Skip to content
Part 16 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

“Yau ina da aiyuka sosai saboda kin san gobe ranar hutun ƙarshen mako son zuwa Katsina.”

Asiya ta furta yayinda take sunkuyar da kai. Ƙureta ta yi da idanu tana san tabbatar da abin da take zargi.

“Kina nufin har yanzu ba ki gaji da nacin zuwa bincika ko za ki gan su ba? Me ya sa ne Asiya?”

Wasu hawaye ne suka zubo mata, ta share su tana jan majina.

“Aunty ko ba komai ƙila mu samawa mahaifiyarmu martaba da ƙimar da ta rasa cikin ahali a dalilin kuskurenta. Kina gani ƙiri-ƙiri Appah da Hajja sun hana a kai ta a duba lafiyarta wai abin da ta shuka take girba. Na sa ni ba ta kyauta ba, amma ko ba a duba ‘yan uwantaka ba sai a duba mu.

Mahaifiya ce fa, kuma wadda ta haifi yara har guda takwas duk da ransu, ban da mu ɗin masu biyayya ne kina ganin ba zamu ƙetare layin da wannan tsohon ya gindaya mana ba. Ba fa mu ya haifa ba mahaifinmu ya haifa. Wannan adalci ne!”

Zuciyarta ta ƙuntata, ita kanta tana jin zafin yadda aka juyawa mahaifiyar su baya. Sai dai ko sun ƙi ko sun so ta sani mahaifiyar su ta cancanci sama da hukuncin da Appah ya yi mata. Tabbas ita ɗin butulu ce. Kuma darajar ahali ne ya sa take har yanzu a tare da su.

“Ki yi haƙuri Asiya, ke yarinya ce wasu abubuwan baki san dalilin afkuwar su ba. Amma Appah ki daina ganin ya zaƙe domin Mama ta yi fiye da tsamaninki.

“Shi ke nan Anti. Kinga kuwa nemansa bai zama aibuba matuƙar zan sama mata salama bisa abin da take fuskanta.”

Sai ta juya tana tafiya akan duga-duganta. Yayin da kowane taku yake ajiye mata wani tabo mai zurfi a ranta. Ta rasa dalilin da za a yanke ɗanyen hukunci akan mahaifiyar su. Kuskure duka kuskuren ne. Amma kuskuren wasu matan yana somawa ne daga sababin da kuskuren wasu mazan ke gadar da shi, ta fuskar zamantakewa ko kuma halaya.

*****

Wayar kunnanta ta sake maƙalewa, ta ɗaga kai ta kali Aliyu dake sharar barci. Ta sake duban agofo ƙarfe ɗaya na dare. Salalaɓawa ta yi ta fito falo tana sanɗa kamar munafuka. Zama ta yi kan doguwar kujera daga ita sai wata rigar barci iya gwiwa. Kanta babu ɗankwali. Chats suke yi da Mas’ud amma kuma vedio call.

“Wai sai yaushe za ki samu fitowa ne Alawy?”

“Gaskiya D ba zan samu fitowa ba, saboda kwana biyu ban san nacin da ya zaunar da shi a gida ba!”

Ta faɗa tana yatsina fuska. Ta fuskanci kwana biyu Aliyun sai wani nan da nan yake yi da ita. Tunda ya fahimci ta watsar da lamarinsa ɗan ƙorafin ma da take yi masa kan rashin dawowarsa ta daina. Hasalima idan ya ce ba ya gari kamar wani murna take yi. Hirar su su ka cigaba da yi, cike da baɗala da kaucewa haƙokin ubangiji.

Juyi Aliyu ya yi, ya shafa kusa da shi sai ya ji wayam! Babu Alawiyya babu labarinta. Sake shasshimawa ya yi, amma kuma still ba ta wurin. Kansa ya ɗaure, ina ya je? A saninsa ko banɗaku sai ya rakata saboda mugun tsoro ne da ita. Shi ya sa ko tafiya ce ta kamashi sai ta nemi ɗan ta yin kwana.

Saukowa ya yi daga kan gadon ya duba banɗaki. Gabansa ya faɗi ba ta ciki. Ci gaba ya yi da duba ɗaku nan da suke jikin na su amma babu ita. Kai tsaye ya nufo fallo har tuntuɓe yake. Motsinsa ya ankarar da ita ta yi saurin kashe wayar ta turata ƙasan filo. Duk alamun rashin gaskiya sun bayyana a tare da ita.

