta. Akwai kafiya akwai kuma barkwanci da girmama damuwar nakusa da shi. Ko yana cikin damuwa ya yarda ya yi barkwanci matuƙar na kusa da shi zai gamsu.

<< Kuskuren Wasu 14Kuskuren Wasu 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×