Skip to content
Part 17 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

Dum ya yi, shi sam yanayinta bai yi masa ba. Ya lura da yadda take wani kallonsa kamar za ta haɗiye shi. Ɗauke kai ya yi, ya sha mur. Kamar ba zai shiga ba sai kuma ya shiga, sun soma tafiya tana jan sa da hira tun yana basarwa har ya saki jiki. Anan ya ke jin ita ɗin ‘yar Kaduna ce can ƙasan hayin rigasa nan ne gidan mahaifinta.

Bai dai tankata ba a haka har ta sauke shi ƙofar gidan Malam. Daidai lokacin ya hango Mal zaune kuma yana kallo saitinsu. Jaka ta buɗe ta zaro kuɗi damin yan dubu-dubu ta miƙa masa. Da kallon mamaki yake binta,

“Na mene ne?”

“Na ka ne, ba ka na yi”

“Ba na buƙata”

Daga haka ya fita a motar ya gangara. Fitowa ta yi ta ƙure shi da idanu, wani abu ne ke motsa zuciyarta ji take kamar ta janyoshi. A haka ya ƙarasa, har ƙasa ya sunkuya a kusa da Mal.

“Afuwan Baba Malam, wani tsautsayi ne ya ratsa shi ya sa ban samu amso saƙon ba”
Idanu Mal ya zubawa motar Alawiyya har ta ƙurewa layin,

“Saubahn wace ce wacan?”

Sai da ya kali wurin da shatin motarta ta bari, sannan ya tanka.

“Malam ban santa ba, tsautsayin da na faɗa maka ya afku shi ne dalilin haɗuwata da ita”

Nan ya zayyana masa abin da ya faru cikin ƙasƙantar da kai,

“Na gane Hajiya Khadija matar Alhaji Salisu. Ai mace ce mai karamci, gidan ne ka ke kai saƙon tofi duk Juma’a”

“Haka ta ce mini Mal amma ni ban taɓa ganinta ba”

“Saubahn ka sake kulawa, rayuwa babu tabbas maso abin ka ta fika dabara”

Ya furta yana sake kallon hanyar da motar ta bi, wani abu na saƙuwa cikin zuciyarsa sai dai ba ya san zama cikin mutane masu zargi domin ya san hukuncinsa. Cikin girmamawa ya furta.

“In sha Allahu Baba Mal na gode”

*****
Alawiyyah tun da ta bar ƙofar gidan Mal take jin wani abu na zaga kanta. Sai dai har zuwa lokacin tana hango idanun Mal masu kaifi a kanta. Idanun da take ji kamar suna yi mata shamaki ne da cikar burinta. Murmushi mai ƙayatarwa ta saki a fili ta furta,

“Allah ka kai damo ga harawa…”

Daga haka ta murza kan motarta ta nufi gidan ƙawarta domin tattauna abin da ya kamata. Game da yadda za su shawo kan Saubahn ko da kuwa ta hanyar bin malamai ne.

*****

Kallon Madu take yi, tana mamakin yadda yake huci kamar namijin zaki. Sake duban idanunsa ta yi, cike da ruwan ƙwalla, ta tsura masa idanu har wata zaiba-zaiba suke yi. Ras! Gabanta ya faɗi, sak ya koma tamkar mahaifinsa. Wata ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi. Murya cike da rauni yake dubanta,

“Mamma wata rayuwar ba tamu ba ce, amma akwai ƙaddarorin dake alamta kasantuwarta a tare damu. Wani ƙuncin ba zunubanmu ba ne, amma kuma mukan iya ɗaukar alhakin ragamar su Mamma! Duk wani ɗaci ya bi bayan ɗacin rashi, rashi na abin da ka ke muradi amma kuma ya yi nisa gareka.

Nisan da ka ke bin sa da tsananin gudun harbawar zuciya amma kuma yana kuɓcewa himmarka. Ba za ka taɓa riskarsa ba sai yayinda wa’adin da aka gindayawa duniyarku ya tabbata. Nisan da za ka yi ta ƙoƙarin bibiyarsa yana kufce maka kamar kufcewar tarwaɗa a hannun kuturu.

A wannan gaɓar kadda ki ce mini kuskure ne Mammah, wannan ma kadda ki ce domin rayuwarmu ki ka yi. Kin yi kuskure da yawa dominsa, kin gindayar da duk wata ƙofar nasarar gobenmu duk domin shi. Me ya sa ki ke son nunawa duniya mu ɗin kamar mun zame miki tilas ne? Me ya sa ki ke son gurgunta muradanmu saboda farin cikin mutumin da kullum burinsa ya ga yankan bayanki.