“Alawiyya me ki ke yi a nan cikin wannan daren?”

“Wasu kaya na ne suka sauka shi ne na yi clearance ɗin su na tura musu kuɗin su.

Ɗakina kasan ba network ne da shi ba shi ya sa na fito nan.”

Ƙureta ya yi da idanu duk sai ta tsaraka,

“Kin tabbata?” Gabanta ya faɗi, to me yake nufi?

“Of couse!”

Ta faɗa tana gujewa haɗa idanu da shi. Haka kuma ta miƙe ta raɓashi ta wuce ba tare da nuna wani abu ta aikata mai girma ba. Kansa ya sake ɗaurewa tamau. Idan a baya ne sai ta bashi haƙuri. Ko ma ta haɗa masa da runguma. Yanayinta bai yi masa ba,

hakan na bashi tabbacin akwai wani abu sabo da bai kamata ya kasance a wurin ba. Tun dawowarsa ya soma fuskantar sauye-sauyenta.

Jikinsa ya soma sanyi da lamarin. Har ya kai ya kasa jurewa. Sagir ne mutum na farko da ya soma karantawa matsalar,

“Ai dama na faɗa maka za ta gaji wata rana ta watsar da kai Aliyu ba fa kai ne autan maza ba. Ka ma yi ta barka da ba ta nemi saki ba”

Ita ce amsar da ya ba shi cike da sarar da gwiwa. Shi kansa ya san yana yin kuskure a rayuwar zamantakewar su sai dai babu yadda zai yi ne. Dole hakan shi ne mafita a gareshi. Sai dai ga shi ya fuskanci hakan na neman haifar masa da ɗan da babu idanu.

Binta ya yi ɗakin, sai dai yana shiga ya samu ta kwanta ta soma barci. Raɓata ya yi ya kwanta, zuciyarsa na yi masa zugi. Wata zuciyar na tunasar da shi da a baya ne da tuni ta juyo ta shige jikinsa kamar magge. Tabbas yana kewar wannan yanayin.

Alawiyya kuwa ƙwafa ta yi, saboda ba ƙaramin takurata ya yi ba da ya katse mata hirarta da Mas’ud. Kwata-kwata ita yanzu Aliyun ba wani burgeta yake yi ba. Ta ma ƙagu ya yi ya yi ya sake yin wata tafiyar ko ta huta yadda ya kamata.

Tunda idan ba ya nan har gida take kawo Mas’ud ɗin ta hanyar ɓoye shi a bayan mota su shiga gidan idan za ta fito su fito tare. Haka suka kwanta kowa da abin da yake saƙawa a ransa.

*****

Safiyar Asabar ta zo wa Haj Khadija a hagunce. Abubuwa ne guda biyu ta tashi da su a ranta, tun jiya take juya lamarin kamar juyin waina, yadda Yaya Kulu ta kirata tana tambayarta wai ta arama mata miliyan guda za ta ƙara jari a plaza ɗinta. Ita a zaman da take ina ta ga miliyan guda? Sai kuma batun Fatima da ta tashi da shi wadda ta kirata tana kuka tana sanar da ita dukan da Samir ya yi mata ya janyo ta sami ɓari.

Zuwa yanzu ta soma jin ya kamata iyayen yarinyar su ɗauki mataki, domin lamarin Samir ya soma wuce gona da iri, ita kanta da take tausarta ta soma gundura. Neman saki ba aibu bane, matuƙar hakan zai zamo masalaha a rayuwar ma’auratan.

Ta lura kamar iyayen na ta suna hukuntata ne da wani laifi. Kwata-kwata ba sa ta tata, ba ta taɓa ganin yarinyar ta yi yunƙurin kai ƙara gida ba. Hasalima gidan kan sa ba ta cika zuwa ba daga sallah sai sallah.

Jiki a sanyaye ta kammala komai, da tunanin kwanakin masu gidan a wata ƙasa ta fito, kuma har zuwa lokacin babu ɗaya daga cikin ahalin gidan da ya kirata. Ta tabbata dai ba ta da wani ‘yanci a gidan. A haka ta ƙarasa farfajiyar gidan, motocin ta ƙarewa kallo duk sun yi ƙura, ba ta yi mamaki ba saboda babu mai hawa. Baba maigadi ne ya taso suka gaisa, duk da girmanta tana da ƴaƙinin zai yi ɗiya da ita.

“Baba ina Audu driver ne?”

