Skip to content
Part 18 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

Saubahn na tsaka da hira da abokansa yaron ya kawo saƙon, gaba ɗaya ya ɗauke wuta saboda yadda zuciyarsa take tafasa. Karɓa ya yi saboda tunanin kadda abokansa su ɗauke shi da wata manufa,

“Saƙon wata ‘yan unguwarmu ne da ta siyi kaya ta bada kwatance a kawo min.”

Shi ne amsar da ya ba Sadi da ya takura masa da tambaya. Kai tsaye da ya koma gida Malam ya nufa da kayan tare da yi masa gamssashen bayani. Kai kawai Mal yake jinjinawa domin ya san za a rina. Sai a lokacin yake ba Saubahn labarin zuwanta da kuma korar da ya yi mata. Sosai Saubahn ya shiga mamaki.

Tun daga lokacin suka shiga takun saƙa mai tsanani. Takai ta kawo har yara ya samu musamman a cikin tasha duk lokacin da ta shigo to kuwa zai sa su yi mata atire. Jifanta suke da duwatsu. Ranar farko har glass ɗin mota aka fasa mata, ya yi zaton ma za ta ɗauki mataki amma ko ajikinta duk da babu yadda Haj Zali ba ta yi ba kan su haɗa shi da ‘yan sanda amma ta tubure kan a ƙyaleshi.
Tana mmakin abin da yake janta ga Saubahn duk wulaƙancin da yake mata. Wasu lokutan sai dai ta shiga ɗaki ta yi kuka, gaba ɗaya ta hargitse. Tun Aliyu ba ya kula da lamuranta har ya soma tambayar abin da yake damunta. Karon farko da daga ya ɗaga hankalinsa akan wani abu da ya danganceta musamman ranar da yaran Saubahn suka sameta a goshi wurin jifa har aka yi mata dressing.

Sanar da shi cewa haɗari ta yi, amma sai ya kafe ya dinga faɗa kan me ya sa ba su je ga hukuma ba, ga fasa glass ga kuma rauni a goshi.

“To Aliyu idan na je hukuma me za su yi? Tsautsayi ne fa.”

Ta furta tana mai fatan ubangiji kadda ya ƙaddara wani idon sani ya ganta, duk da cewa ba ta gangancin zuwa babu facemarks ko kuma niƙab. Karon farko da ta soma jin ya kamata ace ta haƙura da Saubah.

Kwana uku tsakani ba ta haƙura ba ta sake shiryawa ta sameshi. Zuwa lokacin ya zo iya wuya, musamman da ya fuskanci rainin nata ya yi yawa. Ƙafa ya ƙafa ta fito daga cikin motar ta tako har inda yake zama. Take kuwa mutane suka bi su da idanu ɗuu. Ita kuwa ki ajikinta saboda ta rufe fuskarta.

Ta fi minti goma a tsaye ganin ba zai kulata ba ne ya sa ta kada baki ta furta,

“Saubahn wurinka na z…”

Kafin ta ƙarasa ya ɗauketa da maruka guda uku a jere, so yake ya tabbatar mata da shi ɗin ba kanwar lasa bane. Ido ta zuba masa da tsananin mamaki tana jin wata irin ƙuna a ranta. Tabbas ko ba ta so yau za ta bar shi ko da kuwa za ta mutu amma sai ta jiye masa darasi cikin rayuwarsa.

Juyawa ta yi ta koma motarta, ko minti talatin ba ta yi da barin wurin ba sai ga motar jami’an tsaro. Ba su yi wata-wata ba suka damƙe shi suka saka shi a mota. Shugaban tasha ne ya taso domin su yi magana amma babu wanda suka saurara saboda an sakar musu maƙudan kuɗi. Suna zuwa babu bincike suka wulashi cikin cell.

*****
“Amma Alawiyyah wautarki ta yi yawa wallahi. Ya ya za ayi ki sa a kama yaro? So ki ke asirinmu ya tonu ko kuma yaya? Kin san fa waye mijinki kuma kinsan cewa tsaf labari zai iya kai masa.”

Nadama da kuma da na sani ne suka bayyana ƙarara a fuskarta. Sai lokacin ta dawo hankalinta take kuma jin bata kyautawa Saubahn ba. Sai dai aikin gama ya riga ya gama yadda take jin zuciyarsa bisa marin da ya yi mata a lokacin babu abin da ba za ta iya aikatawa ba.

“Yanzu yana wane station ne?”

“Yana Anti daba!”

“Anti daba! Wannan marasa imanin?”

