Dum ya yi, shi sam yanayinta bai yi masa ba. Ya lura da yadda take wani kallonsa kamar za ta haɗiye shi. Ɗauke kai ya yi, ya sha mur. Kamar ba zai shiga ba sai kuma ya shiga, sun soma tafiya tana jan sa da hira tun yana basarwa har ya saki jiki. Anan ya ke jin ita ɗin 'yar Kaduna ce can ƙasan hayin rigasa nan ne gidan mahaifinta.
Bai dai tankata ba a haka har ta sauke shi ƙofar gidan Malam. Daidai lokacin ya hango Mal zaune kuma yana kallo saitinsu. Jaka ta buɗe ta zaro. . .