“Ai Hajiya, Alhaji ya sallame shi tun ranar da za su tafi ya ce sai bayan sun dawo zai ci gaba da aiki.’

Maganar ta ɓata mata rai matuƙa, zuwa yanzu ta soma kaiwa maƙura daga abin da ake yi mata. Idan an sallami driver to ita ina ta kama idan buƙatarta ta fita ta taso? Ƙwafa kawai ta yi tare da juyawa ta fita. Da Ido Baba ya rakata yana mai jin tausayinta. Tunda ta fito ta tabbatar za ta sha wuya domin unguwar su ba unguwa ce mai cika ba. A haka ta shanye tsayin layin su duk ƙafaffunkafunta sun yi nauyi.

Daidai lokacin Saubahn ya fito daga gidan Mal yana sauri zai kai masa wani saƙo daga nan ya wuce tasha ɗaukar dako kamar yadda ya saba. Ras! Gabansa ya doka da wata irin matsewar zuciya, ba don Mammah na da yarinta ba babu abin da zai hana ya ce ita ya gani. Sake murza idanunsa ya yi hata da yanayin tafiyarsu ɗaya ne.

‘Maman Mamma?’

Wani sashi ya tunasar da shi,

‘Ina.’

Ya yi saurin ƙaryata kansa, ya shagala wurin kallonta kamar almara ya ga wata mota ta nufo wurin gadan-gadan. Zuciyarsa ta doka da wani irin tsoro, da hanzari ya nufi wurin kamar wanda aka tunkuɗa. Wani abu ne yake ji yana jansa zuwa gareta hakan na sake tabbatar masa ita ɗin tsattsonsa ce.

Kamar wani rebbort haka ya sanya hannu ya firgo hannunta, sai dai hakan bai hana motar ta daki ƙafafunta ba ta tafi za ta faɗi ya yi saurin tarota suka yi gefe. Duk da kasancewarsa ƙaramin yaro matashi hakan bai hanashi nuna shi ɗin namiji ne.

Hakan ya yi daidai da tsinkewar tunanin da ya lula da ita har ta kasa sanin abin da ya tunkarota daidai lokacin kuma Alawiyyyah ta saki ajiyar zuciya sakammakon ganin yadda ubangiji ya taƙaita lamarin.

Da hanzari ta fito, tana salati, a zuciyarta tana zagin mijinta domin ɓaƙin cikin abin da ya yi mata ne ya sanyata tahowa tana wasiƙar jaki tare da tunanin hanyar mallake shi. Shi ya sa har ta manta cewa tuƙi take yi.

“Sannu Mamma ba ki ji ciwo ba?”

Kalmar Mamma da kuma yanayin yadda ya nuna damuwarsa ta sanya zuciyarta wani irin motsawa. Idan aka ɗauke Fatima da yarinyar mijinta babu wanda ya yi mata wannan karar a rayuwarta. Ƙureshi ta yi da idanu yayin da wani abu ke zagaye zuciyarta wanda ta kasa tantance mene ne. Juyawa ya yi ɓangaren Alawiyyah,

“baiwar Allah a dinga kula yayin tuƙi ko dan gudun faɗawa tsautsayi.”

Sandarewa Alawiyyah ta yi, yayin da ta shagala da kallon Saubahn,

“Matashi ɗan sha takwas ya kamata ki nema za ki tantace a duniyar da ki ke.”

Kalaman ƙanwarta suka dawo mata, tabbas ta tsinci dami a kala. Kwantaciyar sumarsa ta cigaba da kallo wadda ta kasance ta asalin buzaye. Domin komai na sa na mahaifinsa ne. Ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba har zuwa kan fuskarta. Kallon gaula ya yi mata, ban da ta raina masa hankali ta kaɗe mutum kuma ana magana tana murmushi hakan ne ya tunzura shi ya soma magana yana huci.

“Da ma ai baku san ƙimar mutane ba, ganinku talaka bola ne kawai na zuba sharar da kuka kwaso, amma ban da haka ki yi ɓarna ana yi miki magana kina murmushi.”

Su duka biyun sai ya burge su da wadda ta yi laifin da wadda ake faɗan dominta.

“Cold down my brother, a rashi ne irin na ɗan Adam taka ba haka ba ne kamar yadda ka ke zaro ɗan Adam abu ne mai daraja.”

“Na ga alama ai.”

Ya faɗa yana kaɗe ƙasar da ta ɓata Haj Khadija tare da jan hannunta,

“Mamma mu je a duba ki akwai chemist nan gaba kaɗan.”