Ta furta tare da zaro idanu waje, kai ta sake jinjina mata.

“Ai shi ke nan sai ki ta shi mu je mu san abin yi kafin lokaci ya ƙure.”

Lokacin da suka isa wurin ba ƙaramin muzanta suka yi ba domin Malam ya daɗe da zuwa sai dai ƙiri da muzu an hana masa ganin saubahn ɗin. Haka ya zauna hannunsa riƙe da casbaha har lokacin da suka iso. Kallon Allah Ya shirya ya bi su da shi, daga bisani bayan shigar su aka nemi ganinsa ya shiga.

Lokacin da aka fito da Saubahn sai da Mal ya yi ƙwala saboda gaba ɗaya sun saɓa masa kamani. Fuskarsa ta yi wani irin kumburi na ban mamaki. Ita kanta Alawiyyah ta shiga tashin hankali amma gudun nuna rauninta ta dake. Da ƙyar yake takawa akan ƙafafunsa haka ya zauna kan wani benci. Bayan dogon jawabi haɗe da ƙarairayin su Alawiyya ta ce ta yafe masa.

“Ko da baki yafe masa babu abin da zai same shi. Kuma da izinin Allah matuƙar wannan yaro ba shi da haƙƙi akan ki sai kin ga sakayya.”

“Mal kadda ka yi mana baki.”

Haj Zali ta furta cike da rashin kunya,

“Ko ba baki shi haƙƙi masifa ne yarinya a yi dai mugani idan tusa za ta hura wuta.”

Daga haka ya kama kafaɗun Saubahn ya miƙar da shi. Tafiya suke amma kuma zuƙatansu na motsawa da wani irin ciwo.

Duk wani taku da Mal zai yi sai ya nema masa sakayya sosai yake jin ina ma yana da damar da zai ɗauki matakin da ya dace da waɗanan mata. A haka ya samu mai adaidaita sahu ya kai shi asibiti.

Nana ma da ƙyar da siɗin goshi suka karɓe shi, dalilin wani almajirin Mal ɗin da ya yi zurfin karatu yake a matsayin masaenger a asibitin. Haka ya rungumo shi suk dawo gida da tarin magunguna. Matar Mal da kanta ta dafa ruwa ta gasa masa jikinsa, babu abin da yake sai bin su da idanu yana jin kewar Mammah na motsa masa.

Haka ya kwana yana juyi, tare da takaicin rayuwar son zuciyar da Alawiyyah ta ɗaukarwa kanta shi gaba ɗaya ma tausayi take ba shi. Domin ya san rayuwa ce mara ɓulewa ta ɗaukarwa kanta. Tsayin sati guda ya yi yana jinya. A wannan kwanakin zuwanta uku da kaya niƙi niƙi wai ta zo dubiya.

Zuwan farko Baba ta samu Matar Mal shi kuma Saubahn yana barci, Mal kuma ya je musafa. Hakan ya yi mata daɗi sosai don dama a tararrabi ta taho. Don dama ko shawara ba ta yi da Haj Zali ba, saboda tun bayan tafiyar su da suka yi haɗari ta soma tsinewa Mal da Saubahn tana yi mata bala’i kan ta taɓo musu gudan Malami. Don haka da faɗa suka rabu kuma duk sun yi fushi kowa na ganin laifin kowa.

Sai bayan ta tafi ne ya Saubahn ya farka, Baba na kwatanta masa mai zuwan ya hau mamaki da tunanin ƙarfin halinta. Jin wace ce ya sa jikin Baban sanyi. Ta kuma ci alwashin taka mata burki. Ilai kuwa zuwa na biyun ta sake yin katari ba kowa gidan sai Saubahn kaɗai. Ba ƙaramin dokawa zuciyarta ta yi ba, ganinsa ya fito daga shi singlet da wando gajere. Wani abu ta ji yana tsarga mata, sai dai bata yi aune ba ya ƙunduma mata zagi.

Duk sai ta ji ta muzanta. A nan ta ga tsurar tijara da rashin kunya. Ya kuma ba ta tabbacin har gidanta da mai gidanta ya sani. Jikinta ne ya soma rawa, duk tunaninta ya ba ta da gaske yake yi. Cike d hanzari ta bar gidan sai dai hakan bai hana surarsa zama daram cikin kwanyarta ba.

Wannan ne kuskure na ƙarshe da take jin ta yi a rayuwarta. Sai dai zagin da ya yi mata ya fiɓkomai yi mata ciwo,

“Mayya ‘yar tasha.”