Kin sarayar da Yaya Saubahn. A karo na biyu kin sarayar da burin Humaiyrah. A wannan karon kuma ki ke son bani tabbacin kin sarayar da Abdallah! Duk wannan saboda mene ne? Me ya sa za mu yi ta girbar shukar da ba mu muka dasata ba.
Da gaske ki ke san sanar da ni na rasa ɗan uwa kamar Abdallah Mamma? Wannan karon ba kuskure ba ne Mamma sakacinki ne!. Zan yi komai Mamma, idan na ce komai ina nufin komai ɗin. Ki tabbata za ki sake sarayar da wani gudan jinin matuƙar na je na dawo babu tabbatuwar Abdallah. Ni ma zan barki, zan barki da mijinki da ‘ya’yansa”
Ya ƙarasa yana kuka mai cin rai. Kimanin kwanaki uku ke nan rabon su da Abdallah tun bayan da Mamma ta rufe shi da faɗa kan abin da ya faru tsakaninsa da Nuhu a safiyar Asabar. Naira ɗari biyu suka tashi da ita kowa ya haƙura da buƙatunsa aka ba su Humaiyrah su tafi makaranta da ita shi ne ya bi su hanya ya karɓeta ya tafi wurin yin karta.

A hanya Abdallah ya haɗu da su, kusan tara saura basu sami ƙarasawa ba saboda ba su hau mota ba ga shi jarrabawa suke. Kafin wannan kuma keken da Humaiyrah ta ƙwalafa buri akansa Saubahn ya siya mata shi ma ya faki ido ya siyar da shi.

Yarinyar har kwanciya ta yi ciwo saboda yarinya ce mai naci da ƙulafuci idan tana son abu. Idan tana barci kuwa har mafarki take, tana faɗin Baba ka dawo mini da keke na. Da Mamma ta yi magana shi ne ya mareta a gaban yaran shi kuma Abdallah ya rama mata. Wannan ya sanya ta yi masa barazana da tsinuwa saboda ganin ta yi iya ƙoƙarinta wurin sanya shamaki tsakaninsu.

“Ba za ka fahimata ba Madu duk wani yunƙuri nawa domin gobanku ne!”

“A’ a Mammah domin muradinsa dai. Me ya sa ki ke san tabbatar da ƙasƙancin nagartarmu? Me ya sa ki ke san nunawa duniya mu ɗin ƙaddararki ne? Da muna da iko da mun sauya rayuwarmu daga fitowa a tsatson da basa maraba damu! A wane dalili ne za mu dinga girbar shukar da ba mu da alhakin dashenta?”

Ganin ba za ta ba shi amsa ba ne ya sanya shi barin wurin, yana kuka mai ciwo tabbas ya soma gajiya, har ya kai bakin ƙofa ya juyo.

“Mamma matuƙar na je na dawo ban ga Abdallah ba ni ma zan bi su tunda shi ki ka fi buƙata sama da mu!”

Nuhu dake banɗaki kalaman sun masa fari tas. Sai ya ji shi kamar a cikin aljannah.
“In sha Allahu ba za ka gan shi ba”

Ya furta da ƙaramar murya.

“Yaya….Yaya….Yaya”

Afnan ce ke yin furucin tana haki kamar ranta zai fita, hanyar waje take nunawa tana kuka,

“Yaya Abdallah…”

Ai daga Madu har Mamma da gudu suka nufi ƙofar wajen suna rige-rigen ganin abin da take nunawa. Sai dai suna zuwa suka yi turus!

*****

Kai tsaye Alawiyya gidan Hajiya Zali ta nufa, sai dai ba ta sameta ba ta tafi karɓar wata kwangila da ta samu dole sai da ta jirata.

“Ba za ki gane ba Zali, ba za ki fahimci cewar na yi babban kamu ba sai dai bisa dukkan alamu wannan zai ba ni wuya zai tabbata wani irin mutum mai matuƙar sa’a matuƙar ya same ni.”

Kallonta take kamar wata wawuya, ta rasa ko me Alawiyyah ta hanga ajikin wannan yaron da ta zo tana yi mata kuri a kansa. Amma za ta lallaɓata har sai ta nuna mata shi.
“Ko ma dai ya ya yake kin san be kamata ki kurantashi ba tunda baki ga himmarsa ba. Abu mafi muhimmanci tunda kin ce almajiri ne, ba zai yi wuyar ribatuwa ba. Ki soma siye zuciyarsa da tarin siyayya.