Mamman da yake kiranta jefata yake a wata duniya ta daban, dan haka sai ta bi shi kamar raƙumi da akala. Ganin wankin hula zai kai ta dare ya sa Alawiyyah tarar su da sauri tana ba su haƙuri. Tare da roƙon su zo ta kai ta asibiti a dubata. Nan fa taƙadama ta ɓarke, Saubahn ya ce ba za su bita ba ita kuma ta dage sai sun bita.

“Duk abun bai kai haka ba, kunga ni yanzu haka asibiti zan je ɗiyata ce aka kwantar…”

“To mu je can ɗin sai a duba ki.”

Alawiyyah ta faɗa da sauri da tararrabin kadda ta rasa damarta. Haka suka ɗunguma suka ɗauki hanya, kowa da abin da yake saƙawa a zuciyarsa Hajiya Khadija kuwa abin da ya faru ya dake tayar mata da mikin dake zuciyarta. A hanya ne Alawiyyah take jin babu abin da Saubahn ya hada da Hajiyar sakammakon dafe kai da ya yi yana tunawa da cewa Mal ne ya aike shi.

“Ya salam saƙon Mal.”

Sune kalaman da suka auɓuce daga bakinsa zuwa kan harshansa har suka samu nasar ji, hakan ya sanya suka zuba masa ido da rashin fahimta. Cikin nutsuwa ya yi wa Haj Khadija bayani. Hakan kuma ya ƙara martabarsa a idanunsu su duka biyun.

Musamman Alawiyyah da ta ƙara jin ta ƙara samun damar da za ta yaƙi muraɗinta domin da fari ta ɗauka ɗa ne ga Hajiyar ko kuma jika.

A haka suka ƙarasa asibitin, kasancewar Alawiyyah akwai wanda ta sani nan da nan aka duba Hajiyar tare da tabbatar da lafiya take. Ɗangyashin da take yi yana da nasaba ne da buguwa kawai. Dan haka suka jera suka rankaya zuwa ɗakin da aka kwantar da Fatima tamkar uwa da ƴaƴanta.

Lokacin da suka shiga Fatima na zaune tana sharar hawaye, tana ganin su ta yi saurin gogewa, da hanzari Hajiyar ta ƙarasa tare da rungumota jikinta, mai neman kuka…ai sai ta fashe da kukan da duk wanda ya ji zai tabbata daga ƙasan zuciyarta yake.

“Na gaji Anty wallahi na gaji da halin Samir. A wannan karon ko zan rasa mai karɓata a dangina sai na haƙura aurensa domin shi din ba autan maza ba ne!”

“Kul Fatima kadda na sake ji!”

Ta faɗa da muryar gargaɗi saboda ƙoƙarinta na sakayya wace ce Fatiman a wurinta,
“Haba Aunty ko ke da bamu haɗa komai ba dake kinfi dangina jin zafin abin da Samir yake yi min, me ake da rayuwa irin ta mahaifinmu ace mutum ba zai taɓa yafe kuskuren da aka yi masa ba a rayuwa. Laifi na ne zaɓin Samir a matsayin miji, idan laifin nawa ne ina da ƙarfin yin faɗa da rubutun da ƙaddara ta yi wa rayuwata ne?”

“Fatima! Ina tare da baƙi fa”

Sai lokacin Fatima ta sauke idanunta akan Saubahn da kuna Alwaiyyah, wanda zuwa lokacin sun gama fuskantar Fatima sai kamar su ce a wurin Haj Khadija. Sun koma ji a ran su ko yaya ta kasance ita ɗin mace ce mai karamci. A nan suka gaisa tare da yi mata ya jiki ba su jima ba suka fito bayan Alawiyyah ta karbi kwatancen Hajiyar.

Saubahn ma miƙewa ya yi ya yi mata sallama ya ce ya tafi, domin a kwatancan da ta ba Alawiyyah ya ji ba su da nisa da gidan Mal. Hasalima Mal na aikensa kaiwa maigidan saƙo. Haka ita ma Alawiyyah ba su da tazara ta azo a gani.

Lokacin da ya fito ya yi mamakin ganin Alawiyyah amma sai ya shanye, nufo shi ta yi tana murmushi,

“Mu je na rage maka hanya kadda ayi wa Mal laifi.”

<< Kuskuren Wasu 15Kuskuren Wasu 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×