Ta kuma ci alwashin barinsa har a bada. Fita ta yi tana kuka kamar ranta zai fita. Ko gani bata yi ta hau motarta ta tuƙa zuwa gida. Tuƙin da ya zamo sanadin abubuwa da yawa cikin duniyarta. Tuƙin da da ace ƙaddara na shawara da bawa da Alawiyyah ba ta yi shi ba.

*****

Lokacin da Alawiyyah ta juya zuwa gida gaba ɗaya hankalinta ba ya jikinta, babu abin da take tunanin sai Saubhan da surarsa. Yayin da kukanta ya ci gaba da ƙaruwa yana ruruta abin davyake zuciyarta. Wayarta ce ta yi ƙara ta ɗauka tare da karata a kunnanta.

“Kina ina na dawo ba kya nan?”

“Ina hanya gani nan ƙarasowa!”

Ta furta cike da ginshira. Katsewa ta yi tana mai jan dogon tsaki, tana shirin taka birki ne bata yi aune ba wata mota ta zo ta yi ciki da ita. Motarta ta yi dungure tare da mirginawa ta sake dokar wata bishiya bata sake sanin inda kanta yake ba sai farkawa ta yi ta ganta kwance a gadon asibiti. Ƙure ɗakin ta yi da kallo tana mamaki.

Karaf idanunta suka hango mata maigidanta a gefe ya zuba tagumi, kanta ya ɗaure me zai kawo Aliyu da kuma ita nan. Babban abin da ya ba ta mamaki tagumin da ya buga. Bata taɓa ganinsa a wannan yanayin ba.

Ƙwaƙwalwarta ce ta tafi tunani take ta tuno lokacin da mota ta nufo kanta. Ƙara ta saki tare da ƙoƙarin miƙewa amma sai ta ji ƙafafunta sun yi nauyi. Hakan ya juyo da hankalin Aliyun da ya faɗa dogon tunani.

Hawaye ya share tare da nufo inda take.

“Sannu Alawiyyah ashe kin farka?”

“Me ya same ni Aliyu? Me na zo yi nan wurin?

Ina Saubahn?”

Hajiya Zali da shigowarta wurin ke nan ta ɗora hannu a baki jin Alawiyyah na ambatar sunan Saubahn.

“Ki yi haƙuri kin samu haɗari ne bayan mun gama waya a hanyarki ta komawa gida. Yau kwanaki biyar ke nan ba ki san waye a kanki ba sai yanzu da ki ka farfaɗo.”

Kalmar haɗari ce ta cigaba da za ga kwanyarta har zuwa lokacin da idanunta suk sauk kan ƙafafunta. Mugun gani ta yi domin dai an yanke ƙafafunta duka biyun zuwa guiwa an naɗe su da bandeji. Hakan ya samo asaline sakammakon wasu ƙarafa da suka shiga cikin ƙafafun suka dagargaza ƙashin ƙafafun.

Kuma ƙarafan suna da tsatsa a jikinsu. Hakan yasa dole sai an yanke ƙafafun nata, tun da suka kawota asibitin tsayin kwana biyar bata farfaɗo ba. Wannan shi ne dalilin da ya jefa Aliyu cikin tunanin da har ta farka bai sani ba, babban tashin hankalinsa shi ne yadda wurin gwajin jini aka tabbatar da tana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

Jikinsa ba ƙaramin sanyi ya yi ba ya san babu tantama matarsa nutsatsiya ce, kuma an gwadashi an tabbatar da shi ba shi da ita. To ina aka haihu a ragaya? Sai dai zuciyarsa ta kasa nutsuwa da Saubahn data ke kira tun a lokacin da ta soma fita hayyacinta. Ƙara ta saki mai ƙarfi,

“Aliyu me ya sami ƙafata?”

Baya ya juya mata yana share hawaye,
“Ki yi haƙuri Alawiyyah an yanke miki ƙafafunki saboda sun tashi daga aiki”
Suman wucin gadi suka yi ita da Hajiya Zali,
“Sai kuma batu na biyu bincike ya tabbatar kina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki, amma ki yi haƙuri Alawiyya, ba zarginki nake ba, an gwada ni ni lafiyayye ne. Kuma har ga Allah bana neman mata ki faɗa mini ta yaya ki ka samu wannan muguwar….”