*****

Tun daga wannan rana Alawiyyah ta mayar da gidan Mal hanyar zaryarta ko Allah zai haɗata da Saubahn. Amma ubangiji bai taɓa haɗa su ba. Tun tana ɗaukar abin wasa har ta soma shiga hankalinta domin dai dumu-dumu zuciyarta ta ɗokantu da shi.

Ganin kamar idan ta cika zaryar za a saka mata idanu ya sanya ta sauya shawara.

Domin sau uku Mal yana ganinta, ana ukun ne kuma ya yi mata kashedi. Bayan ya tambayeta dalilin zaryarta a gidansa ta tabbatar masa Saubahn ta zo nema.

Kaca-kaca ya yi mata tare da gargadi da kakkausar murya.Ta tsorata matuƙa domin da fari ma ta ɗauka ko ya gano ita ɗin matar aure ce, sai daga baya da ta ji yana faɗin,

“Matuƙar na cigaba da ganinki a nan zan binciko mahaifinki na sanar da shi.”

Da rawar jiki ta bar wurin, sai dai hakan ba sanya gwiwarta yin sanyi ba. Mal kuma bai sanar da Saubahn ba. Don haka sai ta sauya shawara. Da taimakon Haj Zali suka binciko tashar da Saubahn yake zuwa aikin dako. Daga lokacin ta soma bibiyar duk wani motsi na sa. Ranar farko yana zaune yaro ya zo ya kira shi tare da nuna masa motarta ya ce ana kiransa. Bai kawo komai a ransa ba sai cewar kaya ne za a ɗauka, don haka cike da nutsuwa ya nufi wurin.

Tun kafin ya ƙaraso ta zuba ƙwanjinsa da ya soma tasawa ido, wanda ɗaukar kayan ƙarfi ya tilasta masa buɗewa. Ƙaranar riga ce jikinsa, hakan ya sa faffaɗan ƙirjinsa bayyana yadda ya kamata. Ido ta lumshe tana sakin murmushi. Daidai lokacin ya ƙaraso. Ƙwanƙwasa glasa ɗin motar ya yi, sai da ta mula ta buɗe domin tana gudun ta buɗe ya ga ita ce ya ƙi sauraronta.

“Kaya ne?”

Ya furta ba tare da dubanta ba, ita kuwa shi ta ƙurawa idanu,

“na ce kaya….”

Maganar ta maƙale a fatar bakinsa sakammakon haɗa idanu da ita, ɗaure fuska ya yi dama ba gwanun fara’a bane a wurin mata.

“Ashe ke ce, halan kaya ki ka zo karɓa?”

“Eh! Su na zo karɓa kuma driver ɗin bai ƙaraso ba, amma komawa zan yi”
Ta samu kanta da yi masa ƙarya.

“Allah to ya kawo su lafiya sai anjima”

Bai jira cewarta ba ya juya ya tafi yana tsakin da ta ji sautinsa har tsakar kanta. Sake lumshe idanu ta yi tana mai jin wani ɗaci a ranta.

*****

Kwana biyu tana zarya a tasha, amma kuma ba ta bari ya ganta saboda ba ta zuwa da motar da ta zo da ita, kullum sauya wata take. Ko ba ta ɗauko na Aliyu ba tana aro ta Haj Zali. Tun Hajiya Zali na jin haushinta har ta soma ba ta tausayi. Ranar dai ta shirya suka fita tare da sunan za ta takata bayan ta jibgo masa uwar siyaya cike but ɗin mota.
Lokacin da suka je dawowar Saubahn ke nan daga ɗaurin auren wani abokin aikinsu a nan tashar, sanye yake da shaddar da ta karɓi jikinsa wadda bai jima da ɗinka taba saboda bai ɗauko ko tsinke ba a gidan Mamma. Lokacin da yaro ya ce ana kiransa kamar ba zai je ba, sai kuma ya miƙe ya nufi motar.

Ta cikin glass Haj Zali ta ƙare masa kallo. Har wani haɗiyar miyau take yi sabida zalama, kafin Alawiyyah ta yi wani yunƙuri ta buɗe motar ta fita tana wani yauƙi da rangaji.

“Mal Saubahn mune nan muke kiranka na ga kanata waige”

Sai da ya yi mata kallon uku kwabo sannan ya furta,

“Lafiya?”

“Lafiya ba lau ba, duk ka bi ka ɗaga hankalin ƙawata ba ta barci idan ba ta ganka ba ba dole k ganmu ba”

“Ban fahimta ba?”

Ya furta yana kallonta kamar kashi saboda ƙara kusantoshin da take wani ƙarni ne yake duƙansa. Ita kuwa ji take ina ma ta janye ra’ayinsa sai dai Alawy ta ji a salansa. Amma ta ƙudurce ko da tsiya sai ta ɗana. Ganin kwarkasar da take masa taƙi ƙarewa ne tsoro ya sanya Alawiyyah ɓale murfin motar ta fito. Sai yanzu ya kali sashin. Ta nufo wutim kanta a ƙasa. Yana hangota ya soma jan innalillahi.

“Saubahn ƙawata ce tare muke da ita”

Ta furta da wani salo,

“Don Allah ku bar wurin nan, ba ku ga wurin aikina ba ne wai me ki ke nema ne a tare da ni”

“Idan har gudun ɓacin suna ka ke to ka tsaya mu yi magana ko ka biyo ni mota yanzu”
Waige-waige ya soma yi duk sun ɗaureshi da jijiyoyin jikinsa, ganin kowa na sabgarsa ya sa ya bi su kamar raƙumi da akala.

“Saubahn wani taimako nake nema, kuma kai ma za ka taimaki kanka”
“Ina sauraronki!”

Ya furta cikin ɗacin rain, babu kunya ta bayyana masa manufar da take ranta game da shi. Haj Zali na sake tayata. Take yanayinsa ya sauya. Fuska babu annuri ko ɗaya idanunsa sun kaɗa sun yi jajjir tsabar tashin hankali.

“Ina yi miki fatan shiriya, ba zan yi miki rashin kunya ba saboda ko banza kin girme ni amma ya zama karo na ƙarshe!”

Daga haka ya buga murfin motar ya bar su a nan sake da baki. Motar suka ja ransu babu daɗi, sai dai ita Haj Zali hakan ya yi mata gara kowa ya rasa da ace Alawiyyah ta samu. Duk da maza b burgeta suke ba amma dai tasan samun Saubahn a gefenta wata dama ce ta kare ajinta. Kuka sosai Alawiyyah take cikin mota, ji take kamar ta yi hauka saboda gaba ɗaya ta gama matowa akansa.

Haka suka rabu tana lallashinta. Ranar da zazzaɓi mai zafi ta kwana. Haka ta kira Zali tana kuka tana jaddadda mata ƙaunarsa. Ba ta yi mamaki ba tunda komai shirin su ne, amma sai ta kanne ta sake ɗorata kan wasu shawarwarin. Washegari kai tsaye gidan Haj Khadija ta soma zuwa, bayan sun gaisa ta yi mata sannu tare da ƙara jajanta mata abin da ya faru. Sun ɗan yi shiru suna hira jefi-jefi take zungurar Haj Khadij cikin hikima.
“Ni kuwa Hajiya kin sake ganin Saubahn?”

“Wai Saubahn dai, Saubahn nawa?”

Sai da ta ji wani abu da tace Saubahn nawa”

“Eh shi fa”

Ta faɗa kamar za ta yi kashi a wando,.

“Ayya ai Saubahn na gida ne, dama ai na faɗa muku Mal na aiko shi wurin maigidan. Duk da yanzu ba ya gari. Amma tun daga ranar faruwar lamarin nan ba ya kwana biyu bai zo ya gaishe ni ba”

Ta sanar da ita ba tare da tunanin komai ba, haka kuma tana jin wani alfahari a ranta domin duk sanda ya zo sai ya san yadda ya yi ya yi mata wani aiki mai muhimmanci. Shara ko wani dai na gida. Satin da ya wuce har wanki ya yi mata.

Jinjina kai Alawiyyah ta yi kawai , a ranta tana ji ina ma ita ce. Bata wani jima ba ta yi mata sallama ta tafi. Sai bayan tafiyarta ne Haj Khadija take jin kewa domin kwanan Saubah ɗin uku bai leƙota ba. Daga ƙarshe ta yanke idan ta fita zuwa gano Fatima za ta biya ta ji ko lafiya.

Lokacin da ta fito kai tsaye tasha ta nufa, wata ƙatuwar leda ce shaƙe da kayan ƙwalam da maƙulashe da ƙananun kaya na sawa. Wani yaro ta ba ya miƙa masa bayan ya tabbatar ya ganta ta kuna motar ta yi tafiyarta.

<< Kuskuren Wasu 16Kuskuren Wasu 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×