Aliyu da Sagir abokai ne tun suna yara, ɗaya ba ya taɓa ɓoyewa ɗaya damuwarsa. Hata da karatu tun daga primary tare suke tafiya. Couse ɗaya suka so karanta Allah bai nufa ba. Cikin mintuna ƙasa da goma sai ga shi ya iso.
Yanayin da ya gani a fuskar Aliyu da kuma ƙafafun Alawiyyah da ya gani wadda ke kuka shaɓe-shaɓe ne ya ɗaga hankalinsa. Cikin tashin hankali yake tambayarsa abin da ya faru,
"Da ma ka faɗa mini Sagir ashe ranar nadamata na zuwa!"
"Wai mene ne!?"
Ya faɗa a fusace, bai ɓata. . .