“Na shiga uku na lalace, Hajiya Zali kin gani ko? Ke ki ka ja mini wallahi. Da ma sai da Samira ta faɗa mini duk wanda ya ci amanar aure sai amana ta ci shi. Kaicona kaicon rayuwata. Mai ya sa ban yi haƙuri da rayuwar da na samu kaina ba har zuwa lokacin da Aliyu zai fuskanci kuskurensa?”
Hajiya Zali jikinta rawa ya kama yi, musamman ganin Aliyu ya nufota gadan-gadan kamar baƙin kumurci, wata muguwar shaƙa ya yi mata,
“Faɗa mini cutar da ki ka yi wa iyalina”
Idanunta ne suka firfito yayinda numfashinta ya soma ƙwacewa, babu tantama ta san tsaf Ali zai iya kasheta har lahira.
“Ka tsaya zan faɗa, zan faɗa maka ka sake ni”
Ta faɗa a wahalce, sakinta ya yi yana auna mata mugun kallo. Tiryan-tiryan ta faro masa tarrayarsu da matarsa da yadda ta ja hankalinta ta hanyar kwalinsu da suke sakawa na ƙungiya domin jan ra’ayin mata. Ta ɗora da cewar,
“Na so ace ta amince da ƙudurina na neman jinsi amma ta nuna tsoro take ji, sai na rabu da ita da niyyar gaba ma ja ra’ayinta. Amma don Allah ka yi haƙuri ƙungiya ce ta ɗoramini alhakin nemo mace mai yanayinta. Mun kasa nasara a kanta ne saboda tana yawan sadaka.

Amma ko ma mene ne ya faru kai ne sila, kai ne ka bamu lasisim zama tare da ita domin baka mayar da damuwarta taka ba. Neman kuɗinka shi ne kan gaba da komai na rayuwarka hatta kuwa da kulawa da iyayanka.

Akwai ira-iranku da yawa, a tunaninku mace bata buƙatar komai sama da kuɗi, musamman macen da kuka ɗauko daga gidan da ba su da ƙarfi sosai. Kawai sai ku mayar da su masu gadin gidajenku.

Ta ka ma da sauƙi tunda kai neman kuɗi kawai ka sanya a gaba, saɓanin wasu da suna neman wasu matan a waje amma matayen au ko oho. Saubahn kuma da ka ji tana kira sabon yaro ne da sa’armu take tattare da shi aka ba mu tabbacin sai mun haɗa su da ita. Mu muka ɗarsa son kasantuwa da shi a zuciyarta. Ira-iranku muke nema masu wasa da lamuran haƙoƙin matansu.

Mu kuma da wannan damar muke amfani mu ruguza rayuwar matan da sunan taimako, domin mu ma shi ne hanyar samun kuɗinm…”

Wani wawan duka Aliyu ya yi wa bakinta take haƙoran gaba suka fice gaba ɗayansu, nan da nan bakinta ya yi suntum kamar shantun ƙadangare. Zuciya ta kawo shi iya wuya, ya tabbata idan ya ce zai daketa kasheta zai yi har lahira kuma dole doka ta yi aiki a kansa.
Lallai sai yau ya tabbatar shi ɗin wawa ne kuma azzalumi. Wayarsa ya zaro ya danna kiran abokinsa Insp Sagir, sai dai kafin ta soma ƙara ya katse tunawa da maganar da ya faɗa masa ta ƙarshe,

“Aliyu ba ka da cikakiyar lafiya ka sani, kuma ga neman kuɗi da ya rufe maka ido kan gaba da komai. Idan ba za ka iya ba ka sakarwa mutane yarinyar su kadda ka cutar da rayuwarta!”

“Sagir ina neman magani ka sani, sannan batun neman kuɗi ina ga ba ni da matsala da Alawy da su saboda ita kanta idan babu kuɗin ba za ta zauna da ni ba”

“Duk da haka Aliyu idan an ciza…”

“Gaskiya Sagir ba zan iya sakinta ba, zan dai yi ƙoƙarin neman magani.”

Kuka ne ya ƙwacewa Aliyu, har bai san ya sake dana kiran ba Sagir ya ɗauka,

“Lafiya Aliyu?”

Murya a sarƙe ya furta,

“Ina asibitin Marwakh Sagir ka zo da gaggawa”

Gaban Haj Zali ya yanke y faɗi, domin ba ta san wa ya kira ba. Sai ga ta tana sakin fitsari a wando. Alawiyyah kuwa babu bin da take tunawa sai kamalan Mal gani take yi makar bakinsa ne ya kamata, kamar wani abu ya yi mata domin ɗaukarwa Saubahn fansa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Wasu 17Kuskuren Wasu